Skip to content

Chapter 109

Chapter 109

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

ya gane me ta fad'i mishi, ita kuwa hararanshi ta kumayi kana taci gaba da aikinta. Shi kuwa Saifuddeen cikin lumshe ido da shak'ar sassanyar iskar AC mai cike da k'amshi a ranshi yace. "Uhummmm bazan ci kaina ba in sha Allah ke d'in dai zan c...! Duk fa masu bin labarin nan kunsan sashi sashi muke binshi, to da ganin yanzu kun san mun shigo wani sashi na musamman kuma. Wasan yanzu zai fara. Dan Allah da darajar iyayenmu da girman Al'arshi Kada ki fitarmin da littafi na, in kin fitarba ba sai nace Allah ya isaba ko inyi zagi da tashanci ba damn tijar maguzawa ba, No da Allah isasshene kuma shi yana sane daku in ni bana sane daku, kuma shine zai mana hisabi. Dan haka ni bazan zageku ba bare in zagi iyayenku, dan nasan darajar nawa iyayen ko k'abilata bana so a zaga bare iyayena shiyasa bazan zagi iyayen wasuba🤗🤗🤗 BY *GARKUWAR FULANI* 8/18/20, 7:56 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *NAKASA BA KASAWA BACE* *Page 26* *NA* *AISHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Lumshe ido yayi tare da yin magana a cikin zuciyarshi. "Uhmmm bazanci kaina ba insha Allah keɗin dai zan ci!". Sake ɗago idanunsa yayi ya watsa mata su, ita kuwa Zaleeha daketa ƙoƙarin tattara kayan aikinta ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, duk da cewa ba kallonsa takeyi ba amma tabbas tanajin idanunsa na yawo ajikinta, tana gama haɗa kayan aikin nata taɗan ɗago da kanta,aikuwa idanunsu ne ya sake sarƙefe acikin na juna, "Anya wannan ba maye bane!". ta kuma faɗa cikin ƙasa-ƙasa da murya tana me wurga masa harara da kyawawan idanunta. Lumshe idanunsa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa dake beating, tabbas yau yasamu nutsuwa irin wacce yajima bai samu ba, bakomai ke tafiya da hankalinsa ba face yanda take kaɗa idanunta wajen hararansa, harshe yasanya ya ɗan lashi red lips ɗinsa, yanaji ajikinsa inama da yana da damar da zai kusan tota garesa, tabbas daya jawota jikinsa yayiwa wannan bakin tsiwannanta shan tom-tom. hand bag ɗinta ta rayata abisa kafaɗanta tare dakai dubanta ga jama'an dake gabanta, sallama tayi musu akan cewa zata wuce, cikin takunta dake matuƙar ɗaukar hankalin maza ta tako harzuwa inda Ishaq yake, ƙarasowanta garesu yayi dai-dai da kusan ɗaukewar numfashinsa sakamakon daddaɗan ƙamshinta daya samu cakuɗa da numfashinsa, cikin wani irin kasala ya lumshe beautyful eyes ɗinsa. Saura bai wuce taku huɗu ba ta ƙaraso garesu ta tsaya cak tare dayin ƙasa da kanta, sam batajin zata iya kallon cikin idanun Saifuddeen dan wata azababbiyar fitina take hangowa cikin kwayar idanshi mai kama da maganad'isu haiba da kwarjinshi yana sa zuciyarta cikin wani yanayi, hakanan ƙarasowarta garesu ya haifar mata da faɗuwar gaba yayinda ƙirjinta ke duka da sauri-sauri. Cikin tausasa murya ta dubi Ishaq daketa faman murmushi kamar yana ganinta, "Malam Ishaq nizan wuce sai kuma idan munsake haɗuwa wani sati Idan Allah yakaimu!" Murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa, inda ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Saifuddeen cike da ƙaunar Saifuddeen ɗin yace "To bari nai miki rakiya Malama Zaleeha, amma fa wani sati kishirya don kuwa baƙonki na musammanne, abokina Saifuddeen kenan!". Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya daki zuciyar Zaleeha cike da haushinsa ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa harara, inda still ta kamasa yana kallonta, "Nasani ae dama kallona kake maye kawai!". tafaɗa cikin ƙasan maƙoshi tana me mulan-mulan da bakinta, Murmushin daya ƙara bayyana zallan kyau da kwarjininsa yayi, sarai ya fahimci me take faɗa cikin ransa yace. "Zakisan kuwa ni maye ne na gaske duk randa kika shigo hannuna!". Sake gayara zaman jakarta akan kafaɗarta tayi inda ta juya cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta nufi hanayar da zai fitar da ita daga cikin falon, tare da Ishaq suka jera suna tafiya, suna ɗan hira sam idan kaga Ishaq bazakayi tunanin makaho bane. Da wani irin kallon So, haɗi da shauƙi tare da zallan k'auna Saifuddeen ya bita, komai nata abun burgewane, idanunsa ne suka sauƙa akan tsararren hips ɗinta da cikin salo suke juyawa, saurin lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa, don kuwa wani irin harbawa yaji jikinshi da zuciyarshi sa nayi, wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da buɗe idanunsa, dai-dai lokacin ita da Ishaq suka fice daga cikin falon, murmushi yayi tare da ɗan sanya hannu ya shafi lafiyayyen sajen dake kwance akan fuskarsa. Sannu ahankali gaba ɗaya mutanen dake cikin falon suka soma watsewa kowa ya kama gabansa. Har bakin motarta Ishaq ya rakata, inda sosai taji daɗin rakiyar tasa, cikin muryarta dake nuna jin daɗin rakiyar tasa tace. "Godiya dubu Malam Ishaq!". Murmushi Ishaq yayi tare da cewa. "To Malama Zaleeha kigaida mutanen gida!" Da "To" ta amsa masa, kana ya juya yakoma inda yabar Abokinsa Saifuddeen. Murfin motar ta buɗe ta shiga tare da murza mata key, dai-dai-ta tsayuwar motar tata tayi, cikin tuƙinta me ɗauke da nutsuwa ta fice daga cikin harabar ofishin ƙungiyar ta (Jonapwd), cikin salo take murza kan steering motar tata, tunaninsa ne ya faɗo cikin ranta, hakan yasa ta saki wata ƴar siririn tsuka tare dayin ƙwafa, cike da haushin irin kallon daya dinga yi mata ta murguɗa baki tare da yin guna-guni acikin ranta inda tace "Mutum gurgu sannan kurma amma sai shegen sa'ido, no wonder akace gurgu kafi me ƙafa iya shege!". tafaɗi haka adai-dai lokacin da take shan wata kwana. Ishaq na dawowa cikin falon, ya iske Saifuddeen wanda ke zaune cikin matsanancin shauƙinta. Hannayen Saifuddeen ɗin Ishaq ya riƙo cikin nutsuwa yace. "Saifuddeen kaga Zaleeha ko, tana da kirki sosai sannan akwai nutsuwa atattare da ita, sam kyawunta baisakata yin ɗagawa ba". Murmushi Saifuddeen yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya rubutawa Ishaq saƙo kamar haka. "Nayaba da hankalinta matuƙa ishaq, saboda hakane ma na zaɓeta a matsayi. Matar aurena uwar ƴaƴana in Allah ya yarda, ba dama nace maka nasamu matar aure!". Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace. "Wai kana nufin Zaleeha?" Still murmushi Saifuddeen yayi inda ya rubata cewa. "Inasonta Ishaq, haƙiƙa ina tsananin sonta, harma inajin kowani bugu na zuciyata tare da zallan soyayyarta yake tafiya, Inaso na Aureta! Ishaq tun randa na fara ganinta sonta ya zame min abokin rayuwa, shiyasa kullum mukayi mgna da kai sai na tambayeka ita da lfyarta". Koda Ishaq yagama sauraran batun wani irin tsananin farin ciki ne ya lulluɓesa, haƙiƙa baya gani da ido amma yana gani da zuciya, kuma tuni zuciyarsa ta gama karanta masa kyawawan halayya da kuma nagarta irin na Zaleeha, tabbas zaisowa abokinsa Saifuddeen samun mace irin Zaleeha amatsayin mata, cikin jin daɗi tare da son ƙarfafawa Saifuddeen ɗin guiwa Ishaq yace. "Naji daɗi Saifuddeen, kuma zanfi kowa so da muradin kasantuwar aurenku da Zaleeha, saidai kuma baza muyi gaban kanmu ba, zaifi kyau mu fara sanar da manya don baza muje haka kawai ba sai da ƙarfin mu, ma'ana sai munsamu amincewar manyanta, tabbas ayanda nasan Zaleeha nasan tanada nagarta, kuma zata soka". Ya k'arishe mgnar cikin karsashi domin su basu sawa ransu cewa nakasarsu zata zame musu kasawa ba, bare ta hanasu neman duk wani abinda mai cikar

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148