Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

yaje ya zauna a gefen damanta Hayatuddeen kuma ya zauna gefen hagunta yayinda Faruq ya zauna gabanta, Adda Rahma kuma kan gadon ta hau ta kwanta tare yin mik'a sannan ta bugi k'afad'an Raliya da tuni ta fara bacci yayinda Adam ke bisa ruwan cikinta, a hankali ta bud'e ido, sai ta kuma yunk'ura ta zauna jin Rahma na cemata. "Ke tashi kije ki shiga kada kiyi bacci anan ki d'auki Adam ku tafi tare." Kai ta gyad'a kana ta mik'e ruggume da Adam ta fita ta nufi d'akinsu, tana fita Raihana na shigo musu da abincin. By *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 10* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ Free page _Ga masu buΖ™atar sayan littafin turo katin mtn na 300 kacal ta wannan Number 09097853276. Ko ka/yi transfer ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_ A gaban shi ta ajiye tiren, sannan ta d'an zauna gabanshi kular miyar ta bud'e sannan ta zuba mishi miyar a pilit mai d'an zurfi sai ta kuma bud'e na kulan ta sako mishi malmala biyu duk da tasan da wuya ya cinye d'aya ma, kolban man shanun da Ummi ke mik'a mata ta karb'a bud'e marfin tayi ta tsulala man shanun mai d'an yawa, sannan ta jawo gongonin dakekken yajin borkonsu wanda yakeda ta k'amshi kanamfari da tafarnuwa d'an kad'an, spoon tasa ta d'an motso miyar da yake wadace da kifi banda da busasheshen nama dariko kana ga wadacecciyar gyad'a da saida ya bulbulo mai, robar da ta zubo ruwan wonke hannu ta mik'a mishi, jawo robar yayi ya fara wonke hannunshi. Ita kuwa Raihana wani pilet d'in ta kuma d'auka tasa malmala d'aya kana ta zuba miyar a kan tuwon sannan tasa man shanun tare da tarfa yajin borkonon a kai, sai ta kuma kalli Hayatuddeen daketa yamutsa fuska shida Faruq cikin had'e fuska tace. "Ku tashi kuci abinci." Hayatuddeen ne ya zame ya konta tare da cewa. "Ni wlh bazanci tuwoba na k'oshi." shima Faruq had'e fuska yayi tare da cewa. "Shima bazai ci tuwoba." tura musu pilet d'in tayi tare da cewa. "Kada Allah yasa kuci, cikina ko cikinku hegun yara sai iyayi da son k'arya talaka yace bazaici tuwoba." Ummi dai sai ido ta zuba musu, Rahma kuwa murmushi tayi sanin halin Raihana da gajin hak'uri bata jurar rainin wayo hak'urinta kuma ragaggene, shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi sannan ya jawo hannun Hayatuddeen da Faruq ya gyara musu zama sannan yasa hannu ya gutsuri d'an k'aramin loma tare da dandalo miyar sannan ya mik'awa Faruq wanda shi biyewa Hayatuddeen yake bawai baison tuwon har haka bane, bud'e baki yayi da sauri dan yana matuk'ar jin dad'in yaga Uncle inshi na bashi abinci a baki, murmushi Saifuddeen yayi sannan ya kuma gutsuro loma ya dandali miya ya mik'awa Hayatuddeen dake zuzzumbura baki, a hankali ya bud'e baki ya amsa dan dama muddin Hayatuddeen yaci tuwo tofa sai dai in Saifuddeen ne ya bashi da kanshi, cikin lashe baki Hayatuddeen d'in yace. "Adda Rahma miyar tayi dad'i yaseen kinfi Adda Raihana iya girki." dariya sukayi baki d'aya yayinda tuni Raihana ta hatsala ta kai mishi bugu wanda ya kauce ya rab'a jikin Umminshi, ita kuwa Raihana mik'ewa tayi ta fita ganin Saifuddeen ya sauya fuska, shiko Saifuddeen loma ya kuma gutsura ya d'an dandali miyar da taketa nason man shanu da man kuli yasa a bakinshi, idanu ya lumshe dan jin d'and'anon miyar nasa yawun bakinshi tsinkewa, tabbas yasan yan uwanshi sun iya girki ko dan gada sukayi wurin Umminsu. daga nan yaci gaba da basu abinci, yana basu yanaci, saida sukaci sukayi hanik'an sannan Adda Rahma ta tattare filin, ganin Faruq ya fara hamma yasa Ummi ce musu. "Maza ku hau gado ku kwanta saida safe." da sauri suka hau suka konta tare da yin addu'a, shi kuwa Saifuddeen alama yayiwa Adda Rahma da taje ta kira Bappa Ali, kasan cewar tana ganewa yasa ta juya ta nufi side d'in Bappa Alin. ita kuwa Ummi ta fito da asusun Saifuddeen duka uku dan ya mata alamun ta fitar dasu. Ita kuwa Rahma da sallama ta shiga d'akin Aunty Nina wacce take yiwa Abba nabkin cikin kula ta zauna gefenta tare da karb'an yaron taci gaba da sa mishi kayan sanyin dake gefensu cikin sanyinta tace. "Anty Nina Saifuddeen ke son mgna da Bappa Ali,." mik'ewa tayi tare da cewa. "To bari in gaya mishi." to tace sannan ta fara kiciniyar sawa Abba hula shi kuwa sai zillewa yakeyi. Ita kuwa Aunty Nina tana zuwa turakan Bappa Ali tace. "Malam, Saifuddeen ke son Magna da kai." kai ya jinjina tare da cewa. "To gani nan zuwa." daga nan ta juya taje ta gayawa Rahma da tuni ta gama kimtsa Abba, mik'ewa tayi tare da bata yaron sannan ta fita ta tafi. Tana shiga ba jimawa shima bappa Ali ya shigo da sallamarshi, kan kujera ya zauna yayinda suna fuskantar juna dasu Saifuddeen, pepar da biro Saifuddeen ya matso dashi kana yayiwa Rahma nuni data zauna ta harhad'a kan kudad'en asusun da suka farfasa shida Ummi suka juyesu bisa k'aramin sallayar Hayatuddeen. Gyara zama yayi sannan ya fara rubuta mishi abinda yasa ya kirashi. "Bappa Ali kar dai har kayi bacci na tasheka?." kai ya jujjuya tare da cewa. "A a banyi bacciba Saifuddeen dama nima inason mu tattauna." murmushi yayi tare da rubuta mishi. "To dama tun last two weeks nace ma maggi yayi tsada ko yayi ma fiye da yadda aka zata, to shine nake son in sanar maka muyi shawarar yadda zamu saida, sai kuma batun ribar ledodin da nike saidawa ina sawa a asusu to shine wannan yanzu muka fasa asusun." ita dai Ummi tana saurarinsu yayinda ita kuwa Rahma taketa had'a kud'ad'en in ta had'a dubu tara sai tayi musu d'amara da cikon na goma kana sai ta ajiyesu. Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace. "Eh lallai farashin Maggi ya k'aru sosai, ga kuma na kayan abinci ma ya k'aru matuk'a buhunan wake da na saya kan dubu 12 yanzu ya zama 30k ake saidashi, masara dubu 8 na sassaresu gashi yanzu sun koma dubu 15 , Kalwa na sayeshi buhu dubu tara-tara to gashi yanzu buhu dubu ashirin da biyar, gero na sayeshi buhu dubu bakwai yanzu ya koma buhu dubu sha hud'u. Gaba d'aya kayan abinci sun tsefe sunyi tsananin tsada talaka na fama da yunwa manoma sun saidashi tun yana araha gashi yanzu zasu dawo suna sayanshi da tsada kuma a yanzun suke fama da noma damuna tayi zurfi sama ruwa k'asa ruwa, to dama na ajiyeshi ne kan haka yanzu zamu san yadda zamuyi mu sakeshi da araha yadda talaka zai samu sauk'in saya." cikin jin dad'i Ummi tace. "Madallah da mai zuciyar imani inama ace duk masu dama da kud'i suna haka to tabbas da masu sayanshi dan muguntar sai yayi tsada su fiddashi da sun bari." shima Saifuddeen murmushi yayi cikin jin dad'in yanaga zasu samu damar taimakawa marasa k'arfi ya rubuta musu. "Yauwa Bappa Ali wannan abu yayi kyau, Magging ma dole zamu sake fara shinsa dan talaka ya samu yadda zaiyi." jinjina kai bappa Alin yayi tare da cewa. "Yauwa to muga ya lissafin zaiyi, kaga lokacin dana sai wake ana saida mudun akan

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148