Chapter 45
Chapter 45
ya fara bin kasuwannin k'auyuka yana sari babu kama hannun yaro, saida ya cika d'akunan iyayensu mak'il , sannan ya fara sara yana sawa Warisu na kaisu kasuwa cikin shagonsu tuni shago ya cika mak'il, masu sari sukayo musu caa ko yaushe kazo bakin shagon zaka samu dafifin mutane mata da maza manya da yara, ganin haka yasa Saifuddeen fasa asusunshi na wata hud'un ya fito da kudad'en suka sari buhunan al'kama da acca suka had'a a ciki. Nan fa kasuwa ta d'auka sosai da batun shagon Butu da yawa suna son sanin asalin mai shagon kuma sun gaza ganewa, dan wasu kance ai shima wannan shagon butun reshen shagunan Ba miskila ne da yawa kuma suna yarda da haka ganin babban yaron shagon ba miskilan a shagon butun Bello kenan, wasu kuma na cewa shagon Bappa Ali ne, wasu ko na cewa na Warisu ne, sam dai mutane basu gane sahihancin zancenba sunata kame-kame dai, Saifuddeen kuwa time to time yake lek'a shagon. Salisu kuwa sosai yake jin dad'in sabuwar machine d'in da Saifuddeen ya saya mishi inda yaketa karatun shi a F, C, E Gombe. Su Ahmad da Mudassir kuwa Karatu yayi nisa hakama Salisu, tuni Saminu kuwa sune masu gama wannan shekaran. Yayinda Saifuddeen kuwa sune 'yan level 100. Bayan shekara d'aya, kasuwa taci gaba da gudana komai yana tafiya dai-dai da tsari na taimakon talakawa da marasa k'arfi. Kullum jarinsu habaka yakeyi da d'an riban da suke bi da kuma kud'in hayansu, inda kayan masarufi yake mallakin jarin Saifuddeen ne halak d'inshi ba surkin kud'in gadonsu. Yau kusan wata d'aya kenan Saifuddeen da Bappa Ali sunata kan harhad'a cinikinsu na tsawon shekarar suna ware ribar su da hauhawar jarinsu. Koda suka gama had'e komai sai suka fara ware hak'insu Bello da Warisu sunka biyasu biya mai daraja a matsayinsu na masu kula da kasuwancin, daga nan kuma suka ware adadin zakkar da zasu fidda na shekarar bayan sun gama ware zakkar tasu, sun bawa wad'anda shariya ta misalta da a basu sai kuma suka fara shirye-shiryen sari tako wanne sashi inda Bappa Ali zai sarar musu kayayyakin abinci a kasuwannin k'auyuka kamar yadda suka saba, shiko Saifuddeen zai yi musu sarin kayan masarufi wanda wasu direct daga company yake musu sarin shiyasa suke samun damar sakin farashinsu da rahusa, dole zuwa yanxu sunfi k'arfin shago d'aya hakan yasa suka nemi k'arin hayan wani k'aton shagon dake kusa da nasu, ba b'ata lokaci aka basu da yake na Alhaji Kabiru ne, cikin kwana uku aka had'a shagunan sannan aka barsu da k'ofofi biyu. Ya Adnan kuwa tuni ya isar da batun soyayyarshi da Adda Rahma ga manya tuni mgna ta kankama dan iyayensu Adnan sun san nagartar Rahma tunda a gabansu ta girma shiyasa basuyi wata rigimaba, tuni antsaida ranar aurensu bayan sallan layya da mak'o d'aya. Saminu kuwa ya gama karatunshi har ya samu damar tafiya bautan k'asa mgnar sosayyarshi da Raihana kuma tanata kankama har iyaye sun shiga, an bari a kan cewa sai ya gama bautan k'asanshi ya fara aiki sannan ayi musu auren. Mudassir da Ahmad da Ishaq ma duk sun kusa gamawa. Hayatuddeen kuwa shima yana shekararshi ta k'arshe a primary school, Faruq kuwa yana primary 3 Adam na primary 2, Raliyya kuma tana SS 1. Abba yaron Bappa Ali shima ya girma har an yayeshi. Rayuwa dai taci gaba da gudana cikin nasara da ci gaba. Anyi bikin Ya Adnan da Rahma lfy an watse lfy, ta tare a gidanshi dake cikin Gombe wanda yake cikin jerin gida jan ma'akatan lfy na Medical Center Gombe, wannan had'i yayi matuk'ar yiwa Ahmad da Mudassir dad'i dan dama a gidan Ya Adnan d'in suke sukewa kansu girki a cewarsu yanzu sun huta sun samu mai musu girki. Bayan bikin da mako ukune Ya Adnan yaje har dukku da batun yana son a basu Faruq da Adam a cewarsa zai rik'esu, to Ummi dai tak'i amincewa ganin ya tasa gabata da magiya ne yasata ce mishi Saifuddeen ne ya hana ba itaba kuma shi yana can gomben, jin haka yasa Ya Adnan tura mishi text cewar, yana son ganinshi gobe, yana ganin text d'in ya maida mishi amsa da to Allah ya kaimu. daga nan Adnan ya sallami Ummi ya tafi gidansu a nan ya wuni sai da yamma ya koma. Washe gari da safe Salisu da Saifuddeen ko breakfast basu tsaya yiba suka wuce cikin gombe, kasan cewar basu da lectures da wuri sai zuwa k'arfe biyu so kai tsaye gidan ya Adnan suka nufa, a harabar gidan Salisu yayi parking, sannan suka nufi bakin mashigar ainihin cikin gidan, a bakin k'ofa suka tsaya door bell suka d'an danna, jim kad'an aka bud'e k'ofar ganin Ahmad ya bud'e musu k'ofar ne yasa su yin murmushi shima murmushin yayi tare da bawa Salisu hannu tafawa sukayi cikin salon gaisuwa ta abokai da suka shak'u da juna, sai ya kuma juyo ya d'aga hannu alamun zai tafa hannu da Saifuddeen da k'arfi irin yadda yayi da Salisu, shi kuwa Saifuddeen ganin haka yayi saurin janye hannunshi tare da rab'awa gefenshi ya wuce yayi cikin parlour, cikin dariyar shek'iyanci Ahmad ya kalli Salisu da shima dariyar yakeyi, sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen da tuni ya isa tsakar parlour suna ruggume da juna shida Mudassir, dariya ya kumayi tare da cewa. "Hege mai d'an karen son jiki da tsoron wahala." cikin dariya Salisu yace. "Yaseen gskyanshi nima d'in ai bani kuma yarda ka kima min wannan hannun naka, kalli yadda hannuna yayi jazir hege mai suffar samudawa." duka ya kaiwa Salisu, da sauri ya kauce tare da cewa. "Wayyo Ya Adnan kaga Ahmad ko." da sauri Rahma ta yunk'ura zata tashi ta fita jiyo muryar Salisu tasan sarai da Saifuddeen suka zo. Shi kuwa Ya Adnan da sauri ya jawota jikinshi tare da cewa. "Ina zakije?." fuska ta d'an marairaice tare da cewa. "Parlour zanje kaji su Saifuddeen sun zo." ido ya d'an kashe mata tare da cewa. "Barsu suyi ta sabgoginsu muma muyi namu in mun gama ma fita." cikin sanyi tace. "Allah ko nayi missing Saifuddeen tunda akayi bikin nanfa bai zoba." mik'ewa yayi tare da kamota ya tsayar da ita sannan yace. "To muje muyi wonka." a dole ta bishi suka shiga bathroom. Su Ahmad kuwa a falo hira sukayi tayi na yaushe gamo, daga nan suka shiga kitchen suda kansu suka fara kiciniyar had'a breakfast nasu. to Ahmad da Mudassir su sun iya sun saba, Salisu da Saifuddeen kuwa basu iyaba, shiyasa suka kame suka zauna gefe, Ahmad na fire dankali shi kuwa Mudassir yana kiciniyar tafasa musu ruwan tea. Bayan kamar 35 minutes Rahma da Adnan suka fito a tare a parlour ta tsaya tana kasa kunne dan jiyo ta inda hayaniyarsu take, jinsu a kitchen ne yasa tayi sauri ta nufi kitchen d'in tana shiga duk suka juyo murmushi tayi musu ganin duk suna murmushi, sai kuma Saifuddeen yayi saurin tasowa ya iso gabanta murmushi ya kuma yi tare da mata alamun, "Iye-iye kinyi kyau fa." kunnenshi ta d'an rik'e tare da d'an matsewa da d'an k'arfi, d'an tsalle yayi tare da yarfa hannu, Ahmad kuwa sai tsalle yakeyi yana dariya tare da cewa. "Yauwa Adda Rahma matse da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148