Chapter 41
Chapter 41
inda tuni masu kud'i keta sara suna boyewa da nufin sai yayi tsada su fitar to wannan dalilin yasa Bappa Ali fara sara da kekyawar niya dan taimakawa masu k'aramin k'arfi yayi aniyar zai canza salon wannan kasuwancin da ya sara ya ajiye in yayi tsada shi kuma ya fitar ya fara saidawa a farashi mai sauk'i. to nanfa ya k'ara k'aimin bin kasuwannin k'auyuka yana sarar buhuhhunan su. Masara, Dawa, Gero, Maiwa, Shinkafa, Rid'i, kalwa, Wake, Gyad'a, da dai sauran kayayyakin abinci, cikin wata biyu duk ya gama sarin inda ya cika tsoffin d'akunan iyayensu duka biyu da buhunan kayan abincinshi. Tuni Magginsu Saifuddeen kuma ya isa har an shirgesu a babban shagon da Saifuddeen d'in ya kama haya inda aka cikashi mak'il da katon d'in MAGGI mak'il kana aka ja shagon aka rufe, yayinnda shima burinshi irin na Bappanshi ne. Ya kuma ci gaba da sana'o'insa da ya saba, yana kula da ahlinshi da ahlin Baba Bello, yana kuma zura ribar shi a wani sabon asusunshi d'aya saya dan wancan asusun tuni ya cika a cewarsa sai ya cika asusu uku kafin ya bud'esu duka. Bayan wata bakwai da saran Maggin kenan Rayuwa taci gaba da gudana yau dad'i gobe akasin haka abu da dama ya faru. Ana cikin haka rana tsaka Maggin da aka sani a hud'u goma sai gashi yayi gauron zabbi ya koma biyar ashirin kusan ninkin ba ninkin kenan, yayinda yan kasuwa masu harkan magging da sun samu sun sara suketa farin ciki anata hidimar kasuwa anata hidima. kusan tsawon mako uku kenan da farashin maggin yayi sama, wanda yayi dai-dai da cikin tsakiyar damuna ne sama ruwa k'asa ruwa, kayan abinci yayi tsada, tuni talaka ya fara shiga hau'ula'in rayuwa, bappa Ali da Saifuddeen kuwa tuni sun fara shirye-shiryen bud'a kasuwancin nasu Yau jumma, kuma tun bayan sallan la'asar aketa zuga ruwa kamar da bakin gwarya, dole cikin ruwan Salisu da Saifuddeen suka kamo hanyar dukku, daga gombe har cikin Dukku ruwane yake dukansu tamkar zai jasu ya tafi dasu, k'arfe shida dai-dai suka isa cikin dukkun sauri-sauri gudu-gudu Saifuddeen ya shiga cikin gida lokacin da Salisu ya sauk'eshi dan har lokacin ana d'an yayyafi irin na alamun ruwan ya d'auke sai yaf-yaf ruwan keyi. Yana shiga kai tsaye d'akin Umminshi ya nufa dan wannan al'adarshi ce muddin ya dawo ko ruwa ko iska ko dare ko rana sai ya fara shiga inda take ya ganta ta ganshi kafin ya wuce d'akinshi, yayinda ita kuwa Ummi duk nisan dare bata tab'a iya yin bacci har sai taga dawowanshi, duk ruwa kuma bata rumtsawa sai taga ya dawo. Yana isa bakin k'ofarta yasa hannu ya bud'e labule, murmushi yayi ganinta zaune ta zubawa k'ofar idanu yayinda Hayatuddeen ke konce yayi pillow da cinyarta Rahma kuwa na gefenta tana gugan kayan data wonke, Raihana kuwa nayiwa Ummi kitso, ajiyan zuciya Ummi tayi tare yin murmushi ganin gudan jininta, cikin tausayawa Raihana tace. "Sannu da hanya Hamma Saifuddeen." kai ya jinjina mata alamun yauwa. Rahma kuwa ajiye anyone d'in tayi tare da cewa. "Saifuddeen jeka canza kaya kalli yadda ka jik'e jilik sanyi zai kamaka illah fa." cikin body language yace da ita. "To." sai ya kuma yi musu alamun ina Raliya dasu Faruq." gane abinda yake nufine yasa Ummi ce mishi. "Suna wurin Aunty Nina." kai ya jinjina dan yasan dama su Faruq suna son zuwa wurin Aunty Ninan wacce tuni ta haifi d'anta wanda akayiwa Abba mai suna shiyasa su Rahma ke kiranshi da Abban tuni yaron ya girma har yana rarrafe. Juyawa yayi ya nufi d'akinshi daga bakin k'ofa ya mik'a hannunshi ya jawo towel inshi dake shanye a kan k'ofanshi, botiki ya d'auka ya cikashi da ruwa kana ya d'auki kondon soson wonkenshi, ban d'akinshi ya juya ya nufa dan jin ruwan ya d'auke kit. Wonka yayi fes sannan ya d'aura towel d'in ya fito, buta ya d'auka yayi al'wala sannan ya shiga d'akinshi mai ya dauka kana ya zauna bakin katifarshi murze jikinshi yayi ciki da woje sannan ya mik'e tsaye ya zaro tattausan boxer inshi fari k'al ya fesheshi da turare sannan ya saka, yana gama gyara zaman boxer d'in a k'ugunshi ya konce towel d'in ya d'anyi taku biyu zuwa uku sannan ya isa bakin k'ofar wore towel d'in yayi ya shanshi kan k'ofar, sannan ya juya ya isa bakin 'yar durowar tashi ya zaro farin vest fara kal ya fesa mata turare yasa sannan ya kuma zaro bak'ar jallabiya ya zurata a jikinshi, sai ya kuma feffesa turaren, sannan ya matso gaban madubin shin hannu yasa ya gyara suman kanshi da yake konce lib sai shek'i yakeyi wayarshi ya zura a al'jihu sannan yasa takalmanshi dake bakin k'ofa ya fita. A tsakar gida ya samu su Ummi dasu Raihana da Hayatuddeen suna al'wala, kitchen ya lek'a ganin Rahma na kwasar abinci, ganinshi a bakin k'ofa yasa tayi murmushi tare da cewa. "Yauwa je kayi salla ana idarwa ka dawo yau miyarka nayi tunda naga hadari nasan zaka dawo da yunwa." murmushi yayi tare da mata alamun tayi sauri ta gama lokacin salla yayi, sai ya kuma kalli fuskarta ganin alamun saida tayi al'wala kafin tazo ta fara kwasan tuwon shiyasa ya juya , ya kamo hannun Hayatuddeen da Faruq da yanzu ya shigo suka nufi masallaci. Koda aka idar da salla, basu dawo gidaba nan ya zauna da Hayayuddeen da Faruq saida akayi sallan isha sannan suka fito. a bakin masallacin Saifuddeen ya kamo hannun Warisu sai ya kuma yafito Salisu tare da musu alamun su zo suci abinci, kasan cewar yanzu su ukune rak suka rage a dukkun dan Ahmad, Samuni, Mudassir, duk suna cikin gombe, Cikin yamutsa fuska Warisu yace. "Tab aini bani cin abinci da dare dan wlh kun sani bani son k'iba, gwara kai Saifuddeen jikinka ba irin nau bane." Salisu ne ya d'an harareshi tare da cewa. "Kuma in sha Allah wata rana sai kayi k'iba." sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen tare da cewa. "Ni kam a koshe nake muna dawowa na samu iya shatu tana kwasar tuwo tayi wannan hegiyar koriyar miyar nan tata kad'a kwarya yunwace ta sani cinta dole." dariyar mugunta Warisu ya mishi tare da cewa. "Hege ka dai biyewa wannan tsohuwar yaseen sai ta toshe maka kwanyarka da koriyar miyar nan ka zama huhulahu." yana fad'in haka ya juya da sassarfa ya gudu ganin Salisu zai kai mishi duka, shi kuwa Salisu hamma yayi tare da cewa. "Kaga mai jajayen kunnuwa ni zanje inyi bacci saida safe." daga nan sukayi saida safe, shi kuwa yasa Hayatuddeen da Faruq a gaba suka shiga cikin gida yayinda Bappa Ali ke binsu a baya. Suna shiga tsakiyar gidan ana dawo da wutar nepa, kai tsaye d'akin Ummi suka shiga suna shiga ya mik'awa Raihana woyarshi tare da mata alamun taje ta sa mishi caji a d'akinshi, da sauri ta karb'i wayar kana taje ta jona wayar sannan ta dawo. tana shiga kuma Rahma ta kalleta tare da cewa. "Je kitchen ki kawo musu abincinsu." to tace tare da juyawa ta nufi kitchen d'in, Ummi kuwa gyara zamanta tayi tare gyara sallayan da take zaune a kai sannan tayiwa Saifuddeen d'in alamun yazo ya zauna, kai ya gyad'a mata kana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148