Chapter 1
Chapter 1
*NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 1* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Book One ~26/2 2020... 8:06 PM~ *28 February 2020. 9:10 Am* www.ashwarmediahausa.com.ng *BISMILLAHI ina farawa da sunan Allah mai yawan rahma da jink'ai. Alhamdulillahi na godewa Allah mahaliccina daya bani rai da lfy da nitsuwa, da konciyar hankali ya kuma ƙaramin ya buɗa min tunani na ya haskamin nazarina har na samu daman fara wannan sabon littafi nawa mai suna NAKASA BA KASAWA BACE ya Allah ina riƙonka da ka tsare min Al'ƙalami na daga rubuta sharri da abinda zai zamewa bayinka guba ko fitina, ya rabbil izzati ka tsarkake min tunani na ka kame min hannu na daga rubuta wani abinda zai zame min da-na-sa-ni duk ƙanƙantarshi, ya Allah ka bani rai da lfyar gama littafin nan lfy-lfy, dani da masu karatun baki ɗaya* _Wannan shafin forkon nakine ƙanwata kuma mai babban suna Fatima Sardauna, ina tayaki farin cikin gama littafinki SOORAJ lafiya, Allah ƙaro miki basira da hazaƙa, Allah ya bada ladan faɗakarwa_ Nakasarsa bata zama kasawa a gareshi, domin hausawa kance Babu nakasasshe sai kasasshe! ya kasamce mai zarrar da ko lafiyayye marar nakasa bashi da irinta, Rayuwarshi madubine ga dukkan nakasassu, kana abar birgawace ga dukkan lafiyayyu kana abin so da sha'awar ko wanne bawa mai imani a zuciyarshi yadda sunanshi yake haka zahirinshi da bad'irinshi yake *SAIFUDDEEN* Muhammad Ahmadu managarci ne salihi mai yawan fasaha da tawakkali kekyawane irin ken da ke tsantsar haiba. Ɓiggiren tushe da asalinsu Saifuddeen. Asalin su FULANIN DUKKU NE NA JIHAR GOMBE. *DUKKU* wani yankine daga yankunan Gombe wanda ya kasance yankin fulanine masu tsananin kyau uwa uba fulanine masu fafutukar neman ilimi na bankƙare biyu duka wato ilimin Arabic da kuma Boko. Al'ummar Dukku sunyi fice da zarra tako wanna sashin shiyasa, suke ko ina cikin mutane masu daraja masu kima da cikar kamala. *DUKKU diyam sad'i na kosam* Malam Ahmadu shine kaka gasu Saifuddeen, Malamu Ahmadu asalin bafullatanin Dukku ne gaba da baya, nannen tushensa iyaye da kakanni, babban Malami da babu kamarshi a fad'in Dukku a waccan lokacin. Mafi akasari yaran garin a gunshi suke karatu, dan yanada tsankgaya mai girma , sai dai shi baya tara al'majirai, kowa yazo yayi karatu kana in an tashi kowa ya koma gida, shiyasa yaran anguwannin nesama suke zuwa karatu, kamar yaran Sirinkiyo, Katafila, Fada, da nan Dugge, kai wasu daga shabewa ma suna zuwa makarantar, wanna yasa ya shahara a cikin Dukku domin masarautar Dukku da kanta tanaji dashi, domin shine limamin masallacin fada. Allah ya azirta shi da kadararorin filayen cikin garin Dukku da tarin gonaki wanda yawan cinsu ya gajesu ne a wurin mahaifinshi wanda sune suka sari dajuka da tsaunikan Dukku da kewaye kasan cewar wancan lokacin ba'a saida gonaki saida ka shiga daji ka sari fili ka gyarashi shike nan ya zama naka wahalakar ya mallaka maka shi. Malam Ahmadu yanada matarsa d'aya mai suna Bintu Allah ya azurtasu da yara uku. Babban d'ansu sunanshi Muhammad Bella shine mahaifinsu Saifuddeen, sai mai binshi Aliyu sai autarsu Aisha suna kiranta Dada. Sun taso cikin had'in kai da tausayin juna, babu raini ko kad'an sai girmamawa da tausayawa. Yayiwa yaranshi maza aure. Bello mahaifinsu Saifuddeen kenan mutun ne mai mutunci da kamala yanada nitsuwa shiyasa aka had'ashi aure da d'iyar goggonshi mai suna Fatima amman ana kiranta da Bisije, yaranta ku su Saifuddeen suna kiranta Ummi. Ummi kenan, wacce mahaifiyarta k'anwar Malam Ahmadu ne, Ummi marainiyace dan rana d'aya ta rasa iyayenta saka makon gobara da ya cisu dere d'aya, ita kuma lokacin an kaita yaye gidan kakunsu, shiyasa ta tsira, ba nisa tsakaninmu kakanin nasu suka rasu, shiyasa rik'onta ya dawo gidan Malam Ahmadun kawunta kenan. Bello ya rayu da matsalar makarai tattare dashi, wanda yakan tashi time to time yana matuk'ar wahal dashi shiyasa, iyayenshi suka zab'i a had'ashi da Bisije Ummin kenan anaga tunda yar uwarshi ce zatayi hak'urin zama dashi, bayan an gama yin komai na buk'atun hidimar aure, sannan akayi auren Bisije da Bello, anyi biki lfy an watse lfy. Ranar da aka watse abokan Bello na shirin rekoshi gidanshi inda yayi gina cikin asalin family house in nasu. kawai sai suka sameshi ya toni rami mai zurfi kana ya had'a k'irarai ya shirga itatuwa ya hura wuta, wai zai fad'a ciki, nan abokanshi Ashiru da Hamisu sukayi kanshi da gudu suka kamashi, sai fizgewa yakeyi wai su barshi zai fad'a cikin wutar yana me ce musu. Wai a k'asan wutan al'jannace su barshi ya fad'a ciki. Wannan abu ya tada hankali yan uwa da abokan arzi a daren ranar dole Hamisu da Ashiru, a gidanshi suka kwana don in an barshin zai kashe kansa, sabida makaranshi ne suka motso, k'aninshi Aliyu da Dada kuwa sai rarrashin Amarya suke, wacce taketa kuka. To mafarin bak'in cikin Ummi kenan tun randa aka watse bikinta ta fara shiga toskun rayuwa sabida, daga ranar duk bayan wata biyar sai cutar Bello ta tashi wani lokacinma yakan tashi sau uku a shekara, sai dai Alhamdulillahi abun baya sashi duka ko fad'a sai dai yakan tashi tsakiyar dare yayita yawo yana zagaye cikin garin Dukku, kana duk inda ya samu masallaci sai ya tsaya yayi sallah raka'a biyu. Sannan yana tafiya yana karatun qura'an da k'arfi. Kafin gari ya waye sai muryarshi ta disashe, kana sawunshi su kumbura. Mahaifinshi Malam Ahmadu dama yan uwanshi kab suna nema mishi mgn amman Allah baisa anyi dace ba. Haka shekaru sukayi taja Ummi tana ta hak'uri da d'an uwanta mijinta, koda kawunta yayi yunk'urin raba auren sai tayi ta kuka tace ita kam a barta dashi, acewarta in ita ma 'yar uwarshi ta gujeshi wa zai zauna dashi, dole Malam Ahmadu ya barsu yana mai ci gaba da yiwa d'anshin addu'ar samun lfy. Har tsawon shekaru da dama, inda Allah ya azurtasu da yara shida uku maza uku mata. Nuruddeen shine babba sai Rahma, kana Saifuddeen sannan Raihana sai Raliyya sannan Auta Hayatuddeen sakalin Ummi da Hamma Saifuddeen. k'anin Bello Kuma Aliyu har yau matarsa bata tab'a koda b'ariba. su Nuruddeen na kiranshi Bappa Ali, kana Dada ma tayi aure suna kiranta Goggo Dada. Ita kuma tunda tayi haihuwar fari bata kumaba, Ahmad shine sunan d'an nata kuma sa'an Saifuddeen ne. Ana cikin haka ne kuma Allah yayiwa Malam Ahmadu rasuwa. mahaifinsu Abba kenan daga ranar kula da d'aliban ya dawo hannun bappa Ali, da kuma Abban in yana cikin haiyacinshi. kafin bintu ta fita takaba ne itama Allah ya mata rasuwa sakamakon cutar murd'a na dare d'aya. Daga nan Abba da bappa Ali da goggo Dada suka k'ara ruggume juna bisa amana da gsky da tausayawa d'an uwan nasu. Yara kuwa sun fara girma ciwon mahaifinsu na ci musu tuwo a kwarya musamman Nuruddeen da Raihana sai Saifuddeen wanda a lokacin yakeda shekara goma sha uku kana ya gama primary school inshi, har yaci gaba da secondary school inda yake JSS 1 shi kuwa Nurruddeen tuni yayi nisa yana Ss 3 Raihana Ss 2 da yake tsakaninsu da Saifuddeen akwai 'yar tazara, a gefen Arabic kuwa tun sunada shekara goma sha bbbiyu sukayin sauk'an alƙur'an mai girma. So tuni Saifuddeen ya sauk'e Qur'an tun shekarar data gabata lokacin kanninsu na raye dan yanada 12 years yayi sauk'a kamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148