Chapter 130
Chapter 130
tsaye ya fita. Yana zuwa yayi musu jagora har zuwa parlour'n Baba Malam ɗin, sunyi farin cikin ganin juna sosai. Bayan sun gaisa ne tare da ɗan taɓa hira, sai Bappa Ali ya ɗan gyara zamanshi tare da yin gyaran murya kana ya fito da damin kuɗi kimanin dubu ɗari cas, daga cikin aljihun babbar rigarshi, miƙa kuɗin yayi wa Malam Adam tare da cewa. "To ga aiken ɗana Saifuddeen ga sadakinshi." cikin sakin fuska Malam Adam ya karɓa tare da cewa. "Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi. Yasa ayi damu." "Amin Amin." suka amsa baki ɗaya, sai kuma suka kalli Dirankadi da yace. "Tofa ɗalibin naka yace yanzu sauran a saka masa rana kawai." Murmushi mai kama da dariya sukayi baki ɗayansu, sannan Malam Adam ya kalli amininshi Baba malam da yaketa murmushin jin daɗi yace. "To Malam Bashir me kace kan batun saka ranan?." Kanshi ya ɗan rausayar ya kalli babban ɗanshi mafi soyuwa a zuciyarshi, kana kuma ɗansa mai tsananin biyayya da kare mutuncinsa, sannan ya kalli ɗan ɗan uwanshi kuma surkinshi mai kare daraja da martabar ahalinshi wato Ameenu kenan, yace. "To ga yayun Zaleeha nan mu basu dama muga irin dattakunsu mana." da sauri Ahmad ya ɗago kanshi ya kalli mahaifin nashi sai kuma yayi sauri yayi ƙasa da kannasa tare da cewa. "Baba malam in dai kuna raye ai mu bamu da bakin mgn, sai abunda kukace." sosai Ahmad ke burge su Bappa Ali yanayin biyayyarsa tamkar Saifuddeen. malam Adam ne ya ɗan kishin giɗa kana ya kalli Ahmad da Aminu yace. "To Ahmad mu ɗin tabbata zamuyi ne?." A hankali ya jujjuya kanshi yana mai jin tsoron randa zai rasa iyayenshi. Shikuwa Malam Adam cigaba yayi da cewa. "To kaga shiyasa muke jawoku a jiki dan mu nuna muku yadda ake aiwatar da komai na jagoranci, a matsayinku na manya wanda dole wata rana kune a madadinmu, yanzu dole zamu so muga yanayin dattakunku, tunda dai kusan komai kuma kunga an kawo ko wani abu na al'ada kama daga gishiri da goro da lefe da kayan rufi, kana yanzu kuma kunga sun gabatar da abinda shariya ta zantar sun kuma buƙaci a saka ranar biki, to yanzu dattakunku muke son gani, kai Aminu kaine Babba kan Ahmad yaushe nene kakega za'ayi bikin?." A hankali Ya Aminu ya ɗan rusunar da kanshi sai kuma ya kalli Ahmad, kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa. "Ashirin da bakwai ga wata mai kamawa. Yayi ko?." A hankali Baba malam ya fidda sassauƙan numfashi tare da cewa. "Yayi kyau, to Amman meyasa har wata ɗaya, baku shirya bane?." Cikin nitsuwa Ahmad ya kalli mahaifin nashi tare da cewa. "Eh to Baba malam mun shirya amman bamu gama shirin ba. Nanda kwana biyar zan koma Abuja, sannan inada zirga-zirga tsakanin ƙasashe da dama Dubai, India, US, Korea, Egypt. Yanzu dai in na fita zan ɗan kwana biyu kafin in karkato Nigeria, kuma inaso inyiwa Zaleeha kayan ɗaki mai kyau zan bata zabi kayan ƙasar da takeso, zan gama saya mata komai a online sannan nasan cikin sati biyu jirgi zai iso dasu nan, to shiyasa nake son ya kai wata ɗaya." murmushi Dirankadi yayi tare da cewa. "Yaran zamani ku dai kunfi yarda da kayayyakin ƙasashen turawa, sam kun Kasa tsayuwa ku inganta mana na ƙasarmu yadda zamuci gaba muma, yanzu jihar gombe wanne irin kayane babu?. Duk fa arewacin ƙasarnan babu jihar da ta kai jihar Gombawa yawan kafintoci da ci gaban kafintoci. Babu irin samfurin kayan ƙasar waje da basa iya sarrafawa,yanzu konan cikin Sahaja Ventures kuka shiga ae akwai kaya masu kyau da inganci, wasu ma harsun ɗarawa kayan waje kyau." Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa. "Ahmad wannan zirga-zirga duk na menene?." Aminu ne ya ɗan kalleshi tare da cewa. "Ai driver ne shiɗin shiyasa yana nan kamar farin wata yana ko ina." Cikin mamaki Bappa Ali yace. "Driver kuwa?." Murmushi Malam Adam yayi tare da cewa. "Eh shi pilot ne driver' n jirgin sama. Yana aiki da kamfanin Azman Air Land." kai bappa Ali ya jinjina jin suna kamfanin ma aikatar Ahmad ɗin. Nan dai suka gama tsara komai da shirya komai na bikin yadda ya dace, an dai bar batun ɗaurin aure nan da wata ɗaya mai zuwa. Wai to ina Zaleeha ne, mun dai san Mama da Zahira kan suna Doho, Ziyada da Zakariyya kuma mun san su dama gidan Hajja inna suke da zama tsohuwa mai boris. A gidan su Saifuddeen kuwa su Adda Rahma suna dawowa, duk suka zauna parlour'n Ummi suna hirar mutunci da karramawar mutanen, Hajia Rabi ce ta kalli Ummi cikin nitsuwa tace. "Na ɗan samu nitsuwa da naga gidansu yarinyar gidan mutunci ne, duk mutanen gidan sunada mutunci." Kai Ummi ta jinjina tare da cewa. "Masha Allah." Aunty kubra ce tace, "A gsky ba laifi sunada dattaku, sai godiya suketayi kamar kyauta muka basu kayan." Hayatuddeen ne yayi dariya tare da cewa. "Nan kuma wayo zamuyi musuba mu ɗauke musu ƴarsu kayan kuma gidanmu zai dawo da dalelliyar amaryar Hamma na." Dariya sukayi baki ɗaya, Imran ne ya ɗan sosa ƙeya tare da cewa. "Aunty Kubra zamu tafi fa." cikin dariya tace. "Yo to ku tafi mana." Sulaiman ne ya ɗan zaro ido tare da cewa. "To kuɗin namufa da aka bamu?." da sauri suka juyo suka kalli Isma'il da yayi dariyar ras Kamar ba kurma ba. Hajia Rabi ce tace. "Ohoho ni Rabi'atu wlh wata rana kuɗi zaisa Isma'il ɗina yayi magana, ji shewar da yake jin ance kuɗin nasu ne." Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa. "Yaseen kuwa Mom Isma'il in yaga kuɗi har harshenshi zakiga yana rawa." Dariya yayi tare da kaucewa dukan da Isma'il ya kai mishi, Ita kuwa Hajia Rabi kuɗin ta fidda cikin Jakarta irgasu tayi ganin dubu hamsin ne a rafar forko kuma duk girmansu ɗaya, shiyasa suka gane cewa dubu ɗari uku ne suka basu tukuici, wanda a al'adan gombawa in an kai kayan lefe anasa kuɗi a ƙasan turame, in dubu goma akasa to dangin amarya zasu ƙaro wasu dubu goman su ɗaura kan goman dake ƙasan turame sai su bawa wanda suka kawo kayan wannan nasune tukuicinsu kenan so su yasu zasu raba, in dubu biyar akasa to biyar ɗin dangin amarya zasu ƙara, In 20k nema to dole zasu ƙara in 30k ne ko 50k Ko 80k 100k nema dole su ninka, to su dama dubu ɗari suka saka a ƙasan turamen, su kuwa madadin su ƙara dubu ɗarin sai suka ƙara dubu ɗari biyu, shiyasa suka samu dubu ɗari uku. Rafan dubu hamsin Hajia Rabi ta miƙawa Hayatuddeen tare da cewa. "To gashi ku karɓi wannan." Da sauri suka amsa tare da ɗaukan tiren da Adda Rahama ta cika musu pepper chicken dasu drinks akai, tace kuci abinci kafin ku raba kuɗin. to sukace kana suka haura sama a parlour'n Hayatuddeen suka baje kolinsu, Imran ne ya ɗauki kuɗin ya irga 10k ya bawa Sulaiman kana ya bawa Isma'il ma 10k shima ya ɗauki 10k kana ya bawa Hayatuddeen 10k, 40k kenan, sai ya ɗago sauran 10k ɗin kuma yace. "To wannan 10k ɗin kuma na Zakariyya ne. kun san Zakari namu yaseen in mukaci kuɗin nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148