Chapter 121
Chapter 121
ɗinsa ya buɗe tare da ciro wata farar short sleeve da kuma wani combat 3 guater jeans ya sanya, sosai kayan suka amshi jikinsa, kasancewar akwai alwala ajikinsa, yasanya ya shumfuɗa sallaya tare da sauƙa daga kan kekensa, kamar kullum kuma koda yaushe azaune ya gabatar da sallan Magrib ɗinsa, bai tashi akan sallayan ba harsaida yayi sallan Isha, koda ya gabatar da addu'o'insa kamar yanda ya saba, yunƙurawa yayi ya hau kan kekensa, cikin nutsuwa ya shiga tura keken nasa har izuwa bakin haɗaɗɗen gadonsa wanda aka lailaye samansa da tattausan bedshet mai kyau, cikin hikima ya sauƙo daga kan keken nasa tare da kama jikin gadon nasa ya hau, kwanciya yayi luf akan gadon tare dakai hannunsa gefen gadon inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe, bedsite lamb ya kunna, sai yanayin ɗakin yayi daɗi shiba duhu ba shikuma ba wadataccen haske ba. Ɓangaren Zaleeha kuwa, ranta amatuƙar ɓace haka suka koma falon Mama, cikin rufewar ido Zaleeha na shiga cikin falon ta yaye mayafin kanta, saboda tsaban ɓacin rai da takeji, idanunta har rufewa suke, cikin ƙunan zuciya tace. "Ni! wai ni! Zaleeha Kurma kuma Gurgu zaizo yace yanaso, lallai mutanen nan sunfara ganin damata da yawa, chab lallaima nakasassunnan, wato shiga cikinsu da nakeyi ina murmushi shine abun dayasa harsuka rainani ko, waima wannan ɗan ruwan ni zaice yanaso na, ko nayi masa kama da kalan matar aurensa ne?, da sauri taƙarasa gaban ƙaton madubin dake jin k'ofar falon, tsayawa tayi tana me ƙarewa kekyawar surar jikinta kallo, wani irin kuka ta fashe dashi tare da kai dubanta ga su Balkisu waƴanda sukayi saƙare suna kallonta, cikin ƙunan rai da sheshsheƙan kuka tace. "Shin nima akwai wata nakasa ajikina ne dahar wani banzan nakasashshe zaizo yace yana sona?". Dariya Bilkisu ta kwashe dashi cikin tsananin shaƙiyaci tace. "Kawai ganin dama ne irin nasa, hmmm amma wallahi wannan mutumin ya raina miki hankali, tayaya ma in ban da rashin tunani irin nasa da tsaurin ido zai dubi ajibon yarinya kamarki yace wai yanaso". Dariya ta ƙara kwashewa dashi tare da tafa hannunta, cikin son ƙara cusawa Zaleeha tsanan Saifuddeen tace. "Kurma fa, kuma bayan haka ma wai gurgu, lallai kam aikuwa daki auri wannan gwara kin auri dutsi, donshi dama dutsi-dutsi ne bayako motsi, sai inke kika motsa shi, amma wannan kam banga dame zai amfaneki ba, saidai in kuma ko zaman jinyarsa zakiyi ba zaman aure ba!". Rashida ce ta sauƙe ajiyar zuciya tare da duban Bilkisu dake ta dariyan mugunta, cikin ƙasa da murya tace "Haba Bilkisu dan Allah kibari hakanan, nifa Allah gayen yabani tausayi, sannan tsantsar kyawunsa ya tsoratani, koda farko Allah banso yin dariya ba kedaice kika sani, amma gaskia gayen sam bashida wata makusa, kunfasan wata nakasar bata zama kasawa, idan kikaga nakasashshe ya kasa, to tabbas ya kashe zuciyarsa ne, kuma kunsan nakasar zuciya tafi kowacce nakasa ciwo, sannan ayanda na fuskanci mutanen nan sam su awajensu. Nakasarsu ba kasawa bace, don tabbas baƙaramin jahadi sukayi ba da sukazo miki da maganar Soyayya kuma ai komin yaya masoyi yafi mak'iyi". Wata uwar harara Bilkisu ta aunawa Rashida cike da baƙin ciki tace. "Tab amma dai Rashida baki da kai, me za'ayi da waƴannan nakasassun, kyawunsa na banza na wofi, idan kece suka zo gunki da batun soyayya na tabbata bazaki amince ba." Tsagaitawa da maganan tayi tare da dafa duka kafaɗun Zaleeha cikin zugan hasada tace. "Wallahi kada kiyarda ki kashe rayuwarki wajen zama da nakasasshe, me wannan zai yi miki wanna ai dashi da mace duk d'aya, saidai baƙin cikinsa yayi ajalinki, da kyaunki da ƙuruciyarki da komai ki cuci kanki ki auri nakasasshen da bazai iya kauda miki budurcinki bama, ae wallahi Zaleeha kinci baya!". Wani irin kuka Zaleeha ta sake tare da faɗawa jikin Bilkisu cikin aminta da kalaman nata tace. "Bazan taɓa sauraransa ba Wallahi, koda ace duk duniya zasu taru akaina don na soshi, na kuma zauna dashi, bazan taɓa aminta ba, Wallahi na tsaneshi tsana me tsanani, danayi rayuwar aure dashi gwara na mutu, don bazan iya ɗaukar baƙin cikinsa ba!!". Cikin kukan dayaci ƙarfinta ta juya da gudu ta wuce ɗakinta. Wani irin munafukin killer smile Bilkisu tayi tare da bin Zaleehan da kallo. Rashida kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantar da kanta gefe, cikin sanyi tace "Amma Bilkisu dakin tausasa harshenki akan sa, saboda ƙaddara nakan kowa.....". "Dakata Rashida ai nima nasan ƙaddara nakan kowa, amma wannan nakasashshen gurgunne dai Insha Allah Zaleeha bazata aureshi ba". Ajiyar zucia Rashida ta sauƙe tare da ɗaukan jakarta, duban Bilkisu tayi tare da cewa. "Natafi sai gobe saduwar al'khairi". Da sauri itama Bilkisu ta ɗauki jakanta tabi bayan Rashidan, don sam bataso kowa yagane ainihin nufi dakuma abun dake ranta da zuciyarta, saboda ita tamkar mage take me kwanciyar ɗaukan rai... SAIFUDDEEN. Gyara kwanciyarsa yayi tare da gyara zaman kansa dake bisa pillow, idanunsa ya lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, filla-filla kalaman Zaleeha da ƙawayenta ke dawowa cikin idanunsa, inda idanunsa keyi masa imagine duk wani motsin bakinsu, ƙam-ƙam haka ya kulle idanunsa tare da cije laɓɓansa, haƙiƙa yaji kalamanna Zaleeha har acikin zuciyarsa, saidai kuma tsananin soyayyar da yakeyi mata yariga dayaci ƙarfinsa. Jin soyayyarta yake Tamkar zata zautar dashi, sake lumshe idanunsa wanda ke ɗauke da tsananin mayen sonta yayi, wani irin murmushi yayi wanda ya ƙawata fuskarsa, cikin zuciyarsa yace. "Dakin sani da baki nemi cin zarafinmu ba, domin hakan da kikayi bazai taɓa sanyawa na janye batun aurenki ba, ko yasa muradinki ya fita araina ba, kin ƙaramin sonki sannan kuma kin ƙara min kwaɗayi da burin aurenki, bazai taɓa yiwuwaba, kowacce ƙaddara da sanadinta, kuma ni dai nasan Allah ne ya d'ora min sai daifa duk abinda ya sameni arayuwa ta sanadiyarkine, kece kikajamin komai, sannan kuma dole ke zan aura, kamar yanda ƙaddarata akanki take to dole kema saikin ɗanɗani ƙaddaranki dake kaina, zan aureki koda bakyaso!, zankuma shayar dake mmaki da zazzafar soyayyata irin wanda zata zautar dake batare dakin shiryawa hakan ba!". sake muskutawa yayi tare da gyara kwanciyarsa, tabbas ayanzu yaɗauki ɗamaran fuskantarta sam kuma bada wasa zaije mata ba, lallai al'ƙawarine sai ya shayar da ita ruwan mamaki, haka yadinga saƙa abubuwa da dama aransa har bacci ɓarawo ya ɗaukesa. Ɓangaren Zaleeha ma da ƙyar ta iya bacci, ita kaɗai tasan irin suyan da ƙirjinta keyi mata, haƙiƙa sosai zuwan kurma kuma gurgun da ko son jin sunansa batayi ya ɓata mata ranta, babuma abun dake hassalata kamar irin kallon da taga yanayi mata tamkar wani tsohon maye bugu da k'ari kwarjinshi na sata rud'ewa, sannan kuma ta lura duk irin rashin mutumcin data surfa masa sam bai ɓata ransa ba, don bata ga alaman ɓacin rai akan wannan munafukar farar kyakkyawar fuskartasa ba, yau ko tunanin abincin ruhinta batayi sosai ba saboda baƙin ciki, haka tayi bacci cikin ƙuncin rai, wani abun mamaki kuwa fuskarsa ce tayita zuwa mata acikin baccinta. Washegari. Saboda yanda ranta ke ɓace sam ko shirin fita wajen aikima batayi ba, don gaba ɗaya jinta take wani irin kamar wata marar lafiya. Saifuddeen kuwa yau da wani irin sabon tsarin plant ya wayi gari, harzuwa yau yanajin cewa shi nakasarsa ba kasawa bace agaresa, akan dinning
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148