Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

gayawa Ishaq shi kuma zai gayawa Babansu, da Babban yayansu Barrister Rabi'u dan yasa mishi hannu a cikin lamarin ya tsaya mishi a matsayin lawyer inshi. Ya kuma sanar musu cewar suma su Alhaji Kaburu sunce sai sunga iyayenshi sunji inda ya samu kud'in kafin su amince da batunshi. Gyara zama Bappa Ali yayi tare da fuskarshi kana cikin sauk'e numfashi yace. "To inaga dai mu barshi ya gwada mu gani, domin bahaushe yace matsoraci bashi zama gwani ko shi wanene, mu bada yak'ini a kanshi tunda munada makama kuma ba da ka za'ayi abinba kamar yadda abokinshi ishaq ya bada shawara hakan za'ayi, dan su kansu sun tsorita da batun yadda yace yanada kud'in shiyasa sukace sai sunga iyayenshi kinga alamun gsky kenan domin da 'yan damfarane ce mishi zasuyi kada ya gayawa kowa har uwa da uba in yana dasu kada ya gaya musu, in kin amince ni dai na amince na kuma gamsu da kasuwancin." Ya k'arishe mgnar yana kallon Ummi da Rahma jinjina kai Ummi tayi tare da cewa. "Ba matsala Allah ya bashi sa'a ya sanya al'khairi da al'barka a cikin lamarin ni na amince." sosai Saifuddeen yaji dad'in amincewarsu domin suna bada dukkan yardansu a kanshi tamkar bashida nakasar komai, shi kuwa Bappa Ali cikin nitsuwa yaci gaba da cewa. "Zan je in samu Malam Ashiru abokin ya Bello, in mishi bayanin komai sannan muje gomben mu samu Babansu Ishaq da shi barrister Rabi'un sannan muje wurinsu Alhaji Kabirun sai mu tattauna duk abinda ya dace." cikin nitsuwa Rahma tace. "Hakan yayi Allah ya shige mana gaba." Amin Amin sukace baki d'aya sannan suka tashi daga taron nasu. Washe gari tun da asuba bayan an fito masallaci Bappa Ali yasa Salisu ya kaishi gidan Malam Ashiru bayan sun gaisa ya mishi bayanin abinda ke tafe dashi kan batun Saifuddeen, sosai suka tattauna a kai nan suka tsaida cewar gobe zasuje su samu su Alhaji Kabirun. Salisu na dawowa suka d'auki hanyar gombe suna isa Saifuddeen ya rarraba ledanshi kana yaje shagonsu Alhaji Kabiru ya shaida mishi cewa gobe iyayenshi zasu zo cikin mutuntaka alhaji Kabirun yace to sai sun zo d'in. Daga nan Saifuddeen ya wuce gidansu Ishaq yana shiga yayi kicibis dashi da a tsakar gidan, a tare suka shiga parlour Babansu nan ya samu Ya Rabi'u ya iso, bayan sun gaisane suka tattauna lamarin nan ya sanar musu gobe ma su Bappa Ali zasu zo sundai ajiye zance sai goben. Washe gari kuwa koda su Bappa Ali da Baba Ashiru suka taho da babban yayansu Samisu yariman Dukku kenan kai tsaye gidansu ishaq suka wuce. sosai suka samu tarba ta mutuntaka, suka gaggaisa sannan sukayiwa juna k'arin bayani, daga bisani suka sa ishaq yayiwa Saifuddeen text cewa sun isofa a ina zasu had'u dasu Alhaji Kabirun. Yana ganin text d'in ya wuce shagon Alhaji Kabiru d'in ya gaya mishi cewar sun isofa, cikin kula ya mik'e tare da cewa. "To muje can gidansu abokin naka sai muyi musu jagora zuwa can gidan Alhaji Sanin." cikin jin dad'in haka Saifuddeen ya gyad'a mishi kai sannan ya juya yabi bayan Alhaji Kabirun, motarshi suka shiga kai tsaye suka isa gidansu ishaq sosai Alhaji Kabiru yayi mamaki ganin manyan mutane dan barrister Rabi'u sanannene hakama mahaifinshi baraden Gombe, ga kuma Yariman dukku ga kuma Malam Ashiru da Bappa Ali wanda da ka gansu kaga kamala irin ta malaman addinin musulumci. bayan sun gaggaisa ne kuma suka mimmk'e suka nufi gidan Alhaji Sani wanda tuni Alhaji Kabiru ya mishi bayanin zuwansu a waya. G.R.A suka nufa inda nanne anguwar gidan Alhaji Sanin yake, suna isa mai gadi ya bud'e musu gate ganin tsaleliyar motar ya Rabi'u a gaba wanda Saifuddeen da Ishaq ke ciki a baya Yariman Dukku kuma yana gaba kusa da Barrister Rabi'un, sai kuma motar Alhaji Kabiru wacce Malam Ashiru da Babba Ali ke ciki Babansu Ishaq kuma na gaba kusa da Alhaji Kabirun, suna shiga harabar gidan sukayi parking, suna firfitowa wanni d'an matashi wanda zai kai sa'an su Hayatuddeen ya iso gabansu cikin nitsuwa ya gaidasu, kana ya kalli Alhaji Kabiru tare da cewa. "Abba ku shigo ciki inji Daddy na." shafa kanshi yayi tare da cewa. "To Sulaiman." sai ya kuma juyawa ya kalli su Babba Ali tare da cewa. "Bisimillanku mu shiga ciki." to sukace kana suka biyo bayan yaron da aka kira da Sulaiman ,wanda yake rik'e da hannun Alhaji Kabiru yana cewa. "Abba ina Isma'il baka zo min da shiba." dai-dai lokacin kuma suka shiga cikin tamfatsetsen parlour yayinda Alhaji Kabiru yayi sallama tare da cewa Sulaiman. "Isma'il baya nan ai sun tafi Yola shida Maminshi." sai kuma yayi murmushi ganin Alhaji Sani ya nufi gaban Babansu Ishaq cikin mamaki yace. "A a yau inada manyan bak'i kenan kaida kanka Baraden Gombe ai da kayi aike ka kiranima zan amsa kiran." Sai ya kuma kalli su Bappa Ali dake cikin shiga ta kamala cikin sakin fuska yace. "Marhabikun ku iso ku iso." cikin kamala suka zazzauna shi kuwa Alhaji Sani cewa Sulaiman yayi. "Sulaiman maza je ka kawo musu abin sha." da sauri yaron ya juya ya fita ba jimawa ya dawo da wani babban tire cike da ababen sha mai sanyi, sai ya kuma juya da sauri ya fita, yayinda tuni su kuma suna gaggaisawa, cikin nitsuwa Sulaiman ya kuma shigowa tare da tire cike da fruits ya ajiye bisa stol dake tsakiyansu, sannan ya fara ajiye musu gorunan ruwan dana juice sai cup d'ad'd'aya a gabansu. yayinda tuni su kuma suna tattauna abinda ya kawosu, sosai Alhaji Sani ya d'auki abin da mahimmanci dan ganin manyan mutane suna cikin lamarin, nan take yayi musu k'arin bayamin sannan suka bashi kud'in da dama sun taho dasu nan shaidu suka sa hannu, Barrister Rabi'u da Barrister Salman yayan Saminu kenan Yariman dukku suka rattaba hannu ga manyan shaidu. A nan take kuma sukayi mgnar hayan shagon da in kayan sun iso zai ajiyeshi. ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Kabiru ya shaida musu akwai wani shago can k'arshan layinsu amman a luggune, murmushi Babba Ali yayi tare da cemishi. "Ba matsala nawane kud'in hayan." Alhaji Sani ne ya d'an gyara zama tare da cewa. "Shagunanshi ne ai, in kunaso ku biya kud'in wata shida in kuma kunga ba matsala ku biya kud'in shekara d'aya yadda dai kasuwa ta kama." Barrister Rabi'u ne ya kalli Bappa da Saifuddeen tare da cewa. "In dai da hali ku biya kud'in shekara d'aya." da wannan shawarar bappa Ali ya biya kud'in shekara d'aya, sannan Saifuddeen yasa hannu a cikin dukkan takardun da ya kamata na company maggi daga nan suka gama komai sannan suka sallami juna a mutunce suka tafi. Koda suka koma gida kuma Bappa Ali ya fito da sauran kud'insu na hayan filinsu da za'a kafa services ya nunawa Ummi dasu Saifuddeen dan cikinsune ya biya hayan shago, nan kuma suka tsaida shawarar bappa Alin ya sari kayan abinci tunda dama sana'arsa ce aune-aune. nan bappa Ali ya fara sari a duk kasuwannin da yake zuwa kamarsu. Ngalda, bajoga, Nafad'a, Hashidu, dogon ruwa, kiri, Malam Sidi, Kurugu, kumo, Dad'in kowa D'ukul togo. Da dai sauransu. kasan cewar lokacin Kaka'ace amfanin gona ya nuna so kayan abinci yana araha

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148