Chapter 66
Chapter 66
bamu sa'an aiki, kana kasa a ranka nakasa ba kasawa bace, ka jajircewa zuciyarka, kasa a ranka wannan jarrabawace da ubangiji kan iya jarabtan dukkan bawanshi, kaga misali a kaina gani bana iya mik'ewa tsaye kuma rana tsaka larurar ta sameni sakamakon had'arin mota, wanda lokacin ina ganiyar k'uruciya ta, na gama karatu na kenan na fara aiki da mako biyu nayi hatsarin, wanda saida akayi tsawon shekaru biyu ana jinyata kafin na fara tashi zaune da kaina, kumani a lokacinma nakasata ta shafi lafiyata a matsayina na d'a namiji, koda na yarda da k'addara, nasan cewa jarrabawace bayan shekara 8 da faruwar abun lfyar mazan takana ya fara dawowa cikin ikon Allah kafin na cika 10 years da yin had'ari har nayi aure sai da muka shekara 7 da ita kafin Allah ya bamu ciki a lokacin har na cire tsamnani, Allah da ikonshi ciki nada wata 5 ya bare. Nayi matuk'ar shiga damuwa a lokacin ashe abinda bamu saniba, cikin tagwaye ne d'ayan nan bai bareba, bayan wata hud'u aka haifa min d'iya mace, daga kanta kuma Allah bai bamu waniba, to nima kenan da nakasata tafi taka in sha Allah kai muna sa ran zaka samu lfy kuma Alhamdulillahi kaga kai matsalar bata shafi mazantakan kaba. kasa a ranka kana nan da lfyarka." kai ya rausayar tare da lumshe ido kana ya gyad'a kanshi kai alamar. "To, ngd." daga nan suka fara aikinsu ba kama hannun yaro, babu mgna sai nuneneniya, tuk'uru suka duk'ufa kanshi. A can waje kuwa Ummi aje carbin hannunta tayi kana ta jawo wayarta ta fara karatun qura'an tanayi tana nemawa gudan jinin ta lfy a wurin mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa, Allahu wahidun k'ahharar. Ya Rabi'u kuwa ya d'auki Aunty Mami sun tafi ya maidata gida, dan tayiwa bak'in nasu abinci, kana shi kuwa ya wuce ma'aikatansu. Ishaq kuwa da Ahmad suna nan zaune suna dakon fitowan doctors dan suji menene matsalar Saifuddeen d'in. Kana Hayatunddeen kuwa ya tafi Airport dan tarbo Dr Adnan. Bayan kamar awa biyu suka fito a jere, Dr Ayman yana turawa weelchair d'in da Dr Aliyu ke zaune, yayinda, Dr Batulu ke biye dasu a baya. Suna fitowa Dr Adnan da suka ise bada jimawa ba, ya mik'e da sauri, ya nufi inda suke hakama Ahmad da Ishaq wanda kunnuwanshi ke mishi jagora duk inda sautin muryarsu da sautin takun Ahmad yake bi, kai baka tab'a cewa makaho bane, domin mutunne mai cikar zarrah da zati kekyawane mai tarin tsabta da yawa sukance suna ɗan kama da Saifuddeen. cikin girmamawa Dr Adnan ya d'an rusuno ya bawa Dr Aliyu hannu tare da cewa. "Barka da hantsi sir." cikin kula da dottaku Dr Aliyu yayi murmushi irin nasu na manyan doctors kana yace. "Barka dai Adnan ashe har ka iso, ya hanya." "Alhamdulillahi ya aiki?." Adnan yace yana bin bayansu shida Ishaq da Ahmad suka shiga tamfatsetsen office d'in Dr Aliyun. Ummi kuwa addu'a tayi kana ta kife wayar bisa cinyarta, ido ta zuwaba Hayatuddeen dake tsaye gaban Dr Batulu yana neman a barshi ya shiga yaga d'an uwan nashi. cikin kula tace. "Kayi hak'uri bayan mun gama aikin bashi taimakon gaggawa an mishi allurar bacci so ana buk'atar ya huta." sai ta kuma matso gaban Ummi da idanunta suka cika da hawaye, ganin tazo gabanta Ummi tace. "Dan Allah Dr ki gaya min halin da yake ciki? koda baya rayene kada ki boye min, tunda abinnnan ya farufa bangashi ba sai dai in haggoshi daga nesa, ke uwace kinsan abinda uwa kanji in makamancin wannan ya faru da d'anta please me ya sameshi?." a hankali Dr Batulu ta zauna gefenta kana ta dafa kafad'arta tare da cewa. "Abinda ma muke zaton zaiyi tsanani sai muka sameshi da sauk'i, Saifuddeen bai mutuba yana raye kuma insha Allah da yamma ni da kaina zan shigar dake inda yake, kafin nan ya farka zaki ganshi ya ganki kuyi mgna dashi, yanzu dai da ku koma gida domin nan akwai masu kula dashi. wadanda Dr Aliyu ya tanatar su zasu mishi komai, sannan batun abinci ma karku damu akwai d'iyar Dr d'in duk abinda za'a bashi damar ci ita zata shirya mishi komai. Yanzu kuje gida da yamma Ku dawo,zaku ganshi kuma Dr Aliyu zai gaya muku duk abinda ke damushi da matakin daya kamata ku dauka dama yadda zaku kula dashi." sosai Ummi ta gamsu da bayananta kana taji sanyi a ranta, haka yasa tace. "To ba matsala ngd matuk'a Dr in sha zanyita addu'a zamu koma biyar na yamma zamu juyo." cikin fara samun nitsuwa Hayatuddeen yace, "Dr zai gane mu ko? numfashi sa ya dai ta ko?." kai ta gyad'a mishi tare da cewa. "Sosai ma har magna fa yanayi mana da body language alamun yana gane duk abinda muke cewa." a tare sukace Alhamdulillahi. sannan Dr Batulu ta bawa Ummi number ta kan in sun dawo da yamma su nemata. Su Abban Farida kuwa, da Dr Adnan da Ishaq bayasu shiga sun so Dr Aliyu yayi musu bayanin matsalar Saifuddeen, so amman sai ya basu hak'uri sabida ya gaji yana buk'atan hutu ya dai ce suje da yamma su dawo dukansu yana son ganinsu dan zai musu cikekken bayanin matsalar Saifuddeen d'in da basu shawara da da gaya musu dabarun kula dashi. dole suka hak'ura kan saida yamman in sun dawo. Kai tsaye gidan Ya Rabi'u suka wuce dan Ishaq ya k'i su Ahmad da Adnan suje su kama hotel. A motar da Ya Rabi'u ya bari a hannun Hayatuddeen suka tafi, amman Ahmad ya karb'i tukin a cewarshi Hayatuddeen d'an koyone bazai yarda ya jasuba, Ummi na gaba kusa da Ahmad kana Ishaq da Adnan da Hauatudeen suna baya a haka suka tafi. Aunty Mami kuwa tuni ta shirya musu abinci tasa an gyara BQ ensu. *A garin Gombawa d'iban fari* Yau tunda sanyin safiya Zaleeha ta shirya domin zata je kaltingo don zantawa da nakasassun wannan yankin. Amman har zuwa ƙarfe taƙwas na safiyar ta gaza yin komai, ji takeyi tamkar tayi ta kurma ihu ta faɗi abinda folisawannan suka haneta faɗi tare dayi mata barazana da ranshi, kukan da takeyi ya sanya ida nunta kumbura sukayi jazir ga wani fitinennen ciwon kai, ya zatayi a duniya ko wacw ƴa in tanada matsala uwarta take fara tinkara ,amman sam Mama itama bayan folisawan tabi. tafin hannunta tasa ta share hawayenta a karo na barkatai, a hankali ta miƙe kana ta zari car key ɗinta, a falo ta samu Mama a hankali ta gaiseda da muryarta dake disashe, cikin haɗe fuska tace. "Wato dai bazaki bar koke-koken nan ba ko, so kike sai an gane wani abu ya faru da ke ko?." Kai ta jinjina cikin sanyi tace. "Mama ai wani abu kam yama faru, sanadi nane fa akayi mishi komai, ban saniba yana raye ko ya mutu wani hali yake? tun randa abin ya faru da dare washegari naje asibitoci sunfi bakwai babushi ba dalilinshi, ni badan raina da sukayi min barazana da shiba, a a shida yake hannunsu nakeji kar su ƙara cutarmin dashi." ta ƙarishe maganar wasu zafafan hawaye na kwaranyo mata, ita kuwa Mama kasake tayi tare da cewa. "eyeh sannu uwarshi harda su wani kada su ƙara cutar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148