Skip to content

Chapter 104

Chapter 104

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

sajensa wanda tayi matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini dan yadda ya cika yayi lip-lip a farar fatarshi tayiwa fuskar tasa k'awanya, yana kammalawa, yashafawa kansa wani hair oil me ƙamshi, kekensa ya tura har zuwa gaban tangamemen sif ɗinsa, inda aka jere masa gaba ɗaya kayan sawansa a hawa na ƙasa dana tsakiya wani long jeans black colour ya zaro tare da kai dubansa ɓangaren da t-shirt's ɗinsa ke jere reras, gaba ɗaya kayan sawansa sabine ƙal ƙal, wata white polo shirt ya ciro me kyau, cikin dabara yasanya wandon ajikinsa tare da zura farar t-shirt ɗin ajikinsa, masha Allah sosai yayi kyau yayinda gashin kansa keta faman ƙyalli, rufe sif ɗinnasa yayi tare da sake tura kekensa ya ƙarasa gaban mirror, farfumed ya fesa ajikin kayan nasa tare da ɗaukan wayarsa, tura kekensa yayi ya ƙarasa gaban bedsite carbinate inda anan aka aje masa sallayan yin sallan sa, ɗaukan sallayan yayi tare da shimfuɗawa kasancewar lokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Isha, cikin hikima ya sauƙo daga kan kekennasa tare da zama akan sallayan, azaune ya gabatar da sallan isha'ɗinsa yayinda daga ƙarshe ya haɗa da shafa'i da wuturi, akan ƙafafunsa ya zauna inda yajima yana tasbihi, hannunsa ya sanya ya ɗauko al'ƙur'anin dake aje kan bedsite, ɗaura ƙur'anin yayi akan cinyansa tare da buɗe suratul Ma'idah ahankali cikin nutsuwa yashiga rera karatun yayinda zazzaƙar muryarsa ke ratsa mishi zuciyarshi, aƙalla ya ɗauki wasu mintuna kafun ya kammala karatun addu'a yayi tare da shafawa kana ya rufe Al'Qur'anin, gadonsa yaɗan dafa tare da jawo wellchair ɗinsa ya yunƙura tare da komawa kai ya zauna, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga duba harkan kasuwancin su, daga nanne kuma yashiga duba labaran halin da duniya take ciki. Hayatuddeen ne yaturo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda hannunsa ke ɗauke da ɗan ƙaramin tray wanda samansa ke ɗauke da yankakkun fruits masu sanyi sai goran ruwa mai sanyi kana d'aya hannunshi rik'e da robar magunguna, ƙarasowa cikin ɗakin yayi tare da duban hamman nasa da gaba ɗaya hankalinsa ke kan laptop ɗinsa, cikin kulawa ya aje tray ɗin akan table d'in glasses dake gaban gadon hamman nasa tare da cewa. "Hamma kasha fruit inji Ummi, ga kuma magungunan ka" ido ya d'an lumshe tare da ƙaɗa kansa alamar to, ɗaukan green apple wanda yake ba'a yanke ba yaɗan gutsura, lumshe idanunsa ya kuma yi tare da soma tauna apple ɗin ahankali, ganin haka yasanya Hayatuddeen sakin murmushi tare da ɗan matsowa kusa da hamman nashi, wayars ƙiran Samsung galaxy S10 ya ciro tare da shiga camera, hannayensa ya sanya akan kafaɗun Hamman nasa ya ɗaukesu hoto selfie wanda dukansu murmushine ɗauke akan fuskarsu, sosai sukayi kyau a hoton bama kamar Saifuddeen, komawa gefe Hayatuddeen yayi inda ya shiga Whatsapp ɗinsa ya ɗaura hoton nasu da sukayi a status ɗinshi. Shikuwa Saifuddeen sosai yasha kayan fruits dan shi yafi ta'ammali da yayan itatuwa fiye da abinci, bare kuma yanzu da likitocin suka umarceshi da yawanta cinsu. Maganinshi ya sha. ya gamawa sauƙa yayi daga kan wellchair ɗin ya kwanta akan lallusan gadonsa wanda yaji tattausan katifa, luf yakwanta tare da ɗaura kansa akan pillow kana yaja blanket ya rufe rabin jikinsa, ganin haka yasanya Hayatuddeen ɗaukan ragowan kayan marmarin yafice daga cikin ɗakin, ganin fitan Hayatuddeen yasanya Saifuddeen yakai hanunsa saman gadonsa inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe, bedsite lamb wanda ke bata light blue ɗin haske ya kunna tare da sake gyara kwanciyarsa, wani irin sha'awane yasake taso masa wanda yasanya ya kasa bacci sai juyi yaketayi akan makeken gadonnasa. A hankalin Umminshi ta shigo, taku takeyi a hankali dan ganin alamun yayi bacci, kanshi ta iso tare da zuba mishi ido, sai kuma tayi saurin sunkoyowa kanshi jin ya kamo hannunta, murmushi tayi mishi mai cike da k'aunan gudan jinin nata, sannan tasa hannunta na dama ta shafa kanshi tare da cewa. "Ka gaji da yawa kayi bacci ka huta, ko Babana." kai ya gyad'a mata tare da sumbatar hannunta kana ya maida idanunshi ya lumshe a hankali. Ganin hakan yasa Ummi gyara mishi blanket d'in daya rife iya k'ugunshi sannan ta fita, tare da ja mishi k'ofa. A parlour ta samu Ahmad yanzu ya dawo daga meda Rahma gidanta, Ganin kamar yana buk'atar matarshi ne yasa Ummi cewa Raliya. "Ke Raliya dare yayi ni zanyi bacci tashi ku tafi." cikin gajiya dan yau kusan wuni tayi hidima, mik'ewa tayi kana tabi bayan Ahmad da tuni ya fita cikin jin dad'i. Ita kuwa Ummi ita da Raihana ne sukaci gaba da hirar. Hayatuddeen kuwa yana maida plate ɗin kayan marmarin kitchine direct sama ya haura inda ɗakinsa yake, yana shiga ya faɗa kan gado tare da shiga cikin Whatsapp ɗinsa don yaga anturo masa new messages da yawa, sunan Asma'u Ahmad Matawalle ce a sama tayi masa comment akan hoton nasu daya sanya a status ɗinsa inda tayi rubutu kamar haka. "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai da ya halicci Saifuddeen cikin wannan halitta mai d'aukan hankali" murmushi mai kama da dariya Hayatuddeen yayi tare da yi mata reply inda yace. "Kuɗin ganin status yawane dashi ina fatan zaki iya biya?". Itama dariya tayi kana tace "Zan iya bada gaba ɗaya dukiyata indai zanke ganin wannan kyakkyawar fuskar ɗan uwannaka ako da yaushe". Yanzu kam dariya Hayatuddeen yayi sosai yayinda ya rubuta cewa. "Sai kiyi ta addu'a dan samun Hammana sai mai tsananin rabo, dan sai ya zaɓa kuma saiya darje, kuma shi mijin mace d'aya ne d'aya tak" Itama dariya tayi sosai don tasan Alhamdulillahi itama tana da nata kyaun yanda bakowani ɗa namiji bane zai ƙita, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan da ita duk kuma zancennata akan Saifuddeen ne, don sosai ya tsaya mata arai. Saifuddeen kuwa yasha juyi kafun yasamu da ƙyar bacci ya ɗaukesa, ko acikin baccin nasa kyakkyawan fuskar Zaleeha itace keta zuwar masa, inda yayi bacci cikin wani irin shauƙi. Washegari. Ƙarfe tara tuni yagama shirya kansa inda yayi kyau cikin riga da wandon jeans ɗin dake jikinsa, ahankali yake tafiya da keken nasa harya kawo bakin ƙofar fita daga ɗakin, hannunsa yakai jikin handle ɗin ƙofan ya buɗe, yanzukam da kansa yake tuƙa keken nasa cikin nitsuwa da salonsa na k'in wahala inda ya dumfaro babban falonnasu. Ummi, Hayatuddeen, da kuma Raihana su ya tarar zaune acikin falon,yayinda Raliya ke ta kaikawo tsakanin dinning area da kitchine tana shirya musu breakfast, shigowarsa cikin falon shi yabayyana murmushi akan gaba ɗaya fuskokin ƴan uwan nasa, ƙarasowa tsakiyan falon yayi tare da kai dubansa ga mahaifiyarsa wanda takasa ɗauke idanunta akansa, murmushi zallan ƙaunarsa ne kwance akan fuskarta, murmushin daya bayyana kyawunsa yayi tare dayi mata alaman. "Ina kwana" "Lafiya ƙalau Saifuddeen ya jikin naka?". Ummi tafaɗa cikin kulawa. Da body language yayi mata alaman. "Da sauƙi" nan Raihana ta gaidashi tare da tambayar jikinsa, itama da body language ya amsa mata fuskarsa ɗauke da murmushi tare da mik'o hannu ya shafan kan Affan dake kwance bisa jikin Ummi. Raliya da Hayatuddeen ne suka gaidashi, suɗinma amsa musu yayi cike da ƙaunar ƴan uwannasa. Raliya na gama shirya musu break fast shida kansa ya sarrafa kekensa har zuwa kan dinning table ɗin, kujera ɗaya ya matsar gefe kana ya

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148