Chapter 6
Chapter 6
mutanen dake zageye da Nuruddeen suke fad'i, yayinda wasu suka ma kasa mgna sai d'aura hannu sukayi a kai, kana wasu sai jujjuya kai sukeyi. mai mota kuwa da ker ya samu ya fara sarrafa motar har ya samu ta tsaya, yana fitowa da gudu ya nufi inda dandazon mutanen suke, kutsawa yayi tayi tsakiyar mutanen har ya samu ya isa, ido ya rumtse da k'arfi cikin tsananin fargaba ya sunkuyo kan Nuruddeen da yake konce lib bisa titi, ida nunshi a rufe kirib sai numfashin shi dake korar juna, da sauri ya tallaboshi tare dagowa ya kalli mutanen cikin tashin hankali yace. "Ku taimaka min mana in d'agashi in sashi a mota." wani k'ak'k'arfan matashi ne, yayi maza ya sunkuyo ya ciccibi Nuruddeen kana cikin, d'aga murya yace. "Biyoni." yana fad'in haka ya juya ya tsallaka titin zuwa d'aya hannun kana ya nufi cikin asibitin MUSABA dake fuskantar tashan Dukkun, cikin rawan jiki mutumin ya mik'e kana yabi bayanshi. suna shiga Reception suka nufa, ganin sun shigo hajaram majaram yasa Nurse's yin kansu da tambayar meke faruwa, cikin kad'uwa mutumin nan yace, "Accident ne ku taimaka doctor ya dubashi." juyawa sukayi suka kalli juna, kana d'aya daga cikinsu tace. "Ko an gayawa doctor bazai dubashi ba sai an nemo police." jin haka yasa mutumin nan juyawa da sauri ya fita, gudu-gudu sauri-sauri ya tsallaka titin kana ya nufi wurin motar tashi, yana shiga ya nufi Gombe division yana zuwa ya musu bayanin abinda ke faruwa, ba b'ata lokaci suka had'ashi da police d'aya, kana suka tafi tare, suna zuwa Doctor in ya amsheshi bisa sa hannun hukuma kana fara bashi taimakon gaggawa, sannan daga bisani ya ce su tafi Medical Center. Ba b'ata lokaci suka amshi shawararshi suka tafi can, suna zuwa aka amsheshi. shi kuwa police yasa d'aya police d'in yaje ya d'auki machine d'n nashi ya kaishi officensu. kana sun samu wayarshi y'ar Nokia dake jikinshi tanan aka kira Bappa Ali aka sanar mishi meke faruwa. Lokacin da aka gayawa Bappa Ali yana cikin garin kurugu da yake ranar larabace, to yaje cin kasuwa, ana gaya mishi bawan Allah ya bar duk abinda yakeyi ya nufi cikin Gombe kai tsaye Medical Center din ya nufa, inda yana zuwa fargabarshi ta k'aru domin tunda Nuruddeen ya fad'i bai sake bud'e idanunshi ba kuma uwa uba yana konce tamkar gawa komai sai an mishi ga roba a hanci da baki da k'asanshi wannan abu yayi matuk'ar firgitashi, duk da k'arfin zuciya irin na bappa Ali sai da yayi ta kuka, mutumin daya bugi Nuruddeeen ma sai kukan yake sabida kukan da Bappa Ali keyi ya matuk'ar karya mishi zuciya sai hak'uri yake bashi da neman yafiyarsu. Cikin raunin murya yake cewa. "Ku gafar ceni tsautsayine, nayi iya k'ok'arina inga na tsare motata bataje ta bugeshi ba amman ina Allah ya k'addara faruwar hatsarin bani da tsumi ko wayo bare k'arfin hanawa." sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa. "Tunda nake ban tab'a shiga cikin tashan Dukku ba, sai yau, ashe ashe ban saniba masifa ke kirana." shi kuwa Bappa Ali ya gaza cewa komai domin da ganin mutumin ya girmeshi kuma bisa dukkan alamu mutum ne mai daraja da ka ganshi kasan mai kamalane, shi kuwa mutum shirun Bappa Ali sai ya sa mishi rauni yana ganin shike nan ya cucesu, yana bashi hak'uri yana tuno dalilin zuwanshi tashan, dan matarshi da ta kasance yar Ngalda to kullum shi ke kaita to yau kuma har ya shirya zai kaita sai kuma motocin kayanshi suka iso, so shiyasa yace bari ya kaita tasha ta shiga motar kasuwa, to shinefa ya kaita kenan yana fitowa wannan hatsarin ya auku. Bappa Ali kuwa ganin yanata bashi hak'uri ya sashi yin k'arfin halin cewa. "Ba komai Allah ya bashi lfy, ai shi tsautsayi ba ta inda baya wakana." sosai mutumin ya d'anji sanyi kana yace. "Wacce uguwa kuke ne?." cikin sanyi Bappa Ali yace. "Har Dukku muke." da sauri yace. "Ina mamanshi?." kai ya jinjina kana yace. "Mamanshi da babanshi duk basu saniba, suna Dukku ni kuma dama ina Kurugu to da aka kirani sai na taho nand'in. Yanzu in ba matsala in akwai masu kula dashi zan wuce Dukku inje in sanar musu." cikin kad'uwa yace. "To kai waye d'inshi ne?." "Ni bappanshi ne k'anin mahaifinshi kuma mahaifin nashima baida lfy." kai ya jinjina kana ya zaro kud'i a aljihunshi sannan ya mik'a mishi tare da cewa. "Ba matsala zan kula da komai kayi maza kaje ka sanar musu." k'in amsar kud'in yayi, shi kuwa mutumin ya sashi karb'a a dole. Haka dai ya amshi kudin badon ya soba ya tafi, shi kuwa mutumin shida kanshi ya zauna wurin kana ya bada duk abinda ya dace na jinyar Nuruddeen. Shi kuwa bappa Ali daya koma Dukku jiki a mace yayiwa Ummi bayani sai dai ya boye mata hak'ik'anin halin da Seyojinta ke ciki, yace mata da sauk'i sosai baiji ciwoba an dai mishi allurar bacci ne dan ya huta. To shiyasa hankalin ta bai tashi sosaiba, Saifuddeen kuma tun lokacin da Yayan nashi ya tafi sai yaja hannun Hayatuddeen suka tafi gidan Goggo Dada, to shiyasa bappa Ali bai tarar dashi a gidaba, kuma gidan Goggo Dada nada d'an nisa don ita a Shabewa take. Abba kuwa baida lfy ba damar yaje, haka yasa Bappa Ali ya juya shida Adnan babban abokin Nuruddeen d'in, kana sai Rahma. Koda sukaje gaba d'aya hankalinsu ya tashi ganin yadda Nuruddeen ke kwance tamkar gawa Rahma tayi ta kuka tamkar ranta zai fita, Adnan yanata rarrashinta, Bappa Ali kuwa mutumin ne keta rarrashinsa. Ganin dare ya fara nisa yasa Bappa Ali cewa Rahma ta koma dan har takwas na dare yayi, jin haka yasa mutumin nan k'iran d'anshi mai suna Arabi yazo. Kana yace ya maidata Dukku da motar da yazo, ba musu ya d'auki Rahma ya maidata Dukku, yana ajeta ya juyo Gombe. Ita kuwa Rahma jiki a mace ta shiga gida, Ummi dasu Saifuddeen da Abba dasu Raihana suka tasats a gaba da tambayar ya jikin nashi. sanin in ta gaya musu gskyar halin da yake ciki ba mmki jikin Abba ya tashi, Ummi ta k'ara shiga damuwa dan haka sai tai ta ce musu jikifa da sauk'i, koda Ummi ta bata abinci sam ta kasa ci, sai hawaye da take zubdawa time to time, kana tana sa hannu tana goge hawayen dan kar Ummi ko Saifuddeen su gani dan sam ta lura hankalin su a tashe yake. haka dai sukayi ta jimantawa juna kana sukayi shirin bacci da nufin gari na wayewa Ummi da Saifuddeen zasu shirya suje. Rahma kuwa har ta konta Ummi ta kuma biyota d'akinsu tana k'ara tambayar yanayin jikin nashi nanma dai boye mata gskyar tayi. a haka dai suka kwana da fargaba. A can Gombe kuwa k'arfe d'aya dai-dai na dere Nuruddeen yace ga garinku, Allah sarki rai bak'on duniya, bayan likitan ya sanar musu ya cika, Bappa Ali kam sai ya rasa inda zaisa ranshi kawai sai ya shiga d'akin da gawar yake yayi ta zagaya gadon yana wani irin azabebben kuka maicin zuciya da tada hankalin mai sauraro, Adnan kuwa kanshi ya kife gefen kan Nuruddeen yana wani irin sassayan kuka mai zazzafan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148