Chapter 116
Chapter 116
tab'a yarda yanada matsalar spinal cord injury ba. mik'awa Baffa Ali wayar yayi, tare da maida hawayen tausayin Saifuddeen da suka cika masa idanu, kana a hankali yace. "Shin zai iya aure har ya iya kusantar mace har in Allah ya nufa su samu haihuwa!?." Wani sassanyar ajiyar zuciya Baffa Ali yayi kana ya, musu duk cikekken bayanan da doctors sukayi musu ya k'ara da cewa. "Likitoci sun bamu tabbacin cewa zai iya aure harma da haihuwa, domin nakasarsa bata shafi jijiyoyin mazantakarsa ba. Kuma ko jiya da sukaje suka sameni da batun saida na kuma tambayarshi batun lafiyarshi. Ya bani tabbacin shifa baida matsala ko kad'an." Jin haka yasa Baba malam yin murmushi tare da cewa. "Alhamdulillahi, na bawa Saifuddeen dama yazo ya gabatar da kanshi a wurin Zaleeha, in dai tayi mishi to in sha Allah Zan bashi ita." Wani matsainacin farin cikine ya rufesu baki d'aya, Aminu da Ahmad ma sun aminta da Saifuddeen, domin suma ai basu san k'arshensu ba. Malam Adam ne ya gyara zama tare da cewa. "An bashi dama yazo ya gabatar da kanshi, fatanmu Allah ya dai-dai-ta tsakaninsu." "Amin Amin." Sukace baki d'aya kana, daga nan suka ɗan taɓa hira, daga bisani su Baffa Ali suka mik'e da niyar tafiya, Har bakin gate wurin motocinsu, Baba malam da abokinshi Malam Adam dasu Aminu sukayi musu rakiya. Kai tsaye gidansu Saifuddeen suka nufa, Wanda yake zaune a falon side ɗinshi shida Ahmad da kuma ishaq, hira suke amman gaba ɗaya hankalinshi baya kansu, duk tunaninshi naga su Baffa Ali, tsoro yakeji kar suje ace musu anyi mata miji. Ahmad ne ya kalleshi tare da cewa. "Wai mene sai kayi wani shiru, in ma an bada ita, ai akwai wasu matan." Hararanshi yayi tare da girgiza mishi kai, kana ya mishi alaman "Itace muradin zuciyarshi, kuma abincin ruhinshi." mik'ewa Ahmad yayi cikin yin dariya kana yace. "To nama jiyo muryar Baffa Ali a parlour ku taho muje muji dame suka dawo." Kusan a tare suka fito, yayinda Saifuddeen yaketa musu kallon nazartar fuskokinsu. Murmushi yayi ganin Dirankadi na cewa Ummi. "Alhamdulillahi tafiya tayi kyau, abuma duk namune." wani irin sassanyan ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa. "Gidan mutunci ne ko?." Da sauri baffa Ali yace. "D'iyar Bashiru nefa d'an abokin babanmu, kin tuna malamin su Saifuddeen na islamiya?." Da sauri Ummi tace. "La Bashir kam ai bazan mantashi ba, lokacin da muke karatu su sunyi sauk'a, kusan sune manyanmu a wurinsu muke biyawa in kawu baya kusa." Cikin dariya malam Ashiru yace. "Ato baki mance mu ba ashe." Kai ta gyad'a cikin jin Kunya dan tuno k'uruciya. Dirankadi ne yace. "To Zaleeha d'iyarshi ce ai?." Ahmad ne yace. "La Zaleehan Malam Bashir ce? D'alibar Saifuddeen lokacin in bashine zai bata haddaba sam bata tab'a iya kawoshi dai-dai." Sai ya kuma juyawa ya kalli Saifuddeen da ya kauda kanshi kamar ba shiba. Baffa Ali ne ya shafa kanshi, tare dayi mishi cikekken bayanin irin tarbar da suka samu, da irin karra masu da akayi, da kuma basu izinin ya fara zuwa zance duk sanda ya shirya. Wani irin tarin farin ciki yakeji a ransa, a fili kuwa sai hannu ya bawa Dirankadi da Malam Ashiru tare da yi musu alamun godiya da jinjina. sosai Ummi ke lura da irin yadda fuskarsa ke cike da farin ciki, Amman kunyarsa ta boye hakan. Sosai sukaji daɗi daga nan Ahmad ya ɗauki su Baffa Ali ya maidasu Dukku, Ishaq kuwa yabi babanshi suka tafi. Bayan duk sun fitane, Saifuddeen ya sarrafa whellchair ɗinshi har zuwa gaban Ummi dake tsaye, yana isa inda take ya ruggumeta cikin farinciki da salama. Murmushi tayi itama tare da tallafo haɓarshi cikin son abinda ɗan nata keso tace. "Allah ya sanya al'khairi a cikin wannan lamarin naka, Allah ya shige maka gaba ya tabbatar maka da ingantaccen farin ciki!!." A saman lips ɗinshi ya amsa da "Amin Amin my Ummi." Sai ya kuma sarrafa whellchair ɗin nashi ya nufi falonsa. Ummi kuwa da sauri ta haura sama, inda Hayatuddeen ya tasa Raliya a gaba ala dole sai ta share mishi d'akinshi. A parlour ta samesu ita tana shara, shi kuwa yanata zuba mata surutu, hannunshi rik'e da pillet d'in kifin margi special yanaci yanata zuba mata zance, kana yana watsar da k'asusuwan a bayan inda ta share. Cikin gajiya tace. "Wlh na gaji Ummi autanki zai samin ciwon baya dana kunne, duk inda na share yana b'atawa kuma ya cikamin kunne da surutu kamar kabari." Baki ya turo gaba tare da cewa. "Ummi wai dan ina bata labarin wata mawaƙiya, Asma'u Ahmad Matawalle ce da take son Hammana kamar ta mutu, ɗazu muka gama waya da ita wai in gaisheki." Cikin mamaki Ummi tace. "Mawaƙiya kuma?." "Eh" Yace yana lumshe ido tare da kurb'ar juice d'in dake hannunshi. Kauda zancen Ummi tayi da cewa. "Su Baffanku sun dawo harma sun koma." Cikin tsalle Hayatuddeen ya diro daga kan firijin da yake zaune tare da wurga kwalin juice d'in yace. "An bawa Hamma na ita ko yaushe ne auren?." Cikin dariya Ummi tace . "Oh ya Allah ka kimtsa min autana ya zama nitsastse kamar Saifuddeen." Jin Raliya na cewa. "Ummi an bashi izini zuwa zancen?." Cikin gyad'a kai tace. "Eh an bashi sosaima suka samu karramawa, d'iyar Malaminshi nefa Malam bashir, wanda kuma yake shirin Hanyar tsira na gidan radion vission FM." Tsalle Hayatuddeen ya kumayi tare da cewa. "Yanzu kuwa zan tafi gidan Adda Rahma inje musha hira." Kafinma su ankara tuni ya fice abinsa. Nan Raliya ta samu daman gyara mishi ɗakin nashi. Ummi kuwa falonta ta dawo ta zauna taci gaba da karatun da takeyi. Shi kuwa Saifuddeen dake zaune akan lumtsuma -lumtsuman sofan dake falonshi, gyara zamansa yeyi. Wayarshi ne a hannunshi da alamu hira yakeyi da ishaq. "Kai yaro kaji dai ko mun samu karɓuwa. Yanzu yaushe zamuje ne dan gabatar da kanmu?." Cikin tsokana Ishaq yace. "Sai next week ko?." Da sauri ya rubuta mishi. "Kayi hauka ne, ai zuciyata zata narke kafin nan." Dariya sosai Ishaq yayi kana yace. "To yaushe zamuje?." Cikin gyara zamanshi yace. "Anjima da yamma zamuje, kafin nan Ahmad ya dawo." Dariya Ishaq ya kumayi kana yace. "A a sarkin sauri, gsky ka bari sai gobe da yamma. Dan yau zata gabatar da program ɗinta na mushaƙata." Badan ya soba sai don dole haka ya haƙura. 6:00 pm. Zaleeha ce ke cikin ɗakin watsa shirye-shiryen su. Zamanta ta gyara bisa kujerar da take kai, tare da ɗan rage sautin waƙar da tasa, kana cikin irin muryarsu na ma'aikatan gidajen radio tace. "Assalamu alaikum, al'ummar jihar gombe da kewaye, barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirin Mushaƙata, tare dani Zaleeha Bashir Sulaiman Dukku." Sai kuma ta ɗan dakata tare da ƙara sautin waƙar nan ta. Nura M Inuwa mai taken. "Kaso a soka yafi ƙawance cika taso a soka kanaso." sai kuma ta ɗan range sautin tana mai bin waƙar, yadda ake iyajin muryarta dana mawaƙan na tafiya atare. Raveel dake ɗakin kula da shirin dake fita, dariya yayi domin yasan dashi da manager akeyi. Ita kuwa Zaleeha tuni shauƙin sonshi ya rufeta, saboda zafafan waƙoƙin so da take sakawa. Cikin shauƙi ta katse wata waƙan Nura M Inuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148