Chapter 4
Chapter 4
yan ajinsu karatu sukeyi sosai babu kama hannun yaro kuma. Alhamdulillahi kwakwalensu na ja. Tuni Raihana ma ta fara zama yar budurwa hakama Raliyya Hayatuddeen ma tuni ya tafi primary 3. Bappa Ali kuwa har yau Allah bai bashi haihuwa ba, Kuma shike jan ragamar makarantar da mahaifinsu ya bari. Goggo Dada kuwa tun haihuwanta na fari bata kumayin koda b'ariba tuni d'an nata Ahmad ya girma domin sa'an Saifuddeen ne shi. Alhamdulillahi su Saifudddeen sun kammala makarantar especial education lfy, har anyi bikin yaye d'aliban kana yanzu sunata shirin zana jamb dan samun gurbi a jamir'ar G.S.U wanda shine burinsu. Ana cikin haka Allah ya yiwa mijin Rahma rasuwa, dole ta dawo gida da yan yaranta Faruq da Adam daga nan nauyin kula dasu ya dawo kan Nuruddeen, abu ya had'e mishi gashi yanzu jikin Abba ya tsananta tsawon shekara guda kenan da abun ya tashi bai kuma sakeshi ba koda na dare biyu ne, duk ya rame ya lalace sai tsawonshi daya k'ara fitowa kana farinshi ya k'ara baiyyana hancin nan nashi har kan baki, gashi yanzu baifi gonaki shida bane ya rage musu, sai filayen cikin gari, inda sunada fili a biyu a Sirinkiyo da katafila duk sunada fili anan, sai kuma nan gidansu na gado da yake Dugge nan kusa da Fadan Dukku d'in . dole ciwon Abba yasa aka saida gonaki biyu ya rage musu hud'u, inda suka zuba kud'in wurin nema mishi mgnin. Sukaje bauchi wurin wani Mlmi irin masu Islamic kemis innan, nan duk kudaden suka k'are dan magungunansu da tsada, Alhamdulillahi jikin ya d'anyi sauk'i sosai. Sai kuma wani mak'ok'o ya fito mishi nanfa, suka fara jinyar asibiti kuma, amman ina abu sai gaba-gaba yakeyi, ta kai matakin da ko tsawonshi baya iya mik'ewa. Bappa Ali yace a kuma saida sauran gonakin amman Abba ya hana acewarshi kada su Kuma saida komai a kanshi dan yasan wannan ciwon ba barinshi zaiba kar yazo ya mutu bai barwa yaranshi komaiba, sun so suk'i bin shawararshi amman sai yace bai yafe musuba in suka kuma saida wata kaddararshi dan jinyarshi, su bari in ya rasu suyi duk yadda sukaga dama da kaddarorin da suka rage dole suka hak'ura, badon sun soba, haka yasa Nuruddeen zagewa da yin acaba don samo kud'in da za'a nema mishi mgni, wani lokacin sai k'arfe goma na dare yake baro gombe ya nufi Dukku. Saifuddeen kuwa shike kula da Abban tunda yana gida, bappa Ali ma yanzu bai fiye zamaba yana tafiye-tafiye dan yana bin kasuwannin k'auye yana aune-aunen kayan abinci. Still kuma dai yana kula da d'aliban sun, dan da safe baya tafiya sai ya karantar dasu na safe, kana in ya dawo da deddere bayan sallan isha za a hura wuta a tsakiyar tsangayar daliban su zazzauna kan itatuwan dake zagaye da wutan ayi ta karatu, sai k'arfe tara da rabi ake tashi, Yau asabar da sanyin safiya Nuruddeen ya fara shirin tafiya gombe, sai ya kuma fasa ya dawo ya zauna tsakiyar k'annenshi Raihana nayiwa su Faruq wonka dan Faruq ya fara zuwa makaranta, Abba kuwa yana zaune jingine da pillow, kana Saifuddeen na gefenshi yana sa mishi sugar a cikin kunun koko da Ummi ta dama musu, kana Rahma kuma tana toya musu kosan da zasu had'a da kunun suyi karin kumallo dashi, Raliyya kuwa wonke-wonke takeyi. gefen Ummin shi ya zauna tare da tonkoshe kai irin yadda Saifuddeen keyi sannan yace. "Na fasa tafiya yanzu yau sai azahar zan tafi." cikin disashewar murya Abba yace. "Meyasa?." ajiyan zuciya yaja tare mik'e k'afafunshi kana ya yayi murmushi tare da cewa. "Yau dai abincin Ummina zan ci." Rahma ce ta juyo ta kallesu tare da cewa. "Kuma dama d'an malele zamuyi yau Ya Seyo nasan kai kana son d'an malele, ba irin Saifu ba da yake cewa muma mmki muke bashi wai shi baiga abin ciba a dan malele." Hayatuddeen ne ya tura baki tare da cewa. "Gskyan shi ai, dan malele fa abincin matane." murmushi Ummin tayi tare cewa. "Kada ku damu kowa zaici abinda yakeso, nasan Autana da Hamma Saifunshi da Abbanku suna son d'anwake, ni kuwa da sauran muna son d'an malale shiyasa nace ayi duka biyu kowa yaci abinda yake so." murmushi sukayi baki d'aya kana sukaci gaba da hira, sannan Rahma ta gama tuya ta kawo musu tsakiyarsu nan suka zauna sunaci suna hira, saidai Ummi da Saifuddeen sam basuci wani mai yawa ba, shi kuwa Nuruddeen sosai yaci kosan nan yana korawa da koko. cikin kula Nuruddeen ya kalli Ummi tare da cewa. "Lfy kuwa Ummi naga kinyi shiru da yawa, ko kokon baki shaba, gashi kin san Saifu bazai ciba muddin yaga kina cikin damuwa." murmushi tayi sai kuma ga hawaye, da sauri Saifuddeen ya zuba mata idanu lokaci d'aya idanunshi sukayi jazir. shi kuwa Nuruddeen kasa had'iye abincin bakinshi yayi dan ji yayi ya mishi d'aci ranshi na suya, tuni shima hawaye suka ciko mishi ido, Rahma kuwa mik'ewa tayi ta shiga d'akinsu haka nan tausayin Umminsu da kanta da Saifuddeen yasata kuka tuno mijinta daya tafi ya barta, kana ga uba ba lfy. Kuka ne sosai ya rufeta tuno sam Umminsu tunda tayi aure take cikin k'uncin rayuwa. Shi kuwa Nuruddeen cikin k'arfin zuciya ya sharce hawayenshi, kana ya d'ago kanshi ya kalli Ummi da ta zubawa Abba ido tana kuka, cikin raunin murya yace. "Ummi". kai ta juyo a hankali kana ta zuba mishi ido, shi kuwa murmushi yayi still hawaye na zuba, cikin k'arfin guiwa da yak'ini yace. "Ummi ki kalleni, ki cewa k'annena su kalleni." sai ya kuma share hawayenshi kana ya kalli Saifudden daya zuba mishi ido ko k'ibtawa bayayi sannan yaci gaba da cewa. "Ummi na kada kiyi kuka, ki meda idanunki da buk'atun rayuwarki dana k'annena dana yaran k'anwata a kaina, dai zan iya kula daku, Ummi na kada kiyi kuka, kin ganniko ni d'innan nine farin cikinku, kin manta wanne suna kuka bani inkiya SEYO fa kike cemin to kuyi imani da Allah ku yarda da kaddara mai kyau ko akasinta, ku kalleni ni zan jure d'awainiya daku iya rai da mutuwa." sai ya kuma kamo hannun Ummi da Abban su cikin rawan murya yace. "In sha Allahu Ummi na ni d'innan sai na kaiku makka da madina birnin ma'aiki, insha Allah ni d'innan zan share hawayenku, Ummi in dai fa ina raye to insha Allah bazakuyi kukaba." sai ya kuma kalli Saifuddeen kana yace. "Gamu Allah ya baku zaratan yara kyawawa muminai salihan bayin Allah, ko ni na gaza zama gatanku in sha Allah Saifuddeen zai zama Garkuwar ku kuma zai saku farin ciki, zai kula daku ya ruggumi buk'atunku." Raihana ce ta sharte hawayeta tare da cewa. "Dan Allah ya Seyo kubar kukannan haka kallifa yadda kukasa Abba da Hamma Saifu kuka, please Ummi ki rink'a bamu k'arfin guiwa kada ki bari hawayenki suna zubowa." jin haka yasa Ummi share hawayenta kana tasa hannu ta share na Saifuddeen da Seyo, shiko Saifuddeen ya share na Abbansu daya gaza cewa komai dan ya lura jikinsu ne ya fara basu zai mutu ya barsu da maraici. Daga nan sai kuma suka d'an sake, haka dai sukayi ta hira har Rahma ta gama musu abinci, kowa yaci abinda ransa keso. Bayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148