Chapter 13
Chapter 13
kolban man shanun da suke sawa in sunyi d'umame, bud'ewa tayi tare da tsiyaya mishi kana ta mik'e ta koma kitchen robar dakekken yajin borkono ta d'auko sannan ta dawo barbad'a mishi tayi, sannan ta d'auki kofi ta nufi d'akinshi ruwa ta d'ebo mishi a wannan randar tashi, sannan ta kawo mishi tare da cewa. "Kaci kafin ku tafi." kai ya gyad'a mata kana ya kalli Umminshi dake shirya Hayatuddeen yanata zumbura baki, murmushi yayi tare da jawo hannun Hayatuddeen yana mishi tambaya irin tasu ta kurame ya tambayeshi me ya sashi fushin. Bakin ya kuma turawa kana ya rab'a jikin Saifyddeen d'in tare da cewa. "Hamma Saif ba Adda Rahma bace tayi d'umame kua tasan ni bana cin d'umame hakama Faruq da Adda Raliyya." murmushi yayi kana ya jawoshi ya ajiyeshi gefenshi, a hankali yasa cokalin da Rahma ta mik'i mishi ya gutsuri gayan kana ya dandalo miyar da taketa k'amshin man shanu, bakin Hayatuddeen ya kai, tura baki yayi tare kwabe fuska kana yace. "Na k'os. " bai k'arisa mgnar tashiba yayi shiru, jin ya sa mishi loman a bakinshi, lumshe ido yayi tare da fara sarrafa abincin, saida ya had'iye kana ya bud'e idanunshi tare da cewa. "Dad'i wlh miyar tayi dad'i Faruq zo kaci." Ummi kam da Raihana dake shirya Faruq tuni dariya sukeyi, shima Saifuddeen dariya yakeyi har saida dimples nashi suka lotse sosai kana fararen hak'oranshi suka baiyana manyan idanunshi ya lumshe tare daci gaba da basu abincin a baki, aifa sukaci sukayi nak, sannan suka tafi makaranta, ita kuwa Raihana da sauri ta fita tace. "Adda Rahma ki samishi wani abincin su Faruq sun cinye wannan, harda santinsu." dariya sukayi kana Rahma ta samishi wani yana cikin cine Salisu ya shigo nan sukaci tare kafin suka fita suka tafi. Yauma kamar kullum Saifuddeen wuni yayi yana yawo da bulayi a kasuwa, sai da magrib tayi ya fito, kana yayi salla kafin Salisu yazo ya d'aukeshi yau ma fura da nono yasha da zasu tafi. Haka dai Saifuddeen yayi ta fama yawo da wahala a cikin kasuwar Gombe har tsawon kwana bakwai, to a ranan ne kuma Salisu ya basu balance ensu kamar yadda sukayi duk sati zaike basu dubu biyar. Koda ya karbi kud'in Bappa Ali ya kaiwa su, shi kuwa Bappa Ali k'in amsarsu yayi yace ya kaiwa Ummi kud'in zasu samu abinda zasuke sarrafa cefenen abincin. da yake har yanzu sunada sauran abincin da baban Arabi ya kawo musu. Shi kuwa Saifuddeen sai ya zare dubu biyu ya bawa bappan nashi, amman sam yak'i karb'a acewarsa ai da yanada hali shine ya kamata ya basu, to dai ganin Saifuddeen ya b'ata rai ya sashi amsar 1k yasanya al'barka. Shiko yaje ya bawa Ummi dubu uku sannan ya d'auki dubu d'aya. Ummi kam sai sanya mishi al'barka takeyi. Washe gari kamar kullum suka shirya suka tafi cikin. Gombe a inda ya saba sauk'eshi yau ma nan ya sauk'eshin, bayan Salisun ya tafi shi kuma Saifuddeen sai ya d'anyi tattaki zuwa bakin mashigar kasuwar, addu'a yayi kamar kullum kana ya shiga da k'afar dama, yauma bakin shagunan yayi tabi har kusa k'arfe shad'aya lokacin rana ta tsala zafi ya fara, sai ya nufi layin masu robobi, yana zuwa shagon wani bayerbe sai ya tsaya, bokatin kand'e tsirara ya saya wanda wasu ke cemai ganta sarai, bayan sun gama ciniki cikin mgnar kurame ya bashi dubu d'ayannan, kana bayerben ya bashi canjinshi, daga nan ya nufi wani layin tafiya kad'an yayi sai gashi a wani babban shago da yake cike da d'ima-d'ima firiji masu tsawo da masu fad'i. Yana zuwa d'aya daga cikin yaran shagon yace mishi. "Kana son ruwane?." da sauri ya gyad'a mishi alamar eh. shi kuwa yaro bud'e wani k'aton firiji yayi kana ya juyo ya kalleshi, sannan yace. "Leda nawa kake so?." hannunshi ya d'ago kana ya had'a yatsunshi biyu yayi mishi alama da leda biyu yakeso. cikin mmki yaro ya kalleshi kana ya kawo mishi leda biyun sannan yace mushi. "Kai kurmane?." murmushi Saifuddeen yayi kana ya gyad'a mishi kai tare da mik'a mishi d'ari biyun, amsa yayi tare da bashi canjinshi kana yace. "Kuma naga kamar kana gane abinda nake fad'i ko?." still kai ya gyad'a tare dasa lododin ruwan cikin bokatin daya saya d'in, a take botikin yayi sanyi sabida ruwan yanada tsananin sanyi wasu har sun fara yin k'ank'ara, shi kuwa yaron shagon ashirin ya kuma zarowa a al'jihunshi kana ya mik'a mishi tare da cewa. "Gashi nayi maka ragin naira 10 cikin ko wanne leda akan yadda muke sararwa Allah ya baka sa'a inka k'arema kazo zan ajiye maka mai sanyi." cikin murmushi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai alamun baya son ragin, kana ya juya ya nuna mishi sauran yaran ya mishi alamun da sai dai in suma duk za'ayi musu ragin, cikin sauk'e numfashi yaro yace. "To sadaka na baka." fuska ya had'e kana ya tsuguna gefe tare da rubuta mishi. "Bara nazo makane da zakace sadaka ka bani? in sadaka kakeson badawa kaje gidan marayu da gajiyayyu, ni karka kashe min zuciya, ka dai ajemin mai sanyi in wannan ya k'are zan kuma zuwa." hannu yaron ya bashi sukayi musabaha lokacin daya karanta rubutun kana yace. "To kayi hak'uri abokina sai ka dawo d'in." kai ya jinjina kana ya juya hannunshi rik'e da botikin. ya fara bin layi-layi yana yawo, amman babu wanda yace mishi kawo, har ruwan ya fara rage sanyi. cikin gajiya ya dawo bakin shagon masu kayan kitchen inda ya huta jiyan nan, inda ya zauna jiyan yauma nan ya zauna ya tasa batikin a gabanshi. yaron jiyan ne ya kula dashi cikin fara'a yace. "Balarabe yauma ka zone?." cikin gajiya ya lumshe mishi idanu alamar eh, shi kuwa yaron shagon cikin karantar yanayinshi yace. "To yau ma hutawa kazo yine ko zaka sayi abune?." da ido ya nuna mishi botikin pure water enshin, cikin sauri ya zaro ido tare da cewa. "Wai kai dama tallan ruwa kakeyi ne?". Kai ya gyad'a mishi tare gyara zamanshi, cikin sanyi yace. "To wai kai kurmane naga jiyama har ka tafi body language kakeyi min." still sai ya d'aga mishi gira duka biyu alamun eh shi kurmane. da sauri yaron ya kalli alajin shagon cikin tausayawa yace. "Abba kalli wai wannan Balaraben kurmane kuma wai ruwa yake saidawa." sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da yin rau-rau kamar idanunshi zasu zubda hawaye, ganin haka da sauri Saifuddeen ya jujjuya mishi kai sannan yasa hannunshi bisa idanunshi alamun kar yayi kuka. still shima wanda ya kira da Abba sai ya zuba musu ido tare da cewa. "To Hisham kafi ubangijin daya halicceshi a haka sonshi ne? kada kayi kuka kasa mishi rauni, ai ita Nakasa ba kasawa bace, bare wannan mai nagartane Kaga dai jiya kun dad'e tare amman duk bamu gane kurma bane kuma kaga yana gane duk abinda muke cewa. So shi bai sa nakasar jikinsa ta zamar mishi na zuciya ba." Jin haka sai Hisham ya sharshe hawayenshi kana yayi murmushi tare da bawa Saifuddeen hannu yace. "Daga yau kai aboki nane." shima Saifuddeen murmushi yayi, shi kuwa Alhaji Ibrahim al'barka ya samusu. Sai ya kuma kalli costumers insu da suke cike da shagon inda d'aya daga cikinsu ta kalli botikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148