Chapter 129
Chapter 129
ya nufi wurin mai gadin, hannu ya bashi suka gaisa sannan yace mishi ya shiga cikin gida yace bak'in sun iso. Cikin mutuntawa mai gadin yace to tare da juyawa ya shiga cikin gidan. Jim kaɗan ya fito yace. Ance su isa. Nan duk matan suka shiga su kuma mazan duk suka zauna cikin motocin. Suna shiga cikin gidan Maryam tayi musu jagora har babban parlour Mama duk da bata nan dole a bata matsayinta na uwa. Bayan sun zazzauna, an gaisa cikin mutun taka, an kawo musu drinks da snacks, sun ɗan taɓa abin sha. Hajia Rabi ce ta gyara zama tare da cewa. "Raliya je kice Imran Suleiman da Hayatudeen su shigo da kayan." A hankali ta mik'e tare da cewa. "To." A tare suka shigo duk suna riƙe da akwatuna harda ma'aikatan gidan, haka suka dinga shigowa da haɗaɗɗun akwatunan cikin falon, saida suka ƙare sannan suka juya suka fiti suna haki, dan sosai akwatunan suke da nauyi kasancewar kowanne ashaƙe yake da kaya. Aunty Kubra ce ta kalli Raliya dake riƙe da ɗan Maryam tana mishi wasa, tace. "Ke ƙanwar ango ai bakici ta zama tashi ki nuna musu kayan." murmushi tayi tare da cewa. "To Aunty Kubra amman dai a tayani." Murmushi sukayi baki ɗaya ganin yadda taketa kiciniyar bubbude akwatunan, tare da cewa. "Wannan turamene a ciki wannan laces, wannan shadda wanna boyel." sai kuma ta fara jawo na ƙananun kaya dana kayan shafa wanda ta buɗe akwatuna biyu wanda suke cike maƙil da ababen shafawa na kwalliyar jiki irin na mata. Da sauri Mommy matar Malam Adam tace. "Masha Allah. Gsky ki huta kawai, wannan ai yafi ƙarfinki muma masu gani har mun gaji, wani abun ai bazai ganuba, sai dai muce Allah ya sanya al'khairi yasa al'barka a ciki." Aunty Lubna kuwa kai kawai take jinjinawa domin idonta ya raina fata, nakasasshen da ake zatawa riƙe ƙoƙon bara da bin kwararo lungu da saƙo yana allazi wahidin, shine da wannan kayan lefe wanda ita dai a iya ganinta lefen Zahra buhari ne kawai ta taɓa gani wanda zatace yafi wannan, a dai gani da idonta. Goggo Maryama kuwa tausayi suka bata ganin irin ruwan dukiya da suka binne a kan yarinyar da ta sani tabbas uwarta bazata barta ta zauna a gidan Saifuddeen ba. Mamy ma tabbas tausayinsu taji ganin yadda sukayi ɓarin naira. Maryam kuwa sai addu'a takeyi a ranta tana cewa. "Ya Allah ka rufa mana asiri, ka hana mahaifinmu jin kunya da tozarta, ya Allah ka tausasa mana zuciyar wannan baiwar taka Zaleeha kasa tayiwa mahaifinmu biyayya ta zauna lfy da mijinta da yan uwanshi." sosai Maryam ke jin tsoron abinda zai zubarwa mahaifinsu darajarsa da mutuncinsa. Adda Rahamace ta ɗanyi dariya kana ta jawo ɗan kit ɗin da saraƙuna suke ciki, ta buɗe babban gwal ɗin da Saifuddeen ya saya a India ta zaro ta miƙawa Mommy dake kusa da ita cikin sanyi tace. "To ga wannan ko za'a adanashi da ban, duk da cewa sauran ma gwala gwalaine amma shi tsadansa dabanne." sosai Mommy ta girgiza da girma da darajan gwal ɗin, mai surki da ruwan farin zinari. amsa tayi tare da miƙawa Mamy, mamakinsu ya ƙaru ne lokacin da Aunty Kubra ta miƙawa Aunty Lubna car key ɗin kia d'innan tare da cewa. "Ga wannan Key d'in motar amaryarmun ce, motar tana nan waje. zuwa yanzu fa Mamy abin ya fara zarta zatonta cikin dattaku da nitsuwarta da iliminta tace. "Anya kuwa, gsky Malam zaiyi faɗa in muka karɓi abubuwan nan, ko lefen ma in ya gani zaiyi faɗa." Da sauri Goggo Dada da Aunty Kubra sukace. "Dan Allah da manzonsa kar muyi haka daku, Saifuddeen bazaiji daɗiba tunda shi ya gani zai iya yiwa matarsa komai, kuma abinda nanda wani ɗan lokaci ta zama matarsa." Murmushi Aunty Lubna tayi tare da cewa. "Kuma shi za'ayiwa kolliyar ba." Ta ƙarishe mgnar tana kallon Aunty Kubra wacce bazata wuce sa'arta ba. da sauri Aunty Kubra tace. "Ato kunga ai kanshi yayiwa tanadi, mutun da matarsa." Goggo Maryama ne tace. "To mu dai tunda kunce dan Allah da manzonsa to zamu amshi kayan, saura mgna kuma tana wurin Yaya Malam." Hajia Rabi ce tace. "Shima anjima da dare za'a kawo sadaki fatanmu Allah yasa, a saka bikin nanda mako ɗaya." Amin Amin sukace baki ɗaya. Maryam ce tace. "ai kam naga alaman Saifuddeen ya zaƙu yana son matarsa nan kusa tunda gashi harda kayan rufi kuka kawo." Cikin sakin fuska Adda Rahma tace. "Sosai makuwa ,ai shi ko yau ya sameta yana so." Daga nan suka ɗan taɓa hira sannan suma miƙe tare da cewa. "To mu zamu tafi sai kuma in munzo ɗaukan amaryarmu." Da sauri Mommy ta kalli Maryam da Lubna ta musu alamun su ɗauko food flasks ɗin dake cike da ababen mƙulashe. Ganin sunata cika musu kulolin a gabansu yasa, Goggo Dada cewa. "wannan abu yayi yawa ku barshi." da Saudi Goggo Maryama tace. "A a ai yaba kyauta tukuici, ku barmu muma muyi iya iyawarmu." Hajia Rabi ce ta kalli Mommy matar Malam Adam dake miƙa mata damin kuɗin tukuicinsu rafa guda shida yan dubu daddaya. A hankali tace. "Hajia wannan kuɗin kuma na menene duka?." Cikin salon girma ba batun ƙaramta Mommy tace. "Yaba kyauta tukuici, ba ku muka bawa ba yaran da suka shigo da kayan muka bawa." Akan dole su,suka karɓa, nan Aunty Lubna taƙira biyu daga cikin masu aikin gidan Baba Malam ɗin suka shiga jidan food flask ɗin suna kaiwa cikin motocin da su Adda Rahama suka zo dashi. Har bakin gate suka rakosu baki d'ayan su, aka rabu cikin mutunci da jin dadi. Bayan sun koma cikin gida ne, Aunty Lubna ta kalli Maryam tare da cewa. "Ke zo muga kayannan da kyau,". Dariya Maryam tayi kana ta matso ta fara bubbud'e akwatunan, Mommy, Mamy, goggo Dada kuwa suma zama sukayi suna kallon kayan d'aya bayan d'aya. yayinda tuni Aunty Lubna keta viewing tana d'aukan komai a zazzafar wayarta. Sune basu gama ba har aka kira sallan magrib, dole suka hak'ura suka k'arisa kallon a gaggauce kana suka rufe komai, suka shirgeshi a cikin d'akin Mama, kana duk sukayi al'wala dan gabatar da salla. Bayan sunyi sallah harda na isha, sukaci abinci, sukaci gaba da hira, dan Maryam jira take mijinta ne zaizo ya d'auketa hakama Mommy Malam Adam ne zaizo ya d'auketa, Goggo Maryama kuwa Ya Ahmad ne zai maidata gida. Baba Malam kuwa, tunda yamma yake gidan Malam Adam, dan amaryarshi bata zoba. Ya Ahmad kuwa da Ya Aminu tunda safe suka tafi dukku kai ziyara dan Ya Ahmad ya kusa komawa Abuja. Saida akayi sallan magriba suka dawo, Kai tsaye parlour'n Baba Malam suka nufa, nan Maryam ta kawo musu abinci, bayan sun gama cine sukayi al'wala suka nufi masallaci a nan suka samu Baba malam da Malam Adam. Koda aka idar da salla tare suka shigo cikin gida. Suna shiga bada dad'ewa ba, Dirankadi da Bappa Ali da Malam Ashiru suka iso harabar gidan. Dirankadi ne ya kira Baba malam ya shaida masa isowarsu, jin haka ya kalli Ahmad tare da cewa. "Ahmad tashi kaje ka shigo da iyayen Saifuddeen." Cikin tsananin girmamawa da sanin darajar mahaifa Ahmad yace. "To." sannan ya miƙe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148