Chapter 12
Chapter 12
dottijon yana mik'o mishi kullunan lododin yana ce mishi. "Tai maka min mana yarona mik'a musu lododin, ka amso min kud'in na jiya, ba sai na sauk'a bisa motar tawa ba". ya k'arishe mgnar cikin fara'a, shima murmushi yayi kana ya amshi ledodin ya juya cikin shagon inda yagga babban ogansu ya zaro kud'i ya irga gudan dubu guda uku kana da d'ari biyar, yana mik'owa Saifuddeen d'in yana kuma kallon Dottijon tare da cewa. "Barka da yamma baba Bello, kaga ko kamar kasan lododinmu sun k'are." cikin sakin fuska dottijon yace. "Kace nazo a dai-dai kenan?." shiko mai shagon bayan ya karb'i lododin da Saifuddeen yake mik'o mishi sai ya kuma kalleshi kana ya kalli Dottijon tare da cewa. "Kai Baba yau kam inaga a bamu na dubu biyar, sabida kar muzo gobe bakazo da wuriba su gaza mana." da sauri tsohon yace. "To ba matsala." bayan ya amshi kud'in da Saifuddeen yake mik'o mishi ne sai ya kuma bashi wasu banduran lododin, da sauri ya amsa kana ya bawa mai shagon. ganin alamun bakin mai shagon yana cewa. "To Baba bello Allah bada kasuwa sai gobe kuma." da sauri ya juya, ganin Dottijon na ce mishi. "Ngd ko d'an saurayi." kai ya gyad'a mishi tare da zura mushi ido ganin yaja keke nai ya tafi. A hankali ya juya yaci gaba da tafiya bai jima da fara bulayinba yaga anata shirin Sallan la'asar daga nan shima yayi harama. Bayan an idarne ya koma layin masu robobi nan yayi ta yawatawa, hardai aka kira magrib ganin anata rurrufe shaguna ya sashi fitowa, inda yayi sallan magrib jiya anan yauma yayi salla yana dawowa kuma ya samu Salisu ya iso. Daga nan bakin kasuwan bakin General hospital sukana nufa, inda daga bakin titin ta d'aya gefen akwai wata mai saida abinci sanin tanada tsabta ne yasa Salisu kawosu nan, amman Saifuddeen k'in ci yayi, sai dai Salisu yaci kana ya nuna mishi wani shagon fura da nono, gane yana sone yasa Salisu shiga ya seyo mishi k'aramar roba saida yasha sukayi sallan isha kafin suka d'auki hanyar dukku. Bayan sun isa shi Salisu yayi gidansu da machine d'in shi kuwa, Saifuddeen kai tsaye cikin gida ya nufa a tsakar gida ya samesu zaune, gefen Umminshi ya zauna kasan cewar akwai wuta duk suna ganin juna, da sauri Rahma ta kawo mishi abinci kana ta kunce bakin zaninta ta kunto 50 sannan ta kalli Hayatuddeen dake tsaye alamar zai fita ganin Saifuddeen dinne ya hanashi fita, hamtsin d'in ta mik'a mishi tare da cewa. "Ingo jeka gidansu Ya Adnan ka seyo mishi ruwan sanyi." da sauri ya amsa tare ficewa. Ummi kuwa cikin kula tace. "Ya kasuwa?." kai ya jinjina mata cikin son boye yanayin da yake wuni a cikin kasuwar. Rahma kuwa ido ta zuba mishi tare da cewa. "Saifuddeen gobema zakaje ne?." da sauri ya gyad'a mata kai dan baya son su karaya. Raihana kuwa cikin karya wuya tace. "Hamma Saif me kake sayarwa ne to?." ido ya zuba mata cikin rashin son yi musu k'arya ya girgiza mata kai alamar babu da sauri Raliyya tace. "To me kakeyi?." sai ya kuma juyo ya kalli Ummi ba tare daya amsawa Raliyya ba, cikin sanyi take ce mishi. "To Babana me amfanin zuwan, kalli jiya da yau duk baka wuni damu ka tafi har Gombe kuma kaje ba wani abu kakeyi ba ai gwara ka hak'ura ko?." murmushin k'arfin hali yayi kana ya fara rubutu a k'asa. "Ummi wai har kin karaya ne? To ki aro jarumta ki yafa ai komai a hankali yake zuwa, ai mai nema baya fushi, yoh su masu shagunan da kansu wata rana zasu bud'e ko asi basuyiba kuma haka bazaisa gobe su k'i zuwaba, kedai kiyi ta min addu'a in sha Allah, Allah bazai hanani abin yiba." sai ya kuma kalli Rahma dasu Raihana yace. "kuyi tamin addu'a in sha Allah dukkan tsanani tare yake da sauk'i." cikin samun k'warin guiwa, sukayi mishi addu'a. Bayan yaga sun saki Randi sunata hirane sai ya mik'e yad'auki bokiti ya debi ruwa a randa kana shiga d'anshi wanda da shida Nuruddeen ne, farar jallabiyarshi ya d'auka da boxer inshi kana ya fito hannunshi rik'e da kondon wonkanshi ban d'aki ya nufa yaje ya shiga wonka. Ya jima kafin ya fito daga cikin d'an madaidacin bayan gidan nasu da aka lailayeshi da fulo d'in siminti, shaddan na can gefe kana wurin wonkan anyishi da mazaunin siminti da kuma inda zaka ajiye sawunka. A hankali yake tafi bisa dukkan alamu baison kasa ya bud'e mishi sawune, d'akin nashi ya shiga, inda yake gyare tsab sai k'amshin turare yakeyi wanda ishaq ne ke saya musu tare, ko ina a kimtse kodan babu tarkece sosaine, leda carpet ne a malale a tsakiyar d'akin wanda sai Shek'i yakeyi alamun ya wadatu da tsabta sai katifarshi shimfid'e a gefe wanda yasha gyara sai pillows biyu a gefen katifar. can daga k'asa kuma wata yar madaidaciyar durowa ce, inda gefe d'aya ya jera kayayyakinshi dake wonke a goge, sai d'aya side in kuma littafanshi ne a jere daga sama har k'asa kama dana boko na islamiya dana allonsu wanda wasu tun na kakansu ne, sai wani dogon madubi dake lik'e a jikin ginin daga sama har zuwa k'asa dan zaka iya kallon tsawonka duk ta cikin madubin sai wani dan abun aje takalma kana sai fankar k'asa da kuma wani d'an k'aramin randar tabo da sai naso yakeyi alamun ruwan ciki da sanyi sai butarshi a gefe kana can gefen durowar kuma sallayanshi ne ke shimfid'e. Mai ya shafa sannan ya fito tsakar gidan tuni Hayatuddeen ya dawo har yayi bacci hakama su Faruq. Gefen Umminshi ya zauna tare da tonk'oshe sawunshi abincin da Rahma ta ajiye mishi ya jawo, bud'ewa yayi sai ya kuma yi murmushi ganin tuk'ek'k'en tuwan shinkafa da miyar busasshen zogale wanda yasha kifi, gyada, attaruhu, da albasa, wanda aka had'esu da kifi, kana ga wake dasu kayan d'and'ano miyar sai k'amshi take, Allah ya sani Saifuddeen nason miyar zogale shiyasa Umminshi ke yawan yin miyar in dai tanada halin yinta da yake miyar tanada cin kud'i. ledan ruwa d'aya ya d'auka tare da b'ulawa kana ya wonke hannunshi ya fara ci, ita kuwa Ummi ido ta zuba mishi tare da cewa. "Yayanka Adnan yazo ya sallameni d'azu wai zai tafi karatu har Zaria." kanshi ya d'an jinjina alamar Ayyah, sai ya kuma yi mata alamun Allah ya kaishi lfy. Amin Amin tace, bayan ya d'an ci abincin ne ya wonke hannunshi Raihana ta kwashe kwanukan kana ta dawo sukaci gaba da hira. Suna nan a zaune Bappa Ali da Aunty Nina ma suka shigo yi mishi barka da dawowa nan sukayi ta hira. Washe gari da sassafe Rahma ta hura wuta tayi d'umame kamar yadda suka saba, da sauri ta d'auko pillet ganin Saifuddeen ya fito cikin shirin tafiya, yau k'ananun kaya yasa wanda sukayi masifar yi mishi kyau blue Jeans ne a jikinshi sai bak'ar riga mai farin rubutu a jiki, kanshi ba hula hakan ba k'aramin haskashi yayiba, yana shiga d'akin Umminsu tana binshi a baya, bisa kujerarta irin zauna kaci doya nan ne ya zauna, ita kuwa Rahma mik'o mishi fillet d'in tayi kana ta jawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148