Chapter 79
Chapter 79
da ganinsu zasuyi taushi, ji yadda suke shek'i." still bai kulata ba, ganin ta shagala wurin kallonshi, ido ya lumshe yana tuno Zaleeha a ranshi sai yake jin inama itace kusa dashi, a hankali taja numfashi kana tasa hannu bisa fuskarshi ta karkad'a mishi yatsunta, d'ago lumsasshun idanunshi yayi ya d'an kalleta. ganin ta nuna mishi allurane yasashi, rumtse ido kana ya d'an mirgina tare da gyara zaman damtsen hannunshi na dama ya bata damar mishi allurar, a hankali ta zira mishi allurar kana ta fara tura ruwan, ido ya kuma rumtsewa kana yana sunkuyar da yatsun hannunshi har suna bada sautin k'aras-k'aras. a hankali ta kalleshi cikin tausayawa tace. "Sannu." bai nuna mata ya ganeba dan ya lura bata san yana gane mgnar mutaneba in yana ganin bakinsu, maganin ta babballa kana ta mik'a mishi. Hannun dama yasa ya amsa kana ya afasu a baki tare da amsar robar ruwan da ta mik'o mishi, sannan ya had'iyesu, bayan ta gama mishi komaine ta k'ara mishi gudun AC ganin tunda ta mishi allurar yake d'an had'a zufa, gaban gadon ta dawo ta gyara mushi mayafin sannan ta kalleshi tare da cewa. "Zan tafi gida, dare yayi, dan kai gobe da sassafe zan dawo Allah ya baka lfy, da masu kula da kai zasu ku kwana tare." A ranshi yace. "Amin ngd." a zahiri kuma bai kuma kulataba, itako fita tayi, shi kuwa text yayiwa Rahma da Raliyya da Hayatuddeen kana yayi addu'a ya rufe ido dan allurar ta fara sashi gyangyad'i. Rahma kam dama da Adnan zai taho cewa yayi ta koma Side d'in Mamanshi dan yana soron kartayi ta kuka, kuma Alhamdulillahi dake uwar mijintan na sonta suna kuma tausaya mata suna kula da ita shiyasa ta d'an sake bare yanzu da taga text d'in k'anin nata yana ce mata. "Adda, yanzu Ya Adnan yazo, mukasha hira, yace min wai kince sai dai ku taho tare, ni kuwa gani garau na samu sauk'i itama Ummi da Hayatudden zasu dawo, an bar gida ba manya ga Ahmad ma yazo nan, duk sun tare a kaina sai kace basu da aikin yi." murmushi tayi tare da cewa. "Zan zo kam in su Ummi sun dawo, in banzo na gankaba to wa zai zo ya ganka?." murmushi yayi kana yace mata. "Budurwata mana zatazo." dariya tayi cikin samun nitsuwa tace. "Iye to me sunanta surkar tawa." kai ya rausayar tare da cewa. "Sai na dawo zan gaya miki." daga nanne ya rufe wayar tashi. Shiko Dr Adnan tare suka tafi da Dr Aliyu a can ya kwana. Ummi kuwa tunda suka koma ta kasa samun sukuni duk da ta fawwala Allah lamarinta, Amman ta kasa cin abinci, Hayatuddeen kuwa ya d'an sake sabida yadda Ya Rabi'u, da Ya ishaq da Ahmad suka rink'a yi mishi nasiha da bashi k'arfin guiwa da nuna mishi yarda da k'addara. Aunty Mami kuwa tausayin Ummi ya hanata sukuni sabida da ka ganta kasan tana cikin damuwa da fargaba, shiyasa data gama shirin baccinta ta kuma soya mata gwai da biredi kana ta had'a mata tea ta nufi d'akin da suka sauk'i Ummin inda suke sauk'e Mamansu Ishaq in tazo. bisa sallaya ta sameta tana rik'e da carbi, gefenta ta zauna tare da tank'oshe k'afafunta, ganin har yanzu Ummi hawaye take zubdawa cikin sanyi Aunty Mamin tace. "Kiyi hak'uri Ummi ki dena kuka dan Allah kiyi ta mishi Addu'a, insha Allah zai samu lfy." cikin sanyin murya tace, "Mami ya zanyi in banyi kukaba, me zanyi da hawayen nawa, ce minfa sukayi Saifuddeen na bazai sake tsayawa da k'afafunshi ba." cikin tausasawa tace. "A a fa Ummi ana kyautata zaton wata rana zai iya mik'ewa." kai ta jinjina kana tace, "Kayya ba dai boye min sukeyi ba, hakama sukayi min lokacin Nuruddeen da Abbansu." Sai kuma ta share hawayenta cikin tarin damuwa taci gaba da cewa. "Ina rasa nitsuwata da konciyar hankali na in naga Saifuddeen yana cikin wani hali, ina jin tausayinshi a raina ina rasa samun nitsuwata gaba d'aya a kanshi, ina tausayawa Saifuddeen in na tuna lfy lau na haifeshi, sai kuma abubuwa suketa biyu bayan rayuwarshi." cikin tausayawa Aunty Mami tace. "Ummi. Wayene Nuruddeen d'in da Abbansu?." a hankali Ummi ta nisa kana cikin sanyi ta fara bata lbrin asalinsu Saifuddeen dama yadda ya samu larurar rashin ji... Cikin tsananin kuka da tausayawa Aunty Mami tayi saki wani nannauyan ajiyan zuciya. Numfashi ta fudda a hankali sannan ta jingina da gadon tana mai sheshesk'an kuka har saida Ummi ta dawo tana bata hak'uri, cikin rauni ta share hawayenta tare da cewa. "In sha Allah daga yanzu duk sanda nayi salla zansa Saifuddeen cikin addu'o'i na ya bani tausayi tun yana yaro k'arami yayita fuskantar k'alubalen rayuwa." sai ta kuma gyara zamanta tare da cewa. "Dan Allah Ummi na rok'eki ki daina yawan kuka, kiyi ta mishi addu'a in sha Allah Saifuddeen bazai tab'eba." Sassanyan ajiyan zuciya Ummi ta sauk'e tare da cewa. "In sha zan daina yawan kukan zanyi ta mishi addu'a." cikin jin dad'i ta mik'a mata kofin tea d'in, ba musu ta karb'a tare da cewa. "Ngd Allah ya miki al'barka." Amin Amin tace sannan ta mik'e ta fita dan bata wuri. Washe gari kuwa tuni Doctor Aliyu ya harhad'a dukkan bayanan cutar Saifuddeen ya turawa Dr Acash prasat wanda yake aiki a wani babban asibiti dake New Delhi India, Ahmad kuwa E passport d'in Saifuddeen da Hayatuddeen da nashi ya tattara ya nufi Airport tun da sanyin safiya ya fara musu cuku-cukun samun visa, A nan ya samu Adnan ya taho dan tare zasu tafi dole yayi musu jagora a matsayinshi na likita da yaso ace da Dr Aliyu zasuje to shi aiyuka sun mishi yawa, sai da suka gama duk abinda ya dace na zirganiyar samun tafiyar nasu cikin sauri cikin sa'a kuwa suka samu jirgin da zai tashi jibi nan zuwa India direct New Delhi Indira Gandhi Enternational Airport, saida suka gama komai na tafiyar sannan suka baro airport d'in. Ummi kuwa da Ishaq da Saifuddeen Ya Rabi'u ne ya kaisu Asibitin. Suna isa Dr Batulu tayi musu jagora har d'akin da Saifuddeen d'in yake, sosai Ummi taji dad'in samunshi cikin nitsuwa yana rik'e da wayarshi fuskarshi d'auke da murmushi, da sauri ta isa bakin gadon kujerar dake kusa dashi taja ta zauna, ishaq kuwa yana isa bakin gadon ya rik'e k'arfen gadon ya tsaya, Hayatudddeen kuwa gefen shi ya tsaya kusa da Umminsu, da sauri ya ajiye wayarshin tare da juyawa inda suke jin Ummi na shafa kanshi, murmushin ya kumayi tare d'ago hannunshi ya shafa kan Hayatuddeen yayinda Ummi kuwa ke shafa kanshi, sai ya kuma mik'o hannunshi d'aya ya kamo hannun ishaq. Ya Rabi'u ne ya d'anyi murmushi tare da cewa. "Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauk'i ko?." kai ya jinjina alamum eh. Dr Batulu kuwa sai binsu da idanu takeyi cikin shawar shak'uwar dake tsakaninsu. Cikin kula Ummi tace. "Sannu ko babana ya jikin?." wayarshi ya d'auka da sauri ya rubuta mata. "Alhamdulillahi jiki da sauk'i." cikin jin dad'i duk sukace. "Allah ya k'aro mana sauk'i." Amin Amin ya amsa a saman lab'b'ansa. Dai-dai lokacin kuma su Ahmad da Adnan suka shigo, bayan duk sun gaisa sun tabayi ya mai jikine sannan Ahmad ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148