Skip to content

Chapter 146

Chapter 146

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ta dinga sake zafafan waƙoƙi na soyayya masu taɓa zuciya, wani waƙan idan tasaka har ƙwalla ne ke bin ƙuncinta, domin sosai suke ratsa mata zuciya. kai ta jinjina tare dacewa. "Ganin lokaci na hararanmu a gurguje ga zazzafan sak'o na masoyo, wanda shine na kusa da k'arshe. sai kuma ta saki wak'ar K'anina Hamisu Breaker tare da k'ara volume. A hankali Wak'ar ke tashi. Tun forkona duniya an dasa so bisa zuciyar mutun biyu. kuma har abadan bazai yankeba dan yanada armashi. sai ta kuma d'an rage volume d'in tare da d'aga muryarta tana bin wakar yadda sautin ke fitowa tare cikin rauni take bin baitukan. "Soyyyy ruwan zuma inji wasu, wasuko sukace ruwan gubane." haka tai tabin wak'ar har k'arshe kana tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa. "Ganin lokacin da aka d'ibar mana ya k'are ga wak'armu ta k'arshe." wak'ar isa ayagi. Duk masoyi zai jure karan tsan." sai kuma ta d'an k'ara sautin muryarta tare da bin mawak'in inda yake cewa. "Zaya jure kai kawo ko ina, zai nufin masoyinsa da hassada. Ba'ason fushi sai dai dangana." sai kuma ta dai-daita muryarta da mawak'in suka had'a baki wurin cewa. "Yin fushi a so tono fittina, wanda ya fara so baishiga yak'i na kanganba." sai kuma tayi maza ta katse wak'ar dan sai taji kamar Saifuddeen take bawa k'arfin guiwa, tana ƙare shirin nata ta fito. Balkeesu ce ta karɓa don itace zata gudanar da labaran duniya, bayan tagama gabatar da labaranne ta gyara zama, cikin isgilanci tace. "Kanun Labaran duniya da ɗumi ɗuminsu.mun samu wani labarin mai cike da al'ajabi daga wata majiyarmu mai taken Babu nakasasshe sai rago, cewa soyayya ta ɓarke tsakanin masu lafiya da kuma nakasassu, inda shahararriyar matashiyar budurwa maiji da kyau, ilimi, wayewa, haɗi da aji tayi gamdakatar da wani nakasashshen kurma, kana gurgu, inda yazo ya bayyana mata soyayyarsa hartakai ga suna ƙoƙarin yin aure, mudai fatan mu anan shine Allah yaƙara danƙon ƙauna da soyayya, domin ai Nasaka ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai kasasshe!." taƙare maganar tana me ƙoƙarin gimtse dariyarta. Zaleeha dake zaune aɗakin watsa shirye shirye tanajin abun da Balkeesun ta faɗa, taji ranta yayi wani irin ƙuna, take ɓacin rai ya cika mata zuciya, sam bata tsammaci haka daga Balkeesu ba abinda taketa boye shine take son sanarwa duniya. Jakarta ta ɗauka tare da miƙewa tsaye batajin zata iya jure zama awajen aikin, saboda haka tafiyarta gida shine kawai zaifi. Tana fitowa, tayi kiciɓus da Balkeesu, tare da wani Hamza wanda yake shima abokin aikinsu ne, Hamza irin mutanen nanne masu gulman tsiya da kuma shishshigi, gason shiga abun dabai shafesa ba, shiyasa ma sam basa shiri da Zaleeha. Yana ganin Zaleehan yasaki dariya tare da dubanta da kyau, cikin son ƙarin jin gulma don wanda Balkeesu ta gulmata masa bai ishesa ba yace. "Zalees fashion amaryar nakasasu, anguji masu lafiya an ƙare a nakasassu." Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa ta watsa masa wata uwar harara, bata da lokacin tanka masa hakan yasa ta juya taci gaba da tafiyarta. Dariya suka ci gaba dayi shida Balkeesu, ita kuwa ko sake waiwayosu batayi ba. Kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana shiga ta murza wa motar key tare da cillata kan titi, kanta ne ke mata ciwo sosai, gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, har wani ɗaci takeji aranta. Baba malam ne zaune a falonshi bayan tafiyan iyayen Abdussalam wai sun kawo sadakinsu wa Zaleeha kuma wai masu kawo kayan aurenma suna kan hanya, Malam Adam ne ke tausarsa da cewa. "Malam Bashir ka kwantar da hankalinka domin al'amarin yaran yanzu sai du'a'i." cikin tsananin b'acin rai da tarin bak'in ciki murya a hargitee Baba Malam yace. "Me Zaleeha take son maidani da zatayi ta turomin manyan mutane masu daraja a kanta ita d'aya, da kaifa muka amshi sadakin Saifuddeen a hannun mutane masu kima da daraja, sannan yanzu ta kuma turo min wasu, biyu za'a rabata ne? ga uwarta ita ma sai tayar min da hankali takeyi." cikin tausasawa Malam Adam yace. "Kada ka damu tunda su iyayen Abdussalam mun basu hak'uri mun kuma ce musu kada su bari a kawo kayan lefensu ai inaga sun fahimcemu." kai ya jujjuya tare da cewa. "Banga alamun hakaba a fuskokinsu, bakaji cewa suke ai dai da fari nine na bawa d'ansu damar zuwa zance wurinta, kanaji har cewa sukeyi wai in dai daure inyi dottaku kaji fa abinda Zaleeha ta jaza min zubewar mutunci da kima da dottaku a idanun mutane." "Ba komai in sha Allah, bari inje gida anjima zan dawo inyi mgna da ita Zaleeha ka kwantar da hankalinka." Da haka Malam Adam ya sallami Baba Malam ya tafi ya barshi cikin tarin bak'in cikin abinda Zaleeha da Mama keyi mishi... Ita kuwa Zaleeha kaitsaye ta fara zuwa Makay ice cream and chocolate ta saya, daganan ta ɗauki hanyar komawa gida. Tun daga shawo kwananta ta hango wata ƙatuwar mota tirela fake aƙofar gidansu sai ya Habu dake kusa da masu motar alamun suna mgna dashi kamar dai umarni yake basu kan su dena fidda kayan bisa dukkan alamu jagoranci ko kwatancen wani wuri yake musu inda zasu kai kayan. Abakin tangamemen gate ɗin gidannasu tayi parking, buɗe murfin motar nata tayi ta fito nan tashiga bin kayayyakin furnitures ɗin da ake shigarwa cikin gidannasu da kallo, mamakine bayyane akan fuskarta haka ta wuce zuwa cikin gidan. Kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, nan ta iske su Zahira da Ziyada zaune gefensu kuwa Mamyne hannunta riƙe da littafin hisnul muslim. Wurga jakanta tayi kan kujera cikin gajiya ta dubi Mamy ashagwaɓe tace. "Barka da gida Mamy." Dubanta Mamy tayi tare da cewa. "Yauwa Zaleeha ya aikin." "Alhamdulillah". tafaɗa tana me ƙoƙarin buɗe ledar ice cream ɗinta, zaro roban ice cream ɗin tayi tare da buɗewa, harta sanya ɗan ƙaramin cokali cikin ice cream ɗin sai kuma ta ɗago kanta duban Mamy tayi cikin son ƙarin bayani tace. "Mamy naga anata shigo da kayan furnitures gidannan, Baba ne zai sanja kayan part ɗinsa ko?" ta k'arishe maganar tare da cika bakinta da daddad'an sassanyan ice cream d'in Kafun Mamy tayi magana tuni Zahira tayi carab ta cabke maganan inda tace. "Kayan furnitures ɗinki ne na aure wanda Ya Ahmad yayi miki order daga Dubai shine suka iso." Tuni ta ƙware da ice cream ɗin dake cikin bakinta, wani irin tari me ƙarfi ne ya sarƙafemata wuya da numfashi, take idanunta sukayi jajur, tari take sosai, har saida su Mamy suka tsorata, Ziyada ne tatafi kitchine da gudu inda ta dawo hannunta ɗauke da bootle water, Mamy ne ta karɓi ruwan tare da ɓalle murfin goran ta kai bakin Zaleehan, sosai tasha ruwan, saida taji ta rin nata ya tsaya sannan ta kawar da goran daga bakinta, zamowa ƙasa tayi daga kan kujeran tare da fashewa da wani irin kuka, kuka take sosai kamar wacce aka faɗawa ranan mutuwarta, Mamy da su Zahira baki kawai suka sake suna kallonta. Cikin kuka ta mirgino tare da kama ƙafafun Mamy, cikin matsanancin kuka tace. "Mamy dan Allah Kifaɗawa Baba Malam cewa banason wannan auren, wallahi na tsaneshi, matuƙar aka aura mini shi kashe kaina zanyi, wallahi dana aureshi na gwammace mutuwata!" Ajiyar zuciya

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148