Skip to content

Chapter 92

Chapter 92

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

imani cewa Amina batasan da cewa Hammanshi na fahimtar maganar mutunba idan yana kallon bakin me maganar ba, tabbas da batayi wannan katoɓarar ba. Shikuwa Saifuddeen idanunsa ya mayar ya rufe yana mejin yanda heart ɗinsa ke beating, sam yarasa ma tunanin me zaiyi hakan yasa yanemi ƙaƙalowa kansa bacci. *** A nan Nigeria kuwa Zaliha jiki asaluɓe haka kuma zuciyarta ɗauke da mamakin ganin Abdussalam da iyayensa acikin gidansu ta tura hancin motar tata cikin gidan. Tana gama dai-dai-ta parking ta ɗauki ƴar jakanta me kyau tare da buɗe murfin motar ta fito. Kaitsaye ɓangaren Mamy Hajiyar Ya Ahmad ta nufa, da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, Mamy dake zaune akan kujera ta amsa mata sallaman nata fuska ɗauke da murmushi. "Mamy sannu da gida". tafaɗa tana me nufar inda makeken fridge ɗin dake cikin falon yake. "Yauwa Zaliha ya wajen aikin naku?". cewar Mamy data maida hankalinta ga tv. "Alhamdulillah". tabawa Mamy amsa tana me ƙoƙarin kafa bakinta ajikin goran ruwan data ɗauka acikin fridge, dawowa cikin falon tayi tare da kwantawa akan kujera kana ta lumshe gajiyayyun idanunta wandanda suke cike da zallar zazzafar soyayyan Saifuddeen, wanda kullum take k'ara narkar da zuciyarta. Zahira ce tashigo cikin falon daɗan sauri, ganin Zaliha kwance yasanya taɗan tsaya tare da cewa "Laaa Adda Zalee dama kina nan?". Harara Zaliha ta wurga mata tare dacewa. "Da bananan ai bazaki ganni ba!". dariya Zahira tayi tare da cewa. "Dama kina da baƙo a BQ yanajiran dawowarki". Idanu Zaliha ta ɗan zaro cike da mamaki tace. "Baƙo kuma wajena yazo?". Mamy dake jinsu ne tayi murmushi tare da cewa "Bak'ofa akace miki ba dodoba, kike wani zaro ido Abdussalam ne yazo". Jitayi gabanta ya faɗi don sai yanzune ma tatuno ganin da tayi musu shida iyayensa a lokacin da zata shigo cikin gidan, fuska ta kwaɓe tare da langwaɓar da kanta gefe, murya asanyaye tace. "Ayya Mamy mekuma yazoyi?". "Me kuwa zaizo yi idan ba abun da bakyaso ba, kullum muna miki faɗa akan kifitar da tsayayye guda ɗaya amma kinƙi, to dai Abdussalam kam yagaji da wainasa da kikeyi yaturo iyayensa sun nema masa izinin zuwa zance awajen mahaifinki, ko tantama banayi kuma nasan ya amince musu!" Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tsaya amaƙoshin Zaliha, take haushin Abdussalam ya cika ranta, meyasa zaiyi mata haka batare da ya tsaya yaji ta bakinta ba? ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba tare da komawa ta kwanta. "Tashi kije ko bakiji Zahira tace nemanki akeyi ba, Kije ki sameshi ku fuskanci juna, inafa gaya miki Zaleeha kada ki bari ki k'ure Malam kinfa sanshi kaifi d'aya ne zafa kiyi kuka a sanda babu mai lallashinki". Mamy tafaɗa cike da kulawa, cikin turo baki gaba Zaliha ta-tashi daga kwancen da take tare da ɗaukan hand bag ɗinta tafice, sashinsu ta nufa fuskarnan tata babu fara'a ko kaɗan, harta kusa kaiwa ɗakinta taji muryar mahaifiyarta inda take cewa. "Da kika dawo tun ɗazu kika tsaya shashancinki bakisan cewa kina da baƙo bane?". bakinta taƙara turowa gaba tare da cewa. "Ni agajiye nake yaje sai wani lokaci kawai". kallon bata da hankali Mahaifiyarta ta tayi mata tare da cewa "Zaki shirya kije ki samesa ne ko ko sai na ɓata miki rai yaro yazo yana son ganinki kice yaje sai wata rana shi bawan gidanku ne, ko kin mance shi d'an wanene?". ganin yanda mahaifiyarta ta ta haɗe fuska ne yasanya ta buɗe ɗakinta ta shige tana me guna-guni acikin ranta, kayan jikinta ta rage tare da faɗawa bathroom, haka tayi wanka ranta duk acushe, koda ta fito sama sama ta shafa lotion ajikinta, riga da sket na wani purpule ɗin material tasanya, sosai kayan suka amshi jikinta sukayi ɗas. kallon kanta tayi amadubi, tabbas ita kanta tasan cewa kyawunta ya zarce misali, sannan tanada diri irin wanda ke ɗaukan hankalin maza, yanda takeji aranta yasanya bata jin zama ta iyayin kwalliya akan fuskarta, saidai kuma abun da batasani ba shine ko babu kwalliya akan fuskarta tauraron kyawunta haskawa yake, farfumed ta fesa ajikinta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauki wani purpule ɗin mayafi tayafa ajikinta, normal flat shoe ta zura aƙafanta kana ta murɗa handle ɗin ƙofar tafice, BQ ta nufa inda tuni tasake sanja yanayin fuskarta. Sallama tayi can aƙasan maƙoshinta haka ta tura kofar katafaren falon tashiga. duk da cewa sautin sallaman nata baifito sosai ba amma yaji sautin acikin kunnuwansa, lumshe idanunsa yayi sakamakon wani daddaɗan ƙamshi daya kawowa hancinsa ziyara, ahankali ya amsa mata da "Wa'alaikissalam!" Cikin takunta me ɗauke da nutsuwa taƙaraso cikin falon tare da zama akan wata kujera dake nesa da wanda yake kai. Murmushi Abdussalam yayi tare da cewa "Barka da dawowa gimbiyar mata, kiyi haƙuri kindawo kuma na hanaki hutawa". ɗan satan kallon inda yake tayi tare da ɗauke kanta gefe, sanin cewa ba lallai tayi magana ba yasanyashi cigaba da cewa "Kiyi hakuri nima zazzafar soyayyarki ce take hanani hutawa, ita ke ingizani wurin kafa naci. Haƙiƙa yau ina cikin farinciki kasancewar nasamu izinin zuwa wajenki daga wajen Malam. Ina sonki Zaliha ina miki so me tsanani, tabbas kina da wata irin baiwa ta musamman wanda duk wani ɗa namiji idan yaganki dole zaiji wani abu dangane dake, burina bazai wuce naga na sameki amatsayin mata ta ba, dan Allah Zaliha ki amincemin ki duba girman soyayyar danake miki!". yaƙare maganar cikin yanayi na kwantar da murya. wani murmushi Zaliha tayi wanda ya sake bayyana asalin kyawunta, bakomai yasata murmushin ba kuwa face jin ta tsuniyar da Abdussalam keyi mata akan wai yana fatan tazamowarta mata agaresa, lumshe kyawawan idanunta wanda ke masifar jan hankalin maza tayi tare da jingina bayanta da jikin kujera, hoton kyakkyawar fuskarsa ne ke yawo acikin idanunta koda yaushe, wani irin azababben so da shauƙin ganinsa ne suka dirar mata alokaci guda, take yanayinta ya sauya wani irin sanyi taji na shiga jikinta, ƙwaƙwalwarta ne ta tuna no mata lokacin data kalli cikin idanunsa, tsikar jikinta ne taji yatashi yayinda taji zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ji take kamar tayi ta shelanta duniya tana sonshi tana kuma nemanshi da buƙatar ganinshi. Abdussalam kuwa ganin tayi shiru kamar ma bata cikin hayyacinta yasanyashi ƙiran sunanta murya asanyaye yace. "Zaliha!". Ƙiran sunanta dayayi shiyayi sanadiyar dawowarta cikin sense ɗinta, ahankali ta buɗe idanunta da suke cike da shauƙin ganinsa, sam bataso Abdussalam ya katse mata tunaninta ba, kasancewar ayanzu tunaninsa shiya zame mata abincin ruhinta, miƙewa tsaye tayi tare da duban Abdussalam daya ƙafeta da ido. "Zanshiga gida!". ta faɗa ataƙaice. Murmushi yayi tare da cewa. "Idan muna tare banaso kiyi nesa dani". Bakinta taɗan taɓe tare da cewa. "Saida safe". Bata tsaya jin wani abu daga bakinsa ba tasakai tafice daga cikin falon, shiru Abdussalam yayi tare da bin bayanta da ido, jin soyayyarta yake tana ratsa ko ina na jikinsa, jiki asanyaye haka ya ɗauki makullin motarsa shima ya fice daga cikin falon. Itakuwa Zaliha tana kaiwa part ɗinsu kai tsaye ɗakinta ta wuce, kwanciya tayi luf akan gado tare da hugging pillow, idan da ace za a fasa zuciyarta to tabbas za'atarar da tarin begensa acikinta, wani irin abu takeji dangane dashi na musamman, sake rungume pillow'n tayi tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148