Skip to content

Chapter 53

Chapter 53

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

shigewarsa d'an k'aramin side inshi, ita kuwa Raliya taita zumbura baki dan Ummi ta sata tattaramishi kayanshi daya watsar. Saifuddeen kuwa yana fita yaci karo da Salisu wanda shine ya d'aukeshi suka nufi hanyarsu da zata sadasu da titin tutun wada, mik'ewa sukayi direct har kusa da mashigar G.S.U cikin nitsuwa Salisu ke draving suna gab da shiga gate d'in. Jonapwd k'ungiyar nakasassu ta jihar kenan Salisu ya juyo cikin nitsuwa da kula ya kalli Saifuddeen tare da cewa. "Motocin nan da mukayi mgnarsu last week sun iso jiya, shiyasa nazo da nufin muje ka gansu ka zab'i kalan da kakeso a ciki, dan gsky zamanka ba mota baiyiba, tunda ko bazaka yi tuk'iba zamu iya samar maka amintaccen direba da zai rink'a kaika duk inda kakeso da kai da Ummi kafin Hayatuddeen ya k'ara girma." murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara zamanshi duk da yaga Salisun yayi parking kai ya jinjina tare da rubuta mishi. "Bank'i shawararku bafa sai dai kuda kanku kunsan cewa yanzu bani da kud'in a k'asa dan na yashe duk asusuna nayi hidimar k'aurannan to kuma bani son abu da bashi." a take fuskar Salisu ta sauya yanayi, cikin sanyin sauti yace. "Bashi kuma! Saifuddeen yanzu ashe dama kayana ba naka bane, ashe dan ka d'auki mota d'aya rak cikin jerin motoci kusan takwas wanda kaine silar samar min jarinsu sai ya zama wani abu?." Kai ya rink'a jujjuyawa cikin nuna alamun ba haka bane, ganin haka yasa Salisu cewa. "To kada ka sake kiramin kalmar bashi a tsakaninmu kuma ko bakaje ka zab'i kalar da kake soba ni zan zab'a maka da kaina gobe zan kawo maka ita har gida, kuma in ba matsala a cikin yaran da suke wonke mana motocin akwai wani yaro Sule yanada nitsuwa ya kuma iya tuk'i na mutunci sai ya dawo nan ya rink'a kaiku duk inda kuke buk'ata zai kuma iya kula da shuke-shuken gidan in yaso duk wata ka rink'a biyanshi abinda nake biyanshi, to dama kullum ina bashi kud'in abinci, to kaga kai ba sai kayi ta bashi kud'in abinciba sai Ummi ta rink'a zuba mishi shida baba maigadi ko?." ya k'arishe mgnar cikin yanayin tambaya. kai ya jinjina mishi tare da rubuta mishi. "To ba matsala kayi yadda kaga ya dace." cikin jin dad'in amincewar Saifuddeen d'in yace. "To ba matsala." Daga nan suka fito suka shiga cikin harabar wurin, kai tsaye office d'in Ishaq suka nufa, jin motsin bud'e k'ofarne yasa Ishaq juyawa da sauri sai ya kuma mik'e da sauri jin muryar Salisu, numfashi ya shak'a tare da cewa. "Lalle marhabin da manyan bak'i." jin Saifuddeen ya rik'e hannunshi ya sashi juyawa gareshi tare da cewa. "Kai amman naji haushi wlh kaga da kazo awa uku da suka wuce da ka had'u da Zaleeha sabuwar ma'akaciyar gidan radio vision FM gombe wacce take gabatar da shirin *Babu nakasasshe sai rago* yau dani mukayi hira na d'an bata tarihin rayuwata ka ko san dole zaka shiga ciki." shiru yayi jin Saifuddeen ya rufe mishi baki da hannu tare da zaro wayarshi da hannunshi d'aya kana ya rubuta mishi text. "Kai dan Allah ka huta mana wai bakinka bai gajiya da surutune? to ni ka bani ruwan sha tukun." da sauri ya zaro wayarshi jin shigowar sak'o yasan Saifuddeen ne ya mishi mgn, dariya yayi sanda ya karanta kana yace. "To sarkin k'warafi ga wuri ku zauna." sai kuma ya d'anyi taku biyu zuwa uku ya isa gaban firiji ruwan sanyi ya d'auko musu sannan yazo kusa dasu, Salisu kam har yau bai dena mamakin yadda abota ta kasance tsakanin makaho da kurmaba suna kuma fahimtar juna over, amsar ruwan sukayi saida suka d'an sha sannan suka ci gaba da hira amman banda Saifuddeen dan TV yake kallon tashar Farin wata wanda duk had'e suke da vision sosai ya zubawa TV idanu yana karanta rubutun daya bayyana a fuskar tv inda aka rubuta Babu nakasasshe sai rago, sosai Saifuddeen ya maida hankalin shi kan tv ganin sun hasko fuskar wata kekyawar budurwa mai cikar haiba, lips d'inta ya zubawa idanu dan yana son gane abinda zata fad'a da kyau, wani irin sassanyan ajiyan zuciya yayi jin wani abu na yana zirta cikin zuciyarshi har zuwa kwanyar kanshi ganin yadda take motso labb'anta wani sassanyar ajiyan zuciya ya kuma yaja a hankali ya sauk'e jin zuciyarshi na bugawa da sauri-sauri, wani irin shauk'i ne mai cike da farin ciki ya ziyarci zuciyarshi da gangar jikinshi, ina ya kasa kauda idanunshi a kanta, da kyar ya juyo a fizge ya kalli Ishaq da yake tab'ashi yana ce mishi. "Yauwa Saifuddeen juya ka kalli tv kaga sun fara haska hirar da tayi damu yau da safen, kaga wannan itace Zaleeha sabuwar mai gabatar da shirin babu nakasashe sai ragon." da sauri ya maida kanshi ga tv ganin an d'auke fuskarta an haska fuskar Ishaq ya sashi jan dogon tsaki tare da yin mgnar zuci. "Yauwa kaga wannan surutaccen ya janye min hankali da d'an banzai surutunshi kafin in juyo sukuma sarakan azarbab'i sun cire fuskarta sun hasko min sufkar wannan gardin, sai ya kuma ja tsaki tare da buge k'eyar Ishaq da yaketa murmushin jin dad'in shirin. sai kusan 4to5 minutes kafin suka sake nuno fuskarta inda take cewa. "Eh lallai kam na yarda Nakasa ba kasawa bace, tunda gashi kunayin komai kamar sauran masu cikekkiyar halitta." tsaki ya kuma ja ganin an kuma nuno fuskar Ishaq, Salisu kuwa gaba d'aya hankalin shi na kan Saifuddeen d'in dan ya fahimci ya bawa kallon tv mahimmanci a ranshi yace. "Kamar yana jin me suke fad'i." sai ya kuma yi murmushi ganin yadda Saifuddeen keta lumshe idanu da sauk'e sassanyar ajiyan zuciya." a haka dai har aka gama shirin, sannan suka salami Ishaq suka tafi. Washe gari kuwa kamar yadda Salisu ya fad'in haka yayi ya kawowa Saifuddeen motar da tayi matuk'ar bawa kowa mamki dan motace ta kud'i kimanin million uku da rabi, ga kuma Sule direba. Sosai darajar Salisu ta kuma k'aruwa a idanun makusanta Saifuddeen. Daga ranar Ahmad kuwa ya kasa ya tsare akan ala dole Saifuddeen ya daina tallan leda, ruwa da omo kuwa maiso yazo shagonsu ya saya, haka tasa dole Saifuddeen ya dena yawo a kasuwa yana gararamba, sai dai ya ajiye yaro d'aya mai wul baro, wanda yake cika baronshi da leda ya rink'a kaiwa duk costumes d'in Saifuddeen shago-shago suna bashi kud'in ya kawowa Saifuddeen inda shi kuwa yake sallaman yaron da dubu biyu kullum, haka yayiwa Ado dad'i sosai dan cikin awa uku yake gama raba ledan sannan ya dawo yaci gaba da dakon kayan mutane. A kwana a tashi asarar mai rai. Lokacin yaci gaba da tafiya, tuni Saifuddeen harkalla taci gaba ya gama biyan bashin daya amsa a shagonsu wanda ya cikata ya sayi gidanshi, ya kuma k'ara sayan wata dalleliyar mota mai d'an karen kyau da tsada. Ya kuma jonawa Hayatuddeen da Faruq makarantar da suke son, ya sayawa Hayatuddeen mashin d'in U.D sabuwa dal a leda. Hayatuddeen kuwa rawan kai sai abinda ya k'aru ya k'ara sabawa da abokanshi su Zakariyya sosai tunda yanzu makarantarsu d'aya kuma duk su hud'u sunada U.D Sosai Sule direba ya saba da Saifuddeen yana gane body language d'inshi sosai, duk

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148