Chapter 18
Chapter 18
bakin igiyar daga jikin kuros d'in, dan ta gama gugar nashi har ta goge uniforms d'insu Hayatuddeen da Faruq na boko da islamiya. gyara zamanta tayi suna fuskantar juna, a hankali ya bud'e bakinshi kana ya had'a lips enshi da alamu furta. "Sannu Addana ngd." lumshe ido tayi tare da cewa. "Godiya kuma a kan me?." zuba musu ido Ummi tayi tana jin so da k'aunar yaran nata da tausayinsu na ratsa mata zuciya musamman Saifuddeen, hannu ta d'aura bisa kan Saifuddeen d'in, shafawa takeyi a hankali tare kallon yadda ya manna kanshi bisa cinyarta murya a tausashe tace. "Babana kayi shiru kamar ranka baiso mu amshi kayan bako?." jujjuya mata kai yayi kana suka juyo suka kalli Rahma data shafa k'afarshi tare da jan 'yan yatsunsi biyu kana tace. "Kada ranka ya b'aci muma bisa dole muka amsa bawan Allah nan har durk'usa mana yayi yana kuka yana bamu hak'uri, k'in amsar kayan zaisa yayi ta zaton ko bamu yafe mishi bane." murmushi yayi tare da lumshe ido cikin kurma-kurma dayin body language ya had'a hannunshi duka biyu ya karkad'a kana ya shafa gemunshi tare da nuna musu kunnenshi alamun yace. "Ba komifa na fahimta, ai Bappa Ali yamin bayani." sai ya kuma kalli Ummi kana ya gyara zama sannan yayi mata bayanin canjin kasuwancin da zaiyi, haka nan Ummi ta tsinci kanta cikin farin ciki dan wannanma wata alamace dake nuna Saifuddeen inta yana tare da mutanen kirki nagari kuma wannan ya nuna mata kasuwa tasan da Saif d'inta. "Alhamdulillahi Babana Allah ya sanya al'khairi yasa ka fara harkar a sa'a rabbi yasa ka shiga da k'afar dama." Amin Amin suka amsa shida Rahma, kana ya mata bayanin fasa asusunshi nanma tace. "Hakan yayi yadda bappankun yace haka zakayi, ka bari tukun kaga yadda kasuwar ledan take." kai ya gyad'a mata kana sukaci gaba da hirarsu har zuwa 11:36 pm sannan sukayi saida safe, Rahma ta tafi d'akinsu ita dasu Raihana Ummi kuwa ita da Autanta da Faruq, shiko Saifuddeen d'akinshi ya tafi, koda yaje buta ya d'auka al'wala yayi sannan yazo yayi nafilfili daga bisani ya fara karatun Qur'an yayi kusan awa biyu sannan yayi addu'o'in da neman sa'a da nasara a kasuwancinsa ya rok'i Allah ya tsareshi da cin amana sannan daga bisani ya mik'e ya kashe wutan d'akin kana ya matso da fankanshi kusa da gadon tare da k'ara gudun fanka, gefen katifar ya zauna tare da yin addu'o'in bacci qulhuwa 3 falaqi 3 nasi 3 sannan ayatul kursi'u 1 ya shafa sannan ya konta da hannun dama, a hankali ya gyara konciyarshi tare da yin mik'a ido ya lumshe yana mai mamakin Al'amarin halittarshi a ranshi yake cewa. "Anya kuwa ni lafiyeyye ne." sai ya muka juya rigingine ya kuma yi mik'a still ba sauyi ajiyan zuciya yaja tare da barin abin a ranshi kana ya fara tasbihi dan ya samu bacci ya saceshi cikin k'ank'anin lokaci kuwa yayi bacci abunshi. Washe gari kuwa kamar kullum da sassafe suka tafi gombe shida Salisu nan suka wuni kasuwancinsu, bayan sallan isha suka koma Dukku. washe gari wanda ana gobe za'a d'au Azumi sabida ana zaton ganin wata yau, wanda ranar ne kuma Baba bello zai sallami kasuwa sai kuma bayan salla. Ranar sammako sukayi sosai shida Salisunshi k'arfe bakwai dai-dai na safe suka isa birnin bubayero, bayan Salisu ya sauk'eshi sai ya tsallaka bakin tashar gombe line, ya fara d'aukan irin masu kai aike tasha da sanyin safiyan nan. Shi kuwa Saifuddeen yazo dai-dai mashigar kenan yaga Jabeer ma, da sauri Jabeer ya iso gabanshi tare da bashi hannu cikin fara'a yace. "Tab Lallai wannan balaraben dukkun da himma kake wato in junin wani sammako kai a tafe ka kwanako?." hannu yasa ya d'an bugi k'eyar Jabeer irin ya cika surutu nan. shi kuwa Jabeer kama hannunshi yayi suka nufi cikin kasuwar da yanzu ake shirin bud'eta sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da d'aga mishi gira kana yace. "Ko dai kudin aure kake nema ne wannan iya sammako haka har ka rigamu mu yan cikin gari, nima dana fito yanzu yaseen Ya Adamu ne ya matsa wai inzo in kimtsa shagon yau zuwa jibi kayanmu zasu iso zamu fara baza hajar cinikin salla ne." murmushi ya d'anyi kana ya jinjina mishi hannu alamun mgninka ai. suna isa shagon Jabeer ya bud'e sannan ya fara kikimtsa wurin, yayinda Saifuddeen ke taiyashi, tuni suka kimtsa shagon suka gyara komai yayi ras, kafin su gama tuni kasuwa ta fara cika duk masu shaguna sun firfito da kayayya kinsu cikin yin mik'a alamun gajiya. Jabeer ya kalleshi tare da cewa. "Yauwa Balarabe jirani bari inzo." kai ya gyad'a mishi kana ya konta bisa tattausan sallayan daya shimfid'a cikin shagon ga iskan fanka na kad'ashi ido ya lumshe tare da gyara kinciyarshi. Shi kuwa Jabeer yana fita bakin tashar ya nufa inda wasu masu saida abinci suke, soyayyan dankali da kwai, sai gasashiyar kaza ya sai musu kana ya shiga shagon gefen wurin ya saya musu Faro k'ananun roba guda biyu, sai molt, kana ya juya rik'e da ledojin ya nufi cikin kasuwar. Bayan ya isa ya tsallaka wani dandamali da akayi wanda yake shamaki tsakanin masu shago da masu sayan kaya, kusa da Saifuddeen d'in ya zauna bubbud'e musu takardun abincin yayi kana ya kalli Saifuddeen dake konce yanata tab'e baki cikin tsuke fuska yace. "Ka tashi muyi breakfast." fuskar ya kuma ya mutsawa tare da jujjuya mishi alamun bazai ciba ya koshi, ido Jabeer ya tsura mishi domin tabbas yasan wannan d'abi'ace ta fulani yin fulaku wa kowama. shi kuma Saifuddeen tashi zaune yayi ganin kamar ran Jabeer ya sosu sai ya d'auki ruwa kana ya b'alle marfin sannan ya d'an sha ruwan har kusan rabin robar, a hankali yayi gyatsa kana ya ajiye goran ruwan sannan ya d'auki na molt, ya fara k'ok'arin mik'ewa da sauri Jabeer ya rik'o hannunshi kana yace. "Meyasa ne kake min haka shin baka d'aukeni aboki bako bare in kai matsayin amini." kai ya jujjuya mishi kana ya zaro bironshi tare da ballan takarda ya rubuta mishi. "Am so sorry my friend, wlh a k'oshe nake Ummi ta cika min ciki da d'umame yau da kanta taimin dan Adda Rahma taje gidan Goggo Dada can ta kwana, kana ni bana cin kaza, shiyasa, sannan dankalin kuma ba irin suyan da nake so bane akayi shiyasa bazanci ba, ai dani da kai yanzu mun zarta abokai mun zamma aminai, ka fahimceni." yana karantawa yace. "To gaya min me Kakeso in sayo maka?." amsar takardar ya kumayi ya juya bayanta kana ya rubuta mishi. "Am sorry Jabeer ba wai nak'i ci bane haka nan badan wani abu ba because inada wani banzai kyakk'yani wanda ni kaina yana damuna ba ko ina nake iya cin abinciba. Kaga zansha molt baka tab'a lura daniba haka nake wuni bani cin komai wani lokacin sai dai in had'a molt da pic milk sai insha." tabbas Jabeer yasan hakane so duk da haka baiji dad'in rashin cin nashiba, amman dole ya hak'ura dan Saifuddeen da wuya yaci, shi kuwa Saifuddeen tsallaka madandalin yayi kana ya nufi shagonsu Hisham wanda yau cikansa ya zarta na kullum, bayan sun gaisane yaje ya amshi botikinshi sabida lokacin wasu nata karya kumallonsu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148