Chapter 133
Chapter 133
fuskarnan kamar zatayi ruwan jini Mama ta amsa musu kana ta gaida Baba malam, sannan Ahmad da Habu suka gaidata, Zahira kuma duk ta gaidasu sannan ta wuce cikin gidan tayi shashin maman. Ita kuwa Mama a hankali ta mik'e ta fita ganin duk basubi ta kantaba, to wazai kulata yadda taketa harare-harare, tana fita ta nufi Side d'inta da yake tsab Maryam da Aunty Lubna sun gyarashi jiya da dare. A parlour ta zauna, dai-dai lokacin kuma Zahira ta fito daga bedroom d'in Maman a guje, ganin Maman a parlour yasata tsayuwa cikin rawan jiki da halin fitina tace. "Mama zo zo zo kiga wani abu a bedroom naki." tsaki ta d'an ja tare da cewa. "Menene kike wani zaro idanu haka?." hannun uwar ta kamo tare da cewa. "Mama zo ki gani mana an cika miki d'aki da akwatuna dasu buhunan gishiri dasu goro." ido ta zaro gaba d'aya tare da cewa. "Akwa tuna kuma to na meye." cikin hatsabibanci tace. "To waya sani ko lefen Anty Zaleeha aka kawo." ai kafin ta rufe bakima Mama ta kutsa kai cikin bedroom ɗin. wani irin wawan birki taja tare da cewa. "To wanna kuma daga ina, to ko Abdussalam ne da tace mishi a turo komanshi Zaleeha ta yarda dashi, tuni ya turo ɗin, sai kuma ta girgiza kai ina sam ba shi bane ai in shine zai gaya mata, shida kuma ɗazu suka gama mgna, cikin tafasan bala'i tace to waye. Sai kuma ta dawo parlour da sauri cikin karad'i da kware murya baki d'aya ta fara rabkawa Habu kira. "Habu! Habu!! Habu!!! Habuuuu!." da sauri ya iso cikin parlourn a tsorace yace. "Na'am Mama ganifa nazo." A hatsale tace. "To dan ubanka meyasa bazaka amsa da kyau ba." cikin had'e fuska yace, "Na'am." cikin yamutsa fuska tace. "Wancan kayan fa na meye ne." Kai tsaye yace. "Lefen Zaleeha aka kawo jiya." cikin ɗaga sauti tace waye kawo lefen?." A dake yace. "Wasu mata ne." zaburowa tayi kanshi tare da cewa. "Dan ubanka ba wanda suka kawo nake tambaya ba wanda aka kawowa nake nufi." cikin kauda kai yace. "Zaleeha aka kawowa." wani dogon tsaki taja tare da jawo hannunshi tace. "Kai mahaukacin inane wanne saurayin ne ya aiko lefen." Cikin dakiya da rashin tsoro yace. "Saifuddeen." wani irin zabura tayi tare da buga tsalle tace. "Inji uban waye ya basu damar kawo banzayen lefen wanna musakin d'an nasu?." Yana fita yace. "Inji Baba Malam mana Baban Zaleeha shine ya basu dama." wani irin kware murya tayi tare da yin sauri ta nufi parlour Baba malam tana shiga parlour tare da masifa murya a hargitse tace. "Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya....! *Dan Allah da manzonsa ku dena fitarmin da littafi,* By *GARKUWAR FULANI* 8/ *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 30* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 "Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya na biyu". Fuska ta ƙara haɗewa tamkar wacce akayiwa bushara da mummunan al'kaba'in rayuwar duniya. Ido suka zuba mata baki ɗayansu, tare da maida hankalinsu gareta. Cikin takaici da tashin hankali tace. "Meyasa! Meyasa haka ne malam? Ina dalilin kullum sai an sani baƙin ciki kan aurar da ƴaƴana?." Kauda kanshi yayi daga kallon mummunar fuskarta tare da maida dubanshi ga al'ƙiblah, a hankali yaci gaba da tasbihi da yakeyi. "Subahallahi, walhamdulillahi, wa la'ilahalillahu, wallahu akhbar." haka yaketa mai-maitawa tare da motsa yatsun hannunshi na dama, kana yana ɗan karkaɗa ƙafafunshi dake miƙe bisa table ɗin dake gabanshi a hankali a hankali. idonshi ya rumtse da ƙarfi jin Mama na cewa. "Wallahi-Wallahi bazan taɓa yarda a zalumunci Zaleeha irin yadda aka zalumci Maryam ba, akan wani dalili zai sa baza'a sakarmin rayuwar yarana ba, suma su auri wanda sukeso sai ayi ta musu cushe da auren dole ina dalili? to Wallahi muddin ina raye, Wallahi bazan taɓa lamunta Zaleeha ta zauna da wannan banzan nakasasshen kurma kuma gurgun, da kuka yayibo zaku liƙa mata ku kashe mata rayuwa ba, haka kawai dan an iya min kisan mummuƙe, shine za'a nunamin wariyar launin fata, a nuna min ni bare ce to Wallahi ban amince ba!." Cikin gajiya da ihu da hayagagar da take musu Ya Ahmad ya ɗan tanƙwashe sawunshi tare da cewa. "Mama ai Zaleeha ita ta kawo shi, zaɓinta ne ita ta amince dashi babu wanda ya mata dole, itace ta amince tasa ya turo iyayenshi." Cikin tsawa tace. "Rufe min baki, kaima ae munafuki ne, ban nemi jin ta bakinka ba, da ubanka nake magana, karka wani karkace kace zaka meda laifin kan Zaleeha, munafurcin banza kawai." Rumtse idanu Ya Ahmad yayi, cikin takaicin abinda Mama'n kewa mahaifin nashi yace. "Allah ya huci zuciyarki." A hasale tace. "Wannan karon dai zuciyar tawa ba zata huce ba, Wallahi bazan taɓa lamunta da batun ƴata ta auri musakiba, dan rainin hankalin yarinya da kyawunta da ƙimarta tanada masoya gabas da yamma kudu da arewa amman a rasa wanda za'a zaɓa mata sai nakasasshe, wulaƙantacce wanda ko magana bayaji!." Tafaɗa ranta amatuƙar ɓace domin sosai zuciyarta ke tafasa. Duk ihu da hargowan da takeyi Baba Malam bai sake ɗaga ido ya kalleta ba, sai ma tasbihi da yakeyi ga mahaliccinsa da ya jarabceshi da auran wanna mata mai munanan al'adu. Mamy kuwa wayarta ta jawo kana ta fara karanta Dua Azkar. Ganin haka shima Ahmad sai yasa hannu ya ɗauki ɗan madai-daicin Qur'Ani'n dake gefenshi ya buɗe ya fara karatu ahankali cikin suratul. Kahf kasan cewar yammacin Jummu'a ne. Habu ne ya shigo parlour'n a hankali ya nufi gefen mahaifin nasu ya zauna kusa da ɗan uwan shi Ahmad, ido ya rumtse da ƙarfi yana mai jin takaicin hali irin na mahaifiyar tashi, cikin sanyin sauti yace. "Ya salam! Dan Allah Mama kiyi haƙuri ki bar yin ihun nan, kowa yanayin abinda zai samar mishi lada ke kuma kinzo kina tarawa kanki zunubi kina ɗaga harshenki sama dana mijink..." Da sauri ya haɗiye rogowar maganar tashi, sakamakon jin Maman ta kai mishi wani uban bugu kan bakinshi. "Habu kayi asara Wallahi, kai dai ka banunka da baka da kishin mahaifiyarka!." Takuma faɗa a hasale. Baba Malam ne ya miƙe tsaye, tare da kallon yaran nashi cikin kamala da cikar haiba yace. "Kuyi al'awala mu tafi masalaci lokacin sallah ya gabato." Da sauri suka mimmiƙe tare da cewa. "To." Haka duk sukaje suka sabunta al'wala kana suka tafi zuwa masallaci. Mamy ma tuni tayi side ɗinta, inda ta samu Aunty Lubna a parlour tana sawa ƴarta hijabi alamun zatayi salla ne. "Barka da shigowa Mamy." cikin nitsuwa da mutuntaka Mamy tace. "Barka dai Lubna ya gajiyar kitchen? na tafi na barki ke ɗaya da aiki niƙi niƙi ko." Kai ta rausayar tare da cewa. "Tun ɗazu na gama ai Mamy aikin ba yawa." "Masha Allah! Allah Ya saka da al'khairi, ya baki surkai masu miki fiye da abinda kike min." "Amin Amin" Aunty Lubna ta amsa cikin jin daɗi, kana tayi side ɗin da nanne masauƙinsu duk lokacin da sukazo Gombe dan ita da Mamy tamkar uwa da ƴarta haka suke. Ita kuwa Mama ta cika tayi tam sai ihu da haushi takeyi ita kaɗai kamar karya. "Watoma mahaukaciya suka medani? sun watse sun barni wato inyi ta haushi ni ɗaya ko, tam zanyi maganinku, Wallahi gaba ɗaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148