Skip to content

Chapter 102

Chapter 102

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

da sukayi, ganin yadda Raihana ke kuka yasa Saifuddeen mik'o mata hannu, aifa da gudu ta iso inda yake kawai sai ta durkusa dirsham har k'asa ta kafa guiwowinta kana ta kifa kanta bisa cinyarshi tare da yin zazzafan kuka, kawai duk sai suka had'e kai a wurin. Suna kukan farin ciki da tausayawa d'an uwansu. Salisu ne yayi saurin isa inda suke ya janye Hayatuddeen da Faruq, yayinda Ahmad kuwa ya janye Raliyya, Ya Adnan kuwa ya gaza ce musu komai, Ishaq kuwa, yana zuwa ya ruggume abokin nashi, ganin airport d'in yayi musu kad'an wurin farin cikinsu yasa suka, shiga motocin suka tafi, Adda Rahma kam fir taki yin nesa da k'aninta a motar ya Adnan suke ita da Saifuddeen suna baya, Ishaq kuma na gaba. Hayatuddeen kuwa da Faruq da Raliya motar ya Ahmad suka shiga. Salisu kuwa kuwa shi ya kwashi kayansu shida Raihana. Daga airport zuwa cikin gombe akwai yar tazara, so tafe suke suna hirarsu ta yan uwa shak'ik'ai. Cikin tsananin mmki Hayatuddeen yake baza ido lokacin da suka shigo cikin gari sabida, Sosai yaga sauye-sauye a garin. Hakama da suka iso gida Saifuddeen da kanshi yayi mmkin ganin zubi da tsaruwar gidan, Komai yayi shar tsirran da shuke-shuke sunyi lip-lip gwanin sha'awa. Anayin parking Hayatuddeen ya fita da sauri, kai tsaye cikin gidan ya nufa a guje. Ya Adnan kuwa yana fitowa ya bud'ewa Saifuddeen k'ofa kana ya bude but d'in motar ya fito da weelchair d'in. A gab da kofar motar ya ajiye kujerar, yayinda tuni Adda Rahma da da Ishaq suka fito. Hakama su Raihana ganin duk sun zagayeshi sun mishi zobene, yasashi lumshe ido kana ya zuro k'afafunshi wojen tare dasa hannunshi ya dafa gefen motar sannan ya yunk'ura ya taso cid'ak cikin azama da jarumta da zafin nama ya zauna bisa weelchair d'in. Wani irin nannauyan ajiyan zuciya Adda Rahma ta sauk'e da tsananin k'arfi dan da gani take kamar bazai iyaba. Faruq kuwa da sauri ya tsuguna ya saita matakalar kujerar, wani lallausan murmushi Saifuddeen yayi kana da taimakon Ahmad ya d'aura fararen sawunshi kan abin takawan. Salisu kuwa tuni ya firfito da kayayyakinsu ya nufi cikin gida dasu. Shiko Saifuddeen girarshi d'aya ya d'agawa Ahmad alamun tammayar ya dai ganin duk sun tsaya a kanshi. Cikin tsananin tausayi da k'aunar d'an uwan nashi yace. "Ai kaine jagoran." lip inshi na k'asa ya d'an tauna ta gefe kana yasa hannunshi ya share hawayen dake bin fuskar Raihana sannan yasa d'aya hannunshi dai-dai wurin masarrafin weelchair d'in ya d'an daddana wasu madannai sai ga keken ya fara tafiya a hankali. da sauri sukabi bayanshi. Da sauri ya danna wani pin d'in sabida ganin Baba Ado mai gadinsu da Sule direbanshi sun rusuna gabanshi. Sam sule ya gaza tsaida ruwan hawayenshi dan kamar yau yana tuna randa sukayi fitarsu ta k'arshe in da uban gidan nashi ya taka da sawunshi, sai gashi cikin shekara d'aya ya zama bashi da damar tsayuwa. kai ya d'an jujjuya musu alamun suyi hak'uri su bar kuka. da kyar suka iya tsaida hawayensu kana suka mushi sannu da hanya da fatan samun lfy. Hayatuddeen kuwa yana shiga parlour yayi tsalle ya fad'a kan kujera 3 str gefen Umminshi sai ya kuma ruggumota ta baya tare da cewa. "Wayyo dad'i yau gani ga Ummi na." Sosai Ummi ta ruggume autan nata tana maijin son yaran da begenshi. Goggo Dada ce ta kalleshi cikin son yaran d'an uwan nata tace. "Wato Umminka kawai ka gani ko?." Da sauri ya juya zuwa gareta. Dai-dai lokacin kuwa su Saifuddeen suka shigo, wani irin farin cikine mara misaltuwa ya rufe Ummi wanda ta kasa koda motsa yar yatsarta, sai bugawa da zuciyarta keyi da k'arfi-k'arfi. Shikuwa Saifuddeen k'ara gudun weelchair d'inshi yayi ya saitata gaban Ummi. Yana isa inda take gab da ita tayi saurin mik'o mishi hannu, da sauri ya kamo hannun nata duka biyu kana ya tallabe fuskarshi dasu, haka nan rauni zuciya suka rintsa mishi zuciya bai taba zubda k'walla akan wannan larura tashiba sai yau. Kawai sai yaji wasu zafafan hawaye suna kwaranyo mishi, da sauri ta mik'e tsaye ta matso gab dashi hakan ya bashi damar sahannunshi duka biyu ya ruggumeta tare da manna kanshi a cikinta, wani sautin kuka mai cike da raunin d'a a gaban mahaifinshi ya sake. Tuni itama Ummi kukan takeyi tamkar zata shid'e, Raihana kuwa kife kai tayi bisa cinyar goggo dadansu tana kuka da majina. Yau Adda Rahama mai dauriyarma kuka takeyi wi-wi. Raliya kuwa jikin mijinta ta fad'a cikin rauni take cewa. "Ya Ahmad kace suyi shiru, ya zamuyi da k'addararmu da munada dama da tuni mun canza k'addarar Hamma Saifuddeen." ina shima kanshi Ahmad hawaye yakeyi. Ya Adnan ne yayi k'arfin hali cikin d'an d'aga sauti yace. "Kiyi hak'uri Ummi, addu'a shi ya dace da Saifuddeen ba kukaba, da ace kuka na mgni ai da tun kan yau Saifuddeen ya worke." A hankali Ummi ta gyad'a kai kana tasa hannu ta d'ago kan Saifuddeen. murmushi tayi mai had'e da hawaye hannu tasa ta share mishi hawayenta. cikin rawan murya tace. "Baba kada ka mance furucin yayanku, koda ya mutu baya raye ai furucinsa bai mutuba." rimtse idanunshi yayi da k'arfi kana ya bud'esu a hankali. kafad'unshi ta dafa cikin tausasa lafazi tace. "Ae ita Nakasa ba kasawa bace. Da nakasarma ka zame mana jigo garkuwa gata a garemu, ka meyewa k'annenka gurbin uba ni ka zame min uwa uba yaya k'ani d'a kuma abokin kukana." kai ya jinjina mata alamun gamsuwa, Goggo Dada kuwa Raihana ta lallasa kana Ya Adnan yayi musu nasiha mai ratsa jiki, daga bisani yayi addu'ar samun lfy ga Saifuddeen sannan shida Salisu suka fita suka tafi. Ummi kuwa da kanta ta mik'e taje kawowa Saifuddeen ruwan sanyi, Bayan yasha ruwan ne duk sun gaggaisa, tare da mishi sannu da hanya, sukaje Dinning table sukayi breakfast dan suma gidan duk babu wanda yayi karin kumallo. Sosai suka cika musu gaba da abubuwan ci da sha namusammam. Ummi da kanta ta zubawa Saifuddeen tuwon farar d'anyan shinkafa, miyar zogale wanda yasha man shanu da kifi da busasshen nama, cikin kula Ummi tace. "Nida kaina nayi maka girkin dan nasan kayi begen miyar da ita kafi so." murmushi yayi tare mata alamun godiya da jin dadi kana ya fara cin abincin da yayi begenshi sosai. Hayatuddeen kuwa couscous da miyar hanta Adda Rahma ta sa mishi. Ummi kam ji takeyi kamar ta bawa Saifuddeen abinci a baki sabida yadda yakeci wanda dama halittarsa kenan rabin malmalan yaci, kana ya cire hannunshi tare da jawo jug d'in damemmiyar fura da nono mai sanyi da zuma, da Sauri Goggo Dada ta tsiyaya mishi a kofi ta mik'a mishi. Hayatuddeen kuwa kular pepper chicken ya jawo kamar kura yayi ta yagan cinyoyin kaji saida yayi hanik'an sannan ya mik'e ya koma tsakar parlour. Su kuwa su Ummi babu wanda ya iya cin komai saida sukaga Saifuddeen ya k'oshi, sannan sukaci, suna gama duk suka dawo parlour akaci gaba da hira. Suna cikin hirar Bappa Ali da Malam Ashiru da Baba Hamisu suka iso. Nan kuma aka gaggaisa tare da yiwa juna barka, karshe dai su Ummi d'akinta suka koma d'akinta. Dan Su Mudassir, Jabeer, Hisham, Kabiru, Salisu, Ishaq,

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148