Skip to content

Chapter 88

Chapter 88

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

dafa kafaɗansa ya sanyashi buɗe idanunsa ya sauƙesu akan laɓɓan Dr.Adnan, Dr.Adnan kuwa ganin Saifuddeen na kallonsa ya sanyashi cewa. "Yajikin naka?" Kyakkyawan murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, kansa yaɗan jinjina alamar da sauƙi, tare dakai dubansa ga Hayatuddeen dake tsaye ya kafesa da ido, murmushinsa me kyau yayiwa Hayatuddeen tare da miƙo masa hannunsa, ganin haka yasa Hayatudden cikin tsananin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa yataho garesa tare da miƙa masa hannu shima, damƙe hannun Hayatuddeen yayi acikin nasa hannunsa tare da lumshe idanunsa, sosai yakejin son ƴan uwansa acikin rai da zuciyarsa, tabbas yasan Allah shine gatan kowani bawa, amma kuma yasan duk wani buri da fatan ƴan uwansa akanshi yake, shi musulmine da ya yarda da ƙaddara me kyau ko akasinta, haka kuma yayi imani cewa komai ya faru da bawa muƙaddarine daga Allah, Sake rufe idanunsa yayi kirif yayinda zara zaran eye lashes ɗinsa suka kwanta luf aƙasan idanunsa, gashin giransa kuwa sai shinning yake kamar wanda aka shafawa mai, uwa uba ga tohon sabon gashi na tattausan sajen da ya fara yiwa fuskarsa k'awanya, sosai fuskarsa tayi fayau da ita hasken fatarsa yasake bayyana, haƙiƙa Saifuddeen kyakkyawane sosai, sannan duk da nakasar dake tare dashi komai nasa abun burgewa ne da so, ganin kamar yayi bacci ne yasanya Dr.Adnan duban Ahmad da Hayatuddeen cikin kulawa yace. "Yakamata ace kuje ku nemi masauƙi tunda Dr.Acash yayi mana komai ya kuma sama mana nurses ɗin da zasuna kula dashi, sannan gani ni zan zauna atare dashi." Jinjina kai Ahmad yayi tare da duban hayatuddeen da har yanzun hanunsa ke cikin na Hamma Saifuddeen ɗinsa. "Mutafi ko Hayatuddeen, naga idanunsa arufe inaga yasamu bacci". Ahmad yafaɗa yana me kallon Saifuddeen. Kallon Hamma Saifuddeen ɗin hayatuddeen yayi,cike da tausayin ɗan uwan nasa ya soma yunƙurin zare hannunsa dake cikin nasa, har acikin ransa yakejin tausayin Hamman nasa, tabbas shikam da ace ana sauya ƙaddara, to da tuni ya sauya ta hammanshi daga mummuna izuwa kyakkyawa. Haka Hayatuddeen da Ahmad suka baro cikin asibitin don nemawa kansu masauƙin da zasu zauna, taxi suka shiga inda suka ce yakaisu hotel wanda yake mafi kusa. Tafiya kad'an sukayi kana motar ta ratsa cikin Ƙofar katafaren hotel d'in. Sahar International Mumbai, mai taxi din ya sauƙesu, hotel ne ƙawatacce me kyaun gaske wanda yake ɗauke da dogon gine gine gwanin burgewa. Kallon Ahmad Hayatudden yayi bayan sun sauƙa daga taxi ɗin sun biya me taxi ɗin kuɗinsa, cikin yanayi naɗan damuwa yace. "Ya Ahmad baka ganin wannan hotel ɗin zaiyi tsada da yawa? ka duba kyawunsa fa". Ɗan jim Ahmad yayi tare da ɗaga kansa yana ƙarewa hotel ɗin kallo, asanyaye yace. "To Hayatuddeen ya zamuyi, dole haka zamu kama saboda shikaɗaine zai sauƙaƙa mana wahalan zuwa asibiti, kaga idan bashi ba ko ina muka kama sai munyi ta cacan kuɗin transport, kaga kuma wannan ma ƙarin ɗawainiya ne". Kai Hayatuddeen ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman Ahmad, atare suka jera har zuwa cikin hotel ɗin inda suka tsaya a receiption. saida sukayi duk wani abun daya dace kana suka biya kuɗi sannan aka basu makulli da kuma nomban ɗakin da suka kama, tafiya suke suna me dudduba nambobin ɗakunan har suka iso ɗakin dayake da namba dai-dai da wanda aka basu, Ahmad ne yasanya key ya buɗe ƙofar ɗakin, Hayatuddeen na biye dashi abaya haka suka shiga cikin ɗakin, amatuƙar gajiye hayatudden ya faɗa kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin, wanda ke ɗauke da wata luntsumemiyar katifa me laushin gaske, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonsa Ahmad yayi tare da girgiza kai aransa yana me cewa . "Allah Ya shirya mana kai Auntan Ummi". kasancewar agajiye suke su dukansu, yasanya Ahmad soma ɗan rage kayan jikinsa kana ya wuce bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala don gabatar da sallan magriba wanda daf ake da cikar lokacinta, yana fitowa daga cikin bathroom ɗin yaci karo da wandon Hayatudden daya cire yayi wurgi dashi atsakiyan ɗakin, gefe kaɗan ma rigarsa ce wanda ya cire a yashe, cike da takaicin halin Hayatuddeen Ahmad ya girgiza kansa tare da ƙarasawa gaban mirror, don yasan idan yace da Hayatudden ya ɗauke kayan nasa daga ƙasan ma, wani sabon sakalci ne zai tashi, hakan yasa ya ƙyaleshi yashiga fito da kayansa dake cikin jaka don zaɓan wanda zai saka. Haka dai cike da sangarta Hayatuddeen ya wuce bathroom shima yayi wanka tare da ɗauro alwala, koda ya fito awankan kamar yanda ya saba haka ya zazzage kayansu dake cikin jakan kaf akan gado, shidai Ahmad yana kallonsa bai kulasa ba, don yasan me hali baya taɓa fasa halinsa, riga da wando na jeans Hayatuddeen yasanya cike da sakalci ya dubi Ahmad dake ƙoƙarin rufe kwalban turaren dake hannunsa, ɗan ɓata fuska yayi tare da shafa cikinsa cikin murya me ɗauke da gajiya yace. "Yaya Ahmad nifa gaskiya yunwa nakeji, gashi bamu sayawa su Hamma Saifuddeen abinci ba!" "To acici kai-dai baka da wani zance saina ci, yanzun idan mukayi sallah sai munemi waje mafi kusa musai abinci mukai musu, don tabbas nasan zuwa yanzu dole zasuji yunwa". Ahmad yafaɗa yana me ƙoƙarin saka takalmi aƙafarsa. Shi kuwa Hayatuddeen bai sake cewa komai ba har Ahmad yagama kimtsa kansa suka fice daga cikin ɗakin, cikin harshen turanci Ahmad ya tambayi ma'aikatan dake aiki a hotel ɗin inda zai samu abinci, dayake babu wani nisa tsakanin hotel ɗin da kuma inda ake sai da abincin hakan yasa ɗaya daga cikin ma aikatan yayi musu kwatance, saida suka fara zuwa wani masallaci da ke nan kusa suka gabatar da sallan Magriba, daga Hayatudden har Ahmad babu wanda daya kafa goshinsa aƙasa ba tare da yayiwa Saifuddeen addu'ar samun lafiya ba, suna idar da addu'o'insu suka nufi inda zai sadasu da inda ake saida abinci. Koda suka ƙarisa wajen cin abincin, waje ne me kyau da tsabta sannan babu irin abincin da babu awajen, cimar Nigeria sukaci, inda Ahmad yaci Fish roll and gas meat, shikuwa Hayatuddeen yaci roasted fish da kuma damammiyar madara me kaurin gaske, daganan takeaway sukayiwa su Dr.Adnan da Saifuddeen, kasancewar tsakanin hotel ɗin da asibitin babu wani nisa sosai hakan yasa da ƙafansu suka shiga takawa har zuwa privet hospital ɗin. Kaitsaye inda su Hamma Saifuddeen din suke suka nufa, abakin ƙofar ɗakin da Saifudden ɗin yake suka hango Dr.Adnan tare da Dr.Acash prasat, da alama magana suke mai mahimmanci, tsayawa sukayi daga gefe har saida suka kammala maganan kafun suka ƙaraso, kallon fuskan Dr. Adnan sukayi su duka, cikin yanayi naɗan damuwa Ahmad yace. "Akwai matsala ne?" Kai Dr.Adnan yagirgiza tare da cewa. "No babu wata matsala, sai-dai bayanzu zamu samu ganin doctors ɗinba aƙalla sai munshare kwana biyu kafun mugansu, Dr.Anan Mehta, ƙwararren likitane a ɓangaren Orthopeadic surgeon, sai kuma Dr.Mahesh Khurana, wanda shima ƙwararrene afannin neurosurgeon, muna da buƙatan ganin wad'annan likitotin don kuwa sune masu kula da irin lalurar Saifuddeen, fatanmu akullum dai shine Allah yabashi lafiya". Da. "Amin Amin". suka amsa su dukansu, ko wanne zuciyarsa cike da tausayin Saifuddeen. Ganin rauni nashirin bayyana akan fuskokinsu ne yasanya Dr.Adnan karɓan takeaway din hannunsu kana yace su koma masauƙinsu su huta sai kuma zuwa da safe idan Allah yakai rai, bazasu musa masa ba domin

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148