Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

sun tallatama mana ne dan suna mana sha'awar ci gaba, sun bamu sirrin company cewa nanda wata biyar magi zaiyi tsadan da bai tab'a yiba, sun k'ara da ce mana mu fito da kud'ad'enmu mu sari maggin mu ajiye sun sanar damu cikin wata biyar zuwa bakwai company zai k'ara tsadan magi sun bamu tabbacin in sha Allah babu batun fad'uwa sai dai cin riba, in dai bamuci riba ba toko bazamuyi asaraba." sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon kekyawan fuskar Saifuddeen kana cikin tausayawa yace. "Tabbas nasan akwai riba dan yar daddunmu ne suka sanar mana dan son ci gaban junanmu, to matsalar uku daga cikinmu duk last week mukayi sari bamu da kud'i a k'asa asalima kaga sai yau kayan ya isomu, sannan masu zuwa sari su zo su sara wanda yawanci bayan wata d'aya suke dawo da kud'in. To da fari company wata biyu suka bada k'a'idar rufe sarin dan kamar bonanza ne zasuyi mana to sai kuma suka maida k'a'idar wata d'aya. to shi kanshi uban gidanmu Alhaji Sani wata uku da suka gabata ne ya gama ginin sabon gidanshi inda ya k'aura ya koma yanzu, to bashi da kud'i sosai a k'asa da zai ranta mana." ganin yayi shirune yasa Saifuddeen gyara zamanshi tare rubuta mishi. "To magin kuma kamar na k'asa da nawa zasu bada sarin?." Numfashi Alhaji Kabiru ya furzar tare da cewa. "To ai anan gizo ke sak'a domin sun san in sukace kad'an-kad'anne da yawa zasu iya sara, so sai suka d'an saka hikimar da suma zasu samu wani abu, sun bada tabbacin cewa mafi k'arancin sarin da zasu bada shine na 2 million, tofa shisa duk jikinmu yayi sanyi da abun." cikin d'imuwa Saifuddeen ya maimaita 2 million to shi tunda aka haifeshi yazo duniya baima tab'a ganin dubu dari biyar cikakku bama, kai ya rink'a jujjuyawa da a zatonshi ko irin d'an sarin 100k ne zuwa 200k nan zai iya zaton zai samesu in ya fasa asusunshi, tab'ashi da Alhaji Kabiru yayine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi kai ya rink'a jujjuyawa jin tambayar da Alhaji Kabirun ya masa cewa. "Kanada kud'in sari ne?." ganin yanata jujjuya mishi kaine yace. "Shiyasa nace abin da wuya ni du'du du yanzu dubu d'ari biyar nake dashi, in samu wanda zamu had'a hannu muyi sarinma abin ya gagara ya rigada yanzu cinikaiya ta d'anyi k'asa, amman kaje kayi shawara in kanada yadda zaka samu 500k d'in kamar nawa sai mu had'a in sha Allah zan samu su Alhaji Sani sai mu had'a da wasu in an samu." Cikin rauni da sanyi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai tare rubuta mishi. "Kud'in sunfi k'arfina bani da hanyarsu ko dalilinsu. Ngd matuk'a da bani kulawa da shawara naji dad'in yadda kamin kekyawar fahimta." Cikin kula ya kalleshi ganin yana shirin aza kwalin omonshi a kai alamun zai tafi murya a tausashe yace. "Ba komai Saifuddeen wlh ni ina jinka tamkar d'ana na cikina, na kuma yarda da amincinka, muyi ta Addu'a Allah ya bamu sa'a." A saman labb'anshi ya amsa da Amin Amin kana ya juya ya fita shagon. Daga nan yaci gaba da tallanci yanayi cikin nasara, randa yayi kwana biyu da zuwa wurin Alhaji Kabiru, da dare ya sake yin wani mafarki ma kamacin wanda yayi ranan, sosai abin ya d'aure mishi kai al'wala yayi sannan yayi ta karatun Qur'an washe gari, ana fitowa sallan asuba yaga Sabir k'anin Saminu yazo gaban Bappa Ali inda ya shaida mishi wai babanshine ya aikeshi kan yazo ya gaya mishi yana son ganinshi anjima shida Saifuddeen. jin haka bai wani damu Bappa Ali ba dan akwai alak'ar zumunci a tsaka ninsu in abi ya shafi na addini to ana nemanshi. Sai dai da yaji yace shida Saifuddeen shiyasa ya hana Saifuddeen tafiya cikin gombe yace Salisu yaje kawai shi Saifuddeen yau bazai jeba sai gobe in Allah ya kaimu da haka Salisu ya tafi. K'arfe tare dai-dai na safe Saifudddeen da Bappa Ali suka isa fadan masarautan Dukku. Bayan anyi musu iso suka isa har cikin masauk'in bak'i. Cikin mutuntaka suka gaisa da mai martaba da Wazirinshi da sauran wad'anda ke wurin, daga bisani Sarkin ya gyara zama tareda murza rawanin kanshi cikin salon mgnar sarakuna yace. Malam Ali kunga na aika a kira minku da sanyin safi ko?." kai Bappa Alin ya gyad'a tare da cewa. "Eh shine ma dalilin zuwanmu domin amsa kiranka." kai ya jinjina cikin salon adalcin sarauta yaci gaba da cewa. "To batun dai filin nan naku na Dugge ne da filin yayanka na nan bakin kasuwa shine dai dililin kiran naku yau ma, in baka mantaba kwanaki nayi maka mgnar cewar akwai masu son filin walau saya walau haya shi filinku na Dugge d'in sunce su ko haya ne a basu, to da nayima mgna kace min baka da hurumin saida filin domin filin nakune kai da d'an uwanka ne Bello mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa yanzu filin na magada ne yaran shi kenan da kai. To kuma company layin waya na mtn suna tayi mana zirya a gari sabida sun tabbatar mana da cewa, sun samu igiyoyin services a cikin filin naku koda na sanar musu bani da hurumin saida musu filin sabida na magadane to sun kuma dawowa kan cewa ko hayane a basu filin duk shekara zasu rink'a biya, nanma na kuma jaddada musu bani da hurimin filin, to sunci gaba da duddubawa cikin garin dukku amman Allah baisa sun samu wani wurinba da zasu samu su kafa na'u'rarsu ta services, to shiyasa suka kuma dawowa gareni da neman al'farman a basu hayan filin zasu rink'a biyan kud'i mai tsoko cikin ko wanne shekara, to ganin sun dameni nace bari in kuma kiranka kaida Saifuddeen d'in in sanar muku sannan kuyi shawara da juna." ya k'arishe mgnar cikin son jin ta bakinsu, shi kuwa Saifuddeen numfashi ya d'an fesar a hankali kana ya zubawa bappa Ali idanu cikin alamun nuna mishi duk hukuncin da ya yanke yayi dai-dai. gane hakan yasa bappa Ali yin mgna cikin mutuntaka yace. "To ba matsala in sha Allah zamuje gida muyi shawara da mahaifiyarsu Saifuddeen d'in da kuma yayarshi Rahma da k'anneneshi dan jin ta bakinsu tunda suma sunada hak'k'i a ciki." cikin mutuntaka yace. "To ba laifi, sai naji shawarar da kuka yanke, amman nace musu su dawo jibi suji yadda mukayi daku." Sai ya kuma yi gyaran murya tare da cewa. "Yauwa to sai batun filinku na nan bakin kasuwa, wanda kace min filin Bello ne mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa baka da ko sulai d'aya a kud'in sayan filin, to kuma kasan tun last year hukumar bankin nan na GT bank sukayi ta zirya kan suna son sayan filin dan suna son su bud'a cibiyar bankin nasu a nan dukku, to rashin amincewarka yasa suka hak'ura duk da sunyi ta nacin filin, a cewarsu wai rigima kuke musu, to kaga bayan nan kuma A. A Rano ya buk'aci sayan filin dan bud'e gidan mai nanma kak'i bada fuska, dole ya hak'ura yaje ya nema a mashigan hari." sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon yadda suke zaune cikin kamala da cikar haiba, kanshi ya juya ga wazirinshi da Garkuwanshi kana sai

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148