Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

yayi mata alama dataja motar ta gudu, gane abinda yake nufine yasa ta jujjuya kai tare da zubda hawaye cikin haki tace. "Mutafi zasu kasheka fa 'yan kalarene fa yaranshi ne." ganin zata b'ata lokaci har suzo su sameta suyi mata illane yasashi buga marfin motar da k'arfi tare dayi mata gurnani irin nasu na kurame wanda in bawai ka saniba sai kayi zaton tsawa ya buga mata hakance ta kasance ga Zaleeha dan jin sautinshi tayi a sama haka yasa ta figi motarta a guje, tana jan motar suna isowa inda yake, yayinda shi kuwa yake kallonta so yake yaga fitanta a wurin, su kuwa suna isa inda yake ba tare da ya juyoba don shi dai kurmane bazaiji sautin takun k'afafunsu ba, suna isa d'aya daga cikinsu ya narka mishi k'aton katakon dake hannunshi a tsakiyar gadon bayanshi kafin, yayi wani yunk'urinma d'aya daga cikinsune ya dab'a mishi wuk'a a tsakiyar bayanshi kana ya zaro wuk'ar wanda tuni sun farka mishi rigarshi wani irin razanennen ihu Zaleeha tasaka tare da zubawa bayanshi ido sabida tana ganinshi ras dan hasken motoci dake haska wurin da hasken fitulun dake zagaye da farfajiyar wurin cikin tsananin tsoro da firgici taja motarta ta bar sitadiyon d'in, tana fita kai tsaye gombe division ta nufa. Shi kuwa Saifuddin tuni sun mishi illa sun daddatsa mishi kataki a tsakiyan bayanshi. yayinda duk da haka bai bar kare kanshiba sai dai ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi gashi sun zomishi ta bayanshi kuma sunzo tare da makamai yayinda shi kuwa babu ko allura a jikinshi, haka yasa sukayi mishi illah mafi muni a jikin d'an adam, haka suka rink'a hankad'ashi kan k'arafun wurin suna buga bayanshi a kai saida sukaga yabar motsi kana suka dauki uban gidansu da Saifuddeen ya daddaga mishi jelershi sukaja motocinsu suka tafi, yayinda tuni mazauna wurin kuwa sun watse don kowa yasan rashin mutuncin Dalla. Shiru cikin sitadiyon d'in ba ko tsuntsu sai Saifuddin dake yashe tamkar mamaci,. Ita kuwa Zaleeha bayan ta sanarwa hukuma, ganin ita macece kuma sananniya kana yar babban Malamin da akeji dashi a fad'in jihar dama k'asar bak'i d'aya yasa aka had'ata da police officer d'aya ya rakata gidansu dake New G.R.A... A haka police officers na station d'in gombe division suka iso, yayinda aka had'a da sosojin Anty kalare, kana suna isowa ganin halin da yake ciki ne yasa suka d'aukeshi, kai tsaye general hospital Gombe suka nufa dashi, kai tsaye aka wuce dashi o,p,d. suna isa ma aikatan wannan sashin suka turo irin yan wannan gadaje na d'aukar marasa lfy, tare dasa hannun hukuma aka karb'eshi bayan an duddubashi ganin aikin babbane ya kuma ji rauni sosai ne sai aka basu takarda wacce zata sadasu da babban likitan dake Medical Center. Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon Saifuddin ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o, text ne aka turo kamar haka. ```"Babana Saifuddin Kana ina? ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."``` shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa. "Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan." sai kuma ga wani sak'on da yaga suna no daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa. ```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."``` haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi, dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe, kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace. "Saifuddeen!." sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu, mazuk'in numfashin suka manna mishi, kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi. Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba. Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta, amman abin yaci tura, sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu, shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su. Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa, canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu, bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa. Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi, sai ya kuma mik'ewa da sauri kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen. cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa. "Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy." sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi, dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu, da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro, cikin kad'uwa yace. "Doctor Adnan meke faruwa?." kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace. "Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne." cikin firgici Arabi yace. "Innalillahi Saifuddeen! to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana." cikin kad'uwa police d'in yace. "Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi." cikin rauni Arabi yace. "officer kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?." cikin kauda kai officer d'in yace. "Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane, domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya, itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto, to ganin a firgice take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu." cikin

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148