Chapter 75
Chapter 75
meyasa ban aurar dake ba, na barki kinata gallafiri a gari sai kije gidan radio kiyi ta zuba kid'e-kid'e kina waƙe-waƙe kamar zabiya, to na baki shekara guda." cikin jin dad'i Zaleeha ta gyada kai dan ita a ganinta ai bata da matsala shekara guda aka bata so sai takega ai lokacin da tsawo lokacin ya isheta ta nemo inda yake tasan halin da yake ciki ta bashi tukuicin aurenta bisa kareta da yayi ya zame mata Garkuwa ya saida ranshi a kanta, to me take dashi da zata bashi a duniya in banda kanta ta hanyar haure tayi mishi biyayya ta faranta mushi ta haskaka mishi dararen rayuwarsu. Aminu kuwa tsawa ya daka mata tare da cewa. "Baki da bakin amsawa ne sai mgna da kai?." cikin tsoronshi tace. "Na amsa fa Ya Aminu." tsaki ya d'anja kana yace. "Wallahi Allah kenan, kada kiyi kuka da kowa kiyi kuka da kanki in har kika bari akaje matakin da Baba Malam zai miki zabi, kin sani muddin yace eh to eh d'ince har gaban abadan in kuma yace a a to a ance, dana gaba ake gane zurfin ruwa kin daiga Maryam gata a gidane tana kuma da yara har biyu dan haka kada kiyi wasa da damarki ki fito da zabinki in kin tsaida goni dai babu mai miki dole." cikin sanyi tace. "To ngd Ya Aminu." sai ta kuma kalli Mahaifin nasu cikin sanyi da tsantsar biyayya tace. "Ngd Baba Malam Allah ya k'ara girma, ya jik'a magabata." "Amin Amin Allah ya muku al'barka ya tsareku da sharrin shaid'an da fitinar zamani." ya fad'i yana gyara zamanshi, domin yana jin dad'in addu'ar da yaranshi kewa iyayenshi haka yana nuna mishin koda bayan ranshi zasu kasance mishi al'waladul saliha. Ita kuwa Zaleeha sai ta kuma kalli Ya Habu tare da cewa. "Ya Habu ga car Key inka." amsa yayi yana hararanta kana yace. "Ni naso ace wata biyu za'a bata ai." hannu Baban nasu ya d'aga mishi kana yace. "Aminu yi mana addu'a." Addu'a yayi musu kana suka tashi daga taron. ita da Mamanta suka wuce side din Maman, Maryam kuma tabi bayan Mamy, kana Aminu da Ahmad kuwa, suna zaune gaban Baba Malam suna tattauna kan lamarin Zaleehan, ganin mangrib ta gabato yasa sukayi al'wala suka nufi masallacin dake cikin gidan nasu. A falo suka samu d'an wani matashi wanda bazai wuce sa'an Hayatuddeen ba, yana ganin Zaleeha yazo gabanta tare da cewa. "Dan Allah Zaleeha sammin motarki mana." hararanshi tayi tare da cewa, "Lallai kam Zakariyya ni zan baka motata wacce nima ko hawanta banba kai ko key d'intama Ya Ahmad bai banba nima yau da ta Ya Habu naje wurin aiki, yanzune dana dawo ne naga motar a parking lot." harara ya watsa mata cikin tsama irinta sak'o da sak'o yace. "Kada Allah yasa ki bada, kawai dan na tambayeki sai kita min ihu a kai." cikin huce haushinta a kanshi tace. "Ni zaka cewa ina maka ihu a kai ni mahaukaciyace da zan maka ihu." Gwalo ya mata tare da cewa.. "To da banne? Ba gashiba daga mgna kin fara zubda ƙolla." juyawa tayi ta kalli Mamansu data zuba musu ido tana dariya dan yanzu in ta shiga zasu nuna mata itace bare inda sabo kowa yasan Zaleeha da Zakariyya, shida hatta abo kanshi sun medata abokiyar wasansu. ganin Maman tana murmushi yasa tace. "Mama kina jinshi yana cemin mahaukaciya, kuma kina dariya." cikin muryar rashin fara'a tace. "Kunfi kusa." shi kuwa Zakariyya dariya yayi tare da cewa. "Ni barima in koma." zama tayi bisa stull din dake tsakiyar falon kana tace. "Da yafi maka kam, d'an ci rani kawai, gwara ka koma can wurin tsohuwar nan data sakaltaka kuyu fama da wannan tsukekken anguwar taku dake saman dutse." zama yayi kusa da ita tare da cewa. "Tab kaji yarinya nida gidanmu harda cemin d'an cin rani, toma na fasa tafiya." murmushi tayi tare da share hawayenta dake zuba duk sanda ta tunoshi kai ta sunkuyar kana tace, "Rainon kaka kawai". Oho dai na fiki shanawa Baba malam yana ji dani tunda na girma gaban tsohuwarshi bakiji har cewa yake nine zan samu irin tarbiyarshi." cewar Zakariyya, ita kuwa Zaleeha wayarta ta duba tare da cewa. "Rainon sakalci ba, naga hatta abo kanka sakalallune." dariya yayi kana yace. "Oho dai na yarda ni goyon kakane, inje ƙasar da nakeso da ƴar tsohuwata." baki ta tabe kana tace. "Yaro kai ke jiran wani ya biya maka ni in naga dama al'bashi na zai kaini ." murmushi tayi tare da cewa. "Daga baya Keenan." Gefenta ya zauna kana yace. "Yauwa Adda Zaleeha kin tuna wannan abokin nawa Hayatuddeen wanda kwanaki kuka had'u a gidan kaka yaje wurina?." jim ta d'anyi kana tace. "Yes na tunashi wani kekyawan yaro shima sakali irinka." da sauri yace . "Eh shi dai." aje wayarta tayi tare da cewa. "Har yace min shine d'an auta a gidansu shiyasa akeji dashi." Cikin sauri Zakariyya yace. "Yesss kin gane." sai ya kuma yayi kalar tausayi tare da cewa. "Ayyah to shine nakeso inje gidansu. Yayanshi ba lfy, suna Abuja yace ba mmki ma su wuce India, to shine zanje in gaida wata yayarshi Raliyya irinki." cikin sanyi tace. "Ayyah Allah ya bashi lfy, kaje wurin. Ya Ahmad ka amshi Key din." tsalle yayi tare da manna mata kiss a goshinta tare da cewa. "Yesss my lovely Aunty faratu." ajiyan zuciya tai kana tace. "Yayi kyau dan na bakane zaka cemin faratu ko?." bazan sakeba yace yana mai fita, da sauri tabi bayanshi kana tace. "Yauwa Zakariyya ga kud'i in kana dawowa dan Allah ka saya min feesh roll." ba musu ya amshi kudin kana yaje ya amshi key din sannan ya tafi. Ita kuwa saida ta wasa ruwa sannan ta nufi side d'in Mamy inda ta samu Ya Ahmad da Maryam suna cin abinci. Gefen Maryam ta zauna tare da cewa. "Ya tafi ko?." Ahmad ne ya d'an kalleta tare da cewa. "Waye d'in?." jujjuya kai ta d'anyi tare da lek'a hanyar shiga sannan tace. "Wannan masifeffen mijin nata mana. Shi komai in ansa dashi sai ya zak'e ya rink'a rabka over acting." tab'e baki Maryam tayi kana tace. "Kamar a kunnenshi kika fad'i yaseen zan fad'a mishi." ido ta zazzaro tare da cewa. "Dan Allah rufa min asiri, wannan saggamin yanzu zaice zai gwada gwanjinshi a kaina." dariya sukayi sannan daga bisani Ahmad da Maryam sukayi ta bata shawarar kadafa ta bari ta k'ure Baba malam, suna nan sunata hira Zakariyya ya dawo nan akaci gaba da hira tare dashi, sai dai sam Zaleeha bata tare dasu har Ahmad ya fahimci hakan , so sai ya danganta abin da ko mgnar auren da akayi matane, sai daga baya Maryam ta mik'e ta tafi side d'in mamansu nan suka d'an tab'a hira kana, suka fito dan tafiya gidan ganin Ahmad ya fito zai maida Zakariyya gidan kakar tasu da yake shi tun yaye yake hannunta, ganin dare ya d'anyi ne yasa Aminu cewa, Ahmad ya bari zasu biya su sauk'i Zakariyyan. *** Asalin ahlin Zaleeha. Malam Bashir Suleiman Dukku asalin haifeffen garin Dukku ne gaba da baya, Malami ne wanda yakeda cikar haiba da kamala, Su uku ne a wurin iyayensu babban yayansu Malam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148