Chapter 84
Chapter 84
sannan ya saka wani wondo 3 quarter pink color sai rigarshi mai yankekken hannu white Color, sosai kayan sukayi mishi kyau. Shi kuwa Ahmad a fili yace. "Wato haka Raliya ke fama da rigimar Autan Ummi." dai-dai lokacin kuma ya fito tare da cewa. "Na fito ya Ahmad muyi sallan muje muci abinci yunwa nakeyi." cikin had'e fuska Ahmad yace. "To wa zai tattara maka kayan daka watsar d'in?." kai ya d'an longob'ar tare da cewa. "Ni ban iya tattarewa ba ya Ahmad." tsaki Ahmad yaja tare da cewa. "Zaka ma koya ai, dan nima ban iyaba." sai ya kuma fuskanci al'k'ibila ya tada kabbara ganin haka shima Hayatuddeen yabi bayanshi, bayan sun idar da sallolin nasu ne suka sauk'a reception sukayi tambayar ta ina Restaurant yake nan aka kwatanta musu sannan, suka nufi wurin suna isa sashin. Restaurant ɗin. Mathuramakrishna viswanathun. Hayatuddeen ya isa gaban teburin da yaga an rubuta Africa food, gefe d'aya ya juya inda yaga ansa Nigerians food is ready, sai kuma ya juyo jin Ahmad yana ce mishi, "Ni ka amso min feesh roll,." to yace sannan ya saya musu duk abinda suke buk'ata sannan suka juyo, suna dawowa reception d'in suka gayawa ma'aikatan wurin cewa suna son sayan SIM card, kud'in sukace su kawo zasu sayar musu dan suma suna saidawa, nan suka basu kud'in layukan da kuma kati sannan suka musu register tare da karb'an woyoyin suka saka musu layukan sannan suka saka musu katin, ganin tuni lokaci d'aya layin ya hau yasa suka haura d'akinsu. Suna isa suka zauna a parlour sukaci suka sha, ganin ko kad'an Hayatuddeen bai damu da kanshi dake watseba yasa Ahmad mik'ewa ya tattarusu ya shiga bedroom dasu, nan kuma yayi arba da kayansu daya wancakalar hannunshi d'aya yasa ya tokare k'ugunshi kana yasa d'aya ya dafe goshinsa tare da cewa. "Wayyo ni Ahmad jikan Ahmad naga ta kaina da aka had'ani da wannan sangartaccen Ummin." dole ya kimtsa komai. Shi kuwa Hayatuddeen a parlour ana ya konta tuni bacci ya fara d'ibanshi. Ahmad da ya gama tattara abinda ya watsanne ya dawo parlour ya tada Hayatuddeen tare da cewa. "Ka tashi mu koma asibitin mana." cikin gengyad'i yace. "Ya Ahmad dare yayi sosai fa ka bari da asuba muje." da wannan shawarar ya koma bedroom ya konta. Dan akwai gajiyar tafiya tare dasu. Washe gari suna idar da sallan asuba, suka fito suka kama hanyar da zata sadasu da asibitin, tafiya kad'an suka shiga cikin asibitin. Daga bakin harabar wurin, suka fara tambaya da tambayar suka samu suka isa har office d'in Dr Acash prasat dan dashi suke tambaya, suna shiga cikin wurin suka hango Adnan zaune bakin mashigar inda suka kwana, da sauri suka iso gunshi, Ahmad ne ya fara bashi hannu, bayan sun gaisa ne, yace musu ana mishi wonka ne, jin haka yasa Ahmad ya bashi SIM card d'in da suka saya mishi da key d'in d'akinsu ya kwatanta mishi yace. "Kaje kayi wonka ka samu ka canza kaya ka kuma d'an ci abinci kafin ka dawo, wata k'il Dr yazo." haka kuwa akayi ya amsa ya tafi, su kuma suka zauna koda aka gama kimtsashi. Hayatuddeen ne yaje ya samo mishi abinda zaici, daga nan sukayi ta hira dashi har zuwa lokacin da Ya Adnan ya dawo, nan sukayi ta zaman jira sai bayan azahar Dr Acash yazo, haka sukayi ta bin layin ranar amman ina ranar basu samu damar ganinshi ba, the next day ma haka sukayi ta bin layi, har kusa k'arfe biyar na yammansu sannan suka samu damar shiga. Suna shigar da Saifuddeen Dr Adnan yabi bayansu, d'aya daga cikin nurses da suka shigar da Saifuddeen d'inne ya nunawa Dr Adnan wurin zama, bisa wasu kujeru guda biyu dake gaban wani babban table, wanda d'aya sashin shi kuma kujera d'aya ce, wacce Doctor Acash prasat ke zaune, kekyawan ba indiye ne, fayel d'in da Saifuddeen da nurse ta bashi ne ya fara bubbud'ewa yana duddubawa, yayinda Dr Adnan kuwa ya zauna gabanshi, sauran nurses d'in kuwa suke ta kiciniyar kontar da Saifuddeen bisa wani d'an gado dake gefen doctor. Suna gamawa suka koma gefe suka zauna, Da sauri Dr Adnan ya d'ago kanshi cikin mmki yake kallon Dr Acash da yake mishi mgna cikin yaren hausa. "Tun shekaran jiya Dr Aliyu yace min kun iso, kuyi hak'uri abin ne da yawa." cikin nitsuwa Dr Adnan yace. "Ba matsala, d'azu mukayi mgna da Dr Aliyu ma." juyawa yayi ya kalli Saifuddeen dake konce a rigingine, sai ya kuma meda dubanshi ga fayel d'in, kana ya bud'e poldernsu ya fara 'yan wasu rubuce-rubuce kusan tsawon 4 minutes sai ya kuma ture takardun sannan ya jawo system dake gabanshi still rubuce-rubucen yayi, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Dr Adnan cikin bagwariyar hausarsa da zamanshi da Dr Aliyu ne yasa ya iya yace. "Forko dai yanzu za'ayi mishi gwajin, X-ray CT scan MRI scanning wanda ko wanne d'aya N95,000. ne sai kuma Surgery da ya kamata ayishi kan lokaci d'an yanzuma lokaci ya d'an fara ja,." cikin gamsuwa da bayaninshi Dr Adnan yace. "Surgery d'in kuwa zai kai nawane?." kai ya d'an rusunar sannan ya d'anyi dube-dube a system d'in sannan ya d'ago kanshi ya kalleshi kana yace. "N2.5 million." A hankali Dr Adnan yace. "Ba matsala a fara aiki." mik'ewa yayi ya nufi gaban gadon da Saifuddeen yake a hankali yasa hannunshi ya fara jan 'yan yatsun Saifuddeen amman shiru bai kulaba a hankali ya fara bin k'afafunshi yana d'an lallatsawa still Saifuddeen baya ji bare ya bud'e idonshi, sai yaci gaba da tattab'ashi tare da juyawa ya kalli Dr Adnan dake tsaye bayanshi cikin kula yace. "Naga kurmane shi ko?." kai ya gyad'a mishi da sauri, cikin meda hankalin shi kan Saifuddeen yace. "In ba matsala in kunada hali musa doctor kunne a cikin aikinshi mana." jim kad'an Dr Adnan yayi kana ya d'an matso doctor Acash d'in tare da cewa. "Dr kanaga zai worke ne?." da sauri ya jujjuya mishi kai tare da cewa. "Wannan ai sai Doctord ɗin kunnen ne zasu bamu amsar nan in sun dubashi, sai dai muna zaton zai worke tunda ba haifarshi akayi da kuramtarba ko?." da sauri Dr Adnan ya gyad'a mishi kai tare da mishi d'an k'arin bayanin yadda ya samu larurar kuramta, kamar yadda yayiwa Dr Aliyu a Abuja. dawowa sukayi suka zauna bisa kujerun da suka tashi nan suka fara musanyan basira da shawara a matsayinsu na Doctors, sosai Doctor Adnan ya k'ara samun haske a lamarin sashin aikinshi dan zama da kwararran Dr da yayi na awa biyu. da yawa suna kwarafin cewa shi Dr Acash in an aka shigar da mutun ba'a fitowa da wuri, shi kuwa k'a'idar aikinshi ne ya binciki marasa lfy da kyau a nitse ya kuma samu cikikken bayani daga bakin mara lfyar ko iyayenshi. Shiyasa yake dad'ewa da mutane, shiyasa kuma mutane ke son ya dubasu, anan take ya kira wani doctor da yake kula da sashin kunne. Ba jimawa ya shigo nan sukayi 'yan dube-dubensu, daga bisani nan take aka fara aikin gudanar da gwoje-gwajensu. Saida suka gama duba komai sannan aka fitar dasu, aka kaisu room d'in da za'a kwantar dashi zuwa gobe in sun duba sakamakon awun nasu. nan ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148