Chapter 119
Chapter 119
mugun kallo ta watsawa Mamy tare da cewa. "Mugun furuci? Akwai wani mugun furucine daya wuce abinda kuka haɗa baki kuna cewa, dan tsabar son k..". Shiru tayi da bakinta sabida yadda taga Baba malam na watsa mata kallon ki shiga hankalinki kana ya nuna mata ƙofar fita. Kamar kububuwa haka ta fice cikin zafin zuciya da takaici, tana isa parlour'nta ta rinƙa kai mari ta kai gwarzo cikin tarin takaici tace. "Shike nan ga irin ta nan, ni dama sam-sam ban taɓa yin farin ciki da wannan aiki na Zaleeha ba, ta ƙare lokutanta cikin waɗannan kurame da makafi da guragu, abinda nike tsoron shike bina, in banda tsinennen gurgu mai shegen tsaurin ido inashi ina ɗiyata da ƴaƴan ministers ma basu isheta kalloba, wayyo Allah ni Halima Allah ka dubeni da idon rahama wannan kurma kuma gurgu ya Allah tsole idonsa ya zama makaho inga ta inda zai sake kallarmin ƴa bare yace yana sonta." zama tayi bisa sofa cikin zafin zuciya da tarin masifa, sai ta kuma miƙewa tamkar an tsikareta, cikin ɗaga sauti tace. "Ina ai wlh muddin ina raye bazata taɓa saɓuwaba, ɗiyata ta zama matar gurgu kurma nakasasshe. lallai shima Ahmad, wato ɗan ubanci zai nunawa Zaleeha dan ya gadi munafurcin uwarshi, a rinƙa musu kallon salihai kuma mugaye ne." haka dai tayi ta safa da marwa tana surfa bala'i. A parlour kuwa tana fita sukaci gaba da abinda ya damesu, inda Ahmad ya matso mahaifin nashi yana karantar dashi. A can BQ kuwa suna shiga Zaleeha tayi mamakin ganin Ishaq so sai ta saki ranta a zatonta kawai ziyara ya kawo mata ba wanda Baba malam yace zai zo ɗin bane. Cikin ɗan sakin fuska tace. "Malam Ishaq kaine yau a gidanmu kai lale marhaba." cikin jin daɗin yanayin muryarta yace. "Yauwa ƙanwata yau kam dai gani na kawo miki ziyara." "Ai kuwa ka kyauta naji daɗi sannunku da zuwa." ta ƙarisa maganan tana mai kallon Ahmad. "Yauwa Amaryarmu." Ahmad ya faɗa cikin sakin fuska, da sauri ta ɗan waro idanunta wanda kuma sai lokacin ta kalli Saifuddeen dake gefen Ahmad, kamar abin tsafi idanunsu suka sarƙafe cikin na juna. wani irin azabebben faɗuwa taji gabanta yayi, wanda a take ta janye idanunta dan sam bata iya juran kallon cikin ƙwayan idanun wanna ɗan ruwan injita da faɗi. Wani dogon tsaki taja tare da cilla mishi wani zazzafan harara, kana ta janye idanunta da sauri. wanda ganin haka yasa fara'ar Ahmad daƙushewa. Rashida ce ta kalli Ahmad cikin kamala tace. "Ina wuni." jiki a sanyaye yace. "Lafiya lau ya gida." "Alhamdulillahi" Bilkisu tace dashi, ita kuwa Zaleeha juyawa tayi ta fuskanci Ishaq rai a ɗan ɓace tace. "Ya Ishaq ya mutane na?." gyara zamanshi yayi tare da shafa cinyoyinshi irin yadda al'adar makafi take yace. "Duk suna lfy sunce in gaidaki." Cikin ɗan sakin fuska ta kuma cewa. "Ina ko amsawa." sai kuma ta ɗan daure ta ɗan kalli Ahmad a fizge tare da cewa. "Ina wuni." A gajarce yace. "Lafiya!." Juyawa sukayi kan Bilkeesu jin tana cewa. "To waye ne angon namu a cikinku?." Dan so take taje taci gaba da kallonta. Ahmad ne ya kalleta cikin cikar haiba ya nuna Saifuddeen da yake hukunta Zaleeha da ƙwayar idanunshi kana yace. "Gashi nan wannan shine angon naku mai jiran gado in Allah ya yarda." Kusan a tare su duka uku suka zuba mishi ido. ita Zaleeha wani irin mutuwar zaune furucin Ahmad ya jaza mata, hatta bakinta data buɗe dan cewa hahhhh Allah bai bata iko da damar rufeshi ba. Bilkeesu da Rashida kuwa wani irin kallo sukewa Saifuddeen tare da cewa. "Masha Allah. Kai angon nan da amaryarnan sune sirrin kyau." sai kuma Rashida ta kalleshi cikin mutuntaka taka tace. "Ina wuni ango mai jiran gado." shiru bai amsaba sai ta kuma yin murmushi tare da cewa. "Rowar murya ne angon zai mana?." Ahmad ne ya d'an tab'ashi wanda sai yanzu suka lura cewa kan whellchair yake zaune. kusan a tare suka kalleshi suka kalli Zaleeha sai kuma suka kalli juna cikin tarin mmki. Bilkeesu ce tayi ƙarfin halin cewa. "Ina wuni angon Zaleeha." Kai ya jinjina mata alamar lfy, tare da yi mata mgna cikin body language. "Ya kuke." tofa abin ya fara zarta zatonsu cikin son gano gaskiyar abin Bilkeesu tace. "Wai meyasa baya Magana ne? Kodai zuwanmu tarene ya ɓata mishi rai?." Ishaq ne ya ɗanyi Murmushi tare da cewa. "No, ai kurmane bayaji kuma baya Magana." Ya ƙarishe maganar cikin rashin damuwa dan shi a wurinshi sam nakasa ba kasawa bace. Da ƙarfi suka haɗa baki wurin cewa. "Toh kurma kuma gurgu a kan whelchair!." sai kuma Bilkeesu ta tuntsure da wata iriyar dariya mai cike da jin daɗi kana ta bugi ƙafar Zaleeha tare da cewa. "To Hajiar babu nakasashe sai rago. Lallai yau shirinki ya miki rana kin samo zankaɗeɗen saurayi kurma kuma gurgu." ina ita ma Rashida tuni dariyarta da take dannewa ya subce mata. Ahmad kuwa wani irin haɗe fuska yayi tamkar zaiyi ruwan jini. Ishaq kuwa cikin kaushin murya yace. "Ke Zaleeha waɗan nan ƙawayen naki wasu irin muta nene da basu san daraja da ƙimar ɗan adam ba? me a jikinmu da zasuyi ta mana dariya." cikin dariya Bilkisu tace. "Kai tafi daga nan makahon banza makahon wofi. In banda iskanci ina wannan gurgun ina zankaɗeɗiyar baby kamar Zaleeha." Cikin zafin rai da tsawa Ishaq yace. "Ke Zaleeha ki dakatar da wannan mahaukaciyar ƙawar taki da wanna hauk..". Shiru yayi ba tare daya ƙarasa zancen nasa ba jin wani irin kuka mai cin rai da Zaleeha ta saki da ɗan ƙarfi cikin ɗaga murya tace. "Ya isa! Ya isa!! Ya isa!!! Haka malam Ishaq ka farka daga wanna wawan baccin da kakeyi har ya kaika dayin mummunan mafarki. Ƙawata ba mahaukaciya bace, sai dai ko wannan dutsen da ka zo dashi shine mahaukaci." Cikin tsananin fushi Ahmad ya yunƙura, sai ya kuma koma ya zauna jin wani irin zazzafan riƙo da Saifuddeen ya yi mishi wanda ya zubawa su Zaleeha da ƙawayenta ido yana gane duk abinda suke faɗin. Cikin zafin rai Ahmad yace. "Waye kike cewa dutsen?." A zafafe ta kalleshi tace. "Shi wannan halittan ruwan da kuka zomin dashi. Me marabarshi da dutse, kurma kuma gurgu, kalleshi kamar al'jani dan kyau. Ginennen taɓo kawai." Sai ta kuma juyo ta kalli ishaq cikin kuka ta haɗe hannayenta duka biyu wuri ɗaya alamun neman al'farma tamkar yana ganinta tace. "Dan Allah Malam Ishaq kada ka sake min wanna haukan, kadai san ina ganin ƙimarka da darajar ka, so please bana sonshi na tsaneshi!." Sai kuma ta juyo ta kalli Saifuddeen tare da cewa. "Wallahi kurwata kurr ko kaine sarkin mayu to ni nan Zaleeha nafi ƙarfinka, nan gani nan bari, ƙwalelen kare da hantar kura, mcheeww banza kawai!! " Hannu tasa ta jawo hannayensu Bilkisu daketa dariyar ƙeta tayi, fuuuuu suka fice daga cikin falon... Ina Ahmad fa bazai iya magana ba, dan tsananin ɓacin rai da jin tsanar Zaleeha a ranshi. Miƙewa yayi a fusace ya koma bayan Saifuddeen tare da tura whelchair ɗin cikin ƙunan rai yacewa ishaq. "Mu tafi ishaq." shima ishaq rai a ɓace ya miƙe yabi bayansu. Mota suka shiga, kana Ahmad ya figi motar ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148