Chapter 58
Chapter 58
rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa. "Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?." ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa. "Please officer ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in." da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi, a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace. "Sannunku lfy kuwa?." cikin saisaita fuska mai jan motar yace. "Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate." cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo, bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito, hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace. "Kayi mana sallama da Hayatuddeen." to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa. "Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?." ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi, "Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi." cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa. "Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?." cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala, jiki a mace yace. "Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi." cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau. A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen , cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace. "Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi, komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho." cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa. "Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma." ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne." dariya Raliya tayi tare da cewa.. "Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi." dariya sukayi baki d'aya dan shima yasan halinshi kenan. Raihana kuwa cikin dariya tace. "Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka." Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo, cikin raha tace. "Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya." dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras. Shi kuwa buzun nan wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17 years da yan watanni ba, Hayatuddeen, Raliyya matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23 years. Sai kuma Raihana da zata iya kai 26 year da d'anta Affan wanda bazai wuce shekara biyu ba. Cikin maida hankali kan buzun Ummi ta juyo cikin wani yanayi da takeji tun da yammacin yau d'in tace. "Baba ila ya akayi ne?." cikin sanyin jiki yace. "Wasune ke sallama da Hayatuddeen." mik'ewa Hayatuddeen yayi tare da cewa. "Muje wata k'il Zakariya ne." kai ya jujjuya mishi cikin sanyi yace. "A a bashi bane folisawa ne, sunce Saituddeeen ne ya samu d'an hatsari yana asibiti shine akeson yan uwanshi suje." wata iriyar zabura Ummi tayi kana ta rumtse idonta da azaban k'arfi sabida wani irin duhu da jirin da ya rufe mata ido a take, wani irin rawa jikinta ya fara har cikin hanjinta takeji suna hautsinewa zuciyarta kuwa tamkar zata faso k'irjinta ta fito fili sabida tsananin razana da kad'uwa lokaci d'aya wata zazzafar zufa ta yanko mata hakama Raliyya da Raihana shi kuwa Hayatuddeen gaba d'aya idanunshi ya zazzaro woje. kusan gaba d'aya a tare suka fito Ummi kam duk jikinta rawa yakeyi tamkar mazari. Hayatuddin ne yayi saurin isa garesu kana cikin tsananin kad'uwa da firgici yace. "Ina Hamma Saifuddee ina yake meya sameshi ku kaimu wurinshi waya bugeshi?." Raihana kuwa kuka takeyi mai cike da fargaba, ita kuwa Raliyya direbansu taketa rabkawa kira cikin firgici da d'aga murya take cewa. "Sule taho mu tafi wurin Hamma Saifuddee." a hamzarce Sule direban ya taso wanda yayi ta bai jima da dawowa ba dan shi yana ƙofan Baba bello lokacin da abin ya faru kuma yayi ta kiran Saifudddeen alamun yana nemanshi baiga amsaba, to sai yayo zaton ko yayi wani wurin ne shiyasa ya dawo shi ɗaya, Motarnda ke harabar gidan ya bud'e ya shiga tare da jawota zuwa gabansu, dai-dai lokacin kuma police officer d'in yake cewa Hayatuddeen . "Shiga mota muje yana asibitin Medical Center ne." firgici da kad'uwan Ummi ya tsananta jin k'irjinta takeyi yana buguwa da azaban k'arfi wata fargaba da razani ya rufeta, jiki na rawa ta shiga motar da Sule ya kowa gabanta sam ta kasa furta ko k'ala domin harshenta ya mata nauyi jiki na tsuma ta shiga motar, wonda tuni Raliyya da Raihana sun shiga shi kuwa Hayatuddeen cikin kaifin basira da zurfin tunani irin nasu na maza yace. "Ummi kuje, bari in d'auko kud'i zan taho a U.D. d'ina." jin haka yasa Sule jan motar yabi bayan motar police d'in kana suka fita suka nufi Medical Center Gombe. Shi kuwa Hayatuddeen , a guje ya koma cikin gida sam bai lura da Affan ba d'an Raihana wacce itama Raihana ta mance da d'an nata sabida firgincin halin da d'an uwanta ke ciki, to bare kuma Hayatuddeen da Ummi, cikin sassarfa ya haura matakalan benen har yana take steps bibbiyu, direct d'akin Hamman nashi ya shiga bayan wasu yan mituna sai gashi ya fito, yana gyara zaman kud'i a cikin al'jihunshi still bai kula da Affan ba ya wuce yana fitowa harabar gidan ya figi mashin nashi cikin azama ya nufi asibitin. Su Ummi kuwa bisa jagoran jami'an tsaron suka isa k'ofar d'akin da Saifuddeen yake, sai dai ba damar shiga kanshi. suna isowa bakin k'ofar Ummi ta rumtse idonta da k'arfi cikin tsananin hargitsin rayuwa tace. "B....... Hmmmmmmm. Wasa farin girgi karfa ku manta na gaya muku labarin sashi-sashine, littafin yana tafe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148