Chapter 132
Chapter 132
yana kallonta dan sam bai iya mata ƙarya." murmushi tayi tare da cewa. "Allah ya cika rayuwar auren naku da farin ciki." A saman lips inshi ya amsa da Amin. Sai kuma tasa hannu bisa bedside ta ɗauko cup mai ɗauke da zazzafan tea mai ganyen Na'a-na'a, ta miƙa masa. karɓa yayi tare da ɗan zuƙa a hankali, idonshi ya lumshe dan jin ƙamshin da tea ɗin keyi. Ita kuwa Ummi a hankali tace. "Sai da safe ko." Kai ya gyadɗa mata alamun "To." tana fita ta wuce bedroom d'inta, kwanciya tayi amman baccinta yak'i zuwa nazari sosai takeyi tana tsoron duk wani abu da zaizo ya cutar mata da ɗanta. Hayatuddeen kuwa a d'akinshi yana konce yayi ɗai-ɗai yana shan dadɗan sanyin A.C kana yana chatting da yan uwa da abokan arziki inda yaketa sanar musu date ɗin auren Hammanshi. musamman a dandalinshi na Instagram wanda yakeda mabiya sama da dubu 9 wanda kuma yawanci sabida pictures ɗin Saifuddeen ne da yake sawa, da kuma son jin ainihin waye shi, tarin tambayoyin da ake mishi bazai iya amsarsu ba, sabida da yawama a zatonsu Saifuddeen bazai iya aureba. Ganin tambayoyin sun mishi yawane ya rufe datan Instagram yana niyar buɗe WhatsApp sai ga kiran Amina ya shigo wayarshi video call. yana ɗagawa yayi dariya ganin yadda ta haɗe fuska, A ƙufule tace. "Dariya ma na baka kenan?." Cikin dariyar yace. "Hmmm to ni me nayi miki naga sai hararata kikeyi?." ajiyan zuciya ta ɗanyi tare da cewa. "Yau kwana biyar kenan ina kiranka baka ɗaga waya meyasa." da sauri yace. "Sabida nasan zakice in bawa Hamma Saifuddeen wayar, kuma duk sanda kike kira baya kusa shiyasa bana ɗagawa." baki ta ɗan taɓe tare da cewa. "Ai dai yanzu kam yana gida ko?." Miƙewa zaune yayi tare da cewa. "To amman ya shiga fa." Da sauri tace. "Please karkace komai ka kai mishi wayar. Dan Allah karkace a a." jin haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙasa. Kai tsaye Side ɗinshi ya nufa inda Ummi ta rufeshi ta baya dan haka a sauƙaƙe ya shiga parlourn, a hankali yace. "Ni dai duk in da akace nawane sai ya koma kamar tirken doki, kalli yanzu parlour nan ko sarkin makka zai zauna a nan komai tsab-tsab sai ƙamshi tamkar da turare ake mishi mopping, kalli can kuma sama yadda banzayen nan su Imran suka wancakalarmin da parlour haka aka barminshi kamar wani maraya, to yaseen yau a nan zan kwana." Ya k'arishe mgnar lokacin da yake shiga bedroom d'in. Ita kuwa Amina sai dariya takeyi dan duk taji me yake faɗin. Yana shiga kai tsaye ya nufi kan gadon inda ya hango Hamman nashi na zaune wayar ya miƙa mishi cikin zumbura baki ya haura kan gadon ya konta gefen ɗan uwan nashi tare da rufe idanunshi wai shi yayi bacci. Murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara mushi rufuwan da yayi dan yasan bazai iya jure kwana cikin sanyin dashi yake kwana ba, sai ya kuma juyo ya kalli fuskar wayar tashi daya miƙa mishi, da sauri ya rage idanun nashi ganin fuskar Amina ita kuwa, girarta ɗaya ta ɗaga mishi alamun ya dai. sai ta kuma kalleshi cikin lunshe ido tace. "Ya jikin ka?." bata tsumayi amsaba dan tasan ba samu zatayi ba shiyasa taci gaba da cewa. "In zo har garinku har gidanku in dubaka da jiki, in dawo Amman ko ka kira kaji mun dawo lfy ko?." a hankali ya zaro harshenshi ya lashi jajayan labbanshi hakan yasa suka ƙara fitar da sheƙi, Lumshe idonshi yayi tare ds longoɓar da kanshi bisa kafaɗarshi tare da narke fuska, haka nan yaji wani guntun murmushi ya suɓuce mishi, ido ta lumshe tare da cewa. "Bakinka yana min kyau, gashin girarka mai kyau, idanunka masu tarin kyau, sajenka yana min kyau sosai Hamma, ina son komai naka surarka, yan uwanka, abokanka ina son duk wani abu naka, bayan Ya Amir kaine mutun na forko da nake bege da so." shiru yayi ya zuba mata idanu, yana karantar lafuzanta, ita kuwa cikin zazzafar soyayyarshi dake sarƙe mata zuciya da ruhi tace. "Ina sonka Hamma Saifuddeen zaka aureni? Kayi haƙuri kunya nakeji bazan iya rubuta makaba, kuma inajin kunyan in gayawa Hayatuddeen, gashi kai kuma baka jina to ta yaya zan shaida maka soyayyata, ina sonka ka zamo mijina uban ƴaƴana, ina addu'ar Allah ya azurtamu da samun yara masu kama da kai." sai kuma ta kalleshi ganin ya tsareta da ido haka nan yake jin kalaman nata har cikin zuciyarsa, to amman wai meyasa ita bata kunyan faɗi mishi wasu abin ne, ita kuwa ganin yayi shiru ya kuma rage girmam idanunshi ne ya sata cewa. "Ka gaji ko? bacci kakeji ko?, naga idonka yayi limshi, bari in kashe wayar sai da safe." Tana kaiwa nan ta katse kiran, shi kuwa Saifudddeen dariya yayi a ranshi yace. "Sokuwa kawai mai tunanin yara wato kina sona, hmmm ke dai faɗi gsky bani kike wani soba, kinada dai abinda kikeso daga gareni." daga nan yayi ta aikinshi. sai kusan ƙarfe ɗaya, ya sauƙo ya shimfid'a sallaya kana yaje yayi al'wala sannan yazo yayi nafilfilinshi sai d'aya da rabi ya konta. Washe gari ranar Jummu'a tun da safe su Zaleeha suka dawo, daga gidan Hajja inna tayi wanka ta wuce Billiri dan hira da nakassusun wancan yankin wanda k'arfe biyar na yammacin ranar jumma'ar ne zata gabatar da shirin, tun randa ta had'u da Saifudden a Jonapwd, bata sake zuwa canba, kuma tunda ta turawa ishaq text ɗin ban haƙuri bai kulataba itama bata sake bin ta kanshi ba, shi kuwa Ishaq shida Saifuddeen bakinsu a had'e a cewarshi ita da kanshi zata nemeshi har mazauninshi... K'arfe uku ta dawo daga billiri kai tsaye gidan radio nasu ta nufa, a nan tayi sallan la'asar, sannan ta zauna jiran lokacinta, tana zaune anan Bilkisu ta shigo ita da Manager d'insu tana ganin Zaleeha ta kwashe da dariyar shak'iyanci cikin ingizarwa tace. "Hajiyar nakasassu ina mutanen naki ne? Koda yake amaryar nakasashen gurgu kurma zance ko." cikin tsananin takaici Zaleeha ta watsa mata harara tare da cewa. "A a uwar nakasashe zakice ba amryar nakasashe ba wlh mai gado bana so ki daina had'ani da wannan musakin." cikin Shek'iyanci bilkisu ta iso gareta tare da cewa. "Sorry baza k'araba, amman mutanen nakine da abin dariya." juyawa tayi ta fita tabi bayan Manager ita kuwa Zaleeha Raveel ta kalla wanda yake mik'o mata sweet amsa tayi tare da cewa. "Ngd." kai ya gyad'a mata tare da cewa. "Kada ki sake aibata nakasassu dan duk wanda bai mutuba ba'a gama mishi halittaba. da kullum haka kike gaya min to meyasa kawai dan nakasasshe yace yana sonki sai ki juye daga Mai kakkyawar alaƙa i zuwa mummunar ɗabi'a, kada ki bari imaninki ya samu rauni." kai ta gyaɗa mishi sannan ta juya ta nufi ɗakin gabatar da shirin nata ganin lokacinta yayi. Mama kuwa da Zahira sosai zugar Ruda yayi tasiri a kwanyarsu da yake dama zuciyar ba inganci. Ƙarfe huɗu dai-dai suka dawo daga doho, suna shiga gidan kai tsaye side d'in Baba malam suka nupa, a parlour suka sameshi shida Ya Ahmad da Ya Habu, sai Mamy dake haɗa musu tea a kofuna. sannu da hanya sukayi musu,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148