Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

d'as da jikinshi yayi wani irin mashahurin kyau da korjini. Pillows inshi ya d'an d'ad'ad'aga alamun yana duba abu, sabuwar woyarshi ya d'auka sannan ya fito ya nufi d'akin Ummi yana kunna woyar, gefen Ummi ya zauna wacce take shan fura da nono mai sanyi. da sauri ta mik'a mishi kofin kai ya jingina da gado kana ya amshi kofin, kurb'a ya d'anyi sannan ya fara rubutu a woyar da tun randa ya dawo daya sata a caji ta cika ya cireta ya ajiye bai kuma bin ta kantaba sai yanzu, rubutu yayi sannan ya nuna mata fuskar woyan. "Ummi zanje in gaida su Baba Ashiru kuma zan isa gidan Baba Hamisu ma, kuma ya kamata inje dasu Faruq da Hayatuddeen, gashi kuma suna gidan Goggo Dada." bayan ta karanta ne ta d'an gyara zama kana tace. "To kaje ka cewa Salisu ya d'aukosu mana." kai ya gyada cikin gamsuwa daga nan yasha fura da nonon sannan ya fita yaje ya gayawa Salisu, cikin k'ank'anin lokacin Salisu ya d'aukosu. Bayan sun dawo ne ya tasasu a gaba suka tafi Katafila inda nan gidan Baba Ashiru yake, suna shiga matarshi ta tarbesu a mutunce bayan sun gaisane tace su isa yana k'ofanshi tare da abokanshi nan ya tasa keyarsu Hayatuddeen suna isa suka samesu a harabar wurin yana tare da abokanshi a ciki harda Malamin isilamiyar su Saifuddeen, yana ganin Saifuddeen ya saki murmushi tare da cewa. "Masha Allah Saifuddeen d'alibina, yanzu kuwa nake mgnarka." da sauri ya isa inda suke cikin girmamawa ya basu hannu duk ya gaidasu d'aya bayan d'aya, Baba Ashiru kuwa rik'e hannun Hayatuddeen yayi yana shafa kanshi, shi kuwa Malaminsu Saifuddeen cikin iya mgnar kurame yayi ta tambayar Saifuddeen bayan rabuwa nan yake sanarwa Saifuddeen shima ya k'aura ai yanzu baya Dukku jiya da yamma yazo dan ziyartan 'yan uwa da abokan arzik'i, hira sukayi sosai dan Malamin nasu yana tsananin son Saifuddeen dan ya yarda da tarbiyarshi tun yana ji gashi yasan yaron yanada tsananin ilimi da fahimta. koda suka tashi tafiya sai Saifuddeen ya d'an sunkuyo kud'i ya zaro a aljihunshi 'yan d'ari bibbiyu kimanin dubu bakwai dubu biyu ya ware ya ya ajiye a gaban Baba Ashiru sannan ya kuma zaro dubu biyu ya ajiye a gaban Malamin nashi ya kuma ajiye a gaban d'aya abokin nasu dubu biyu kana ya maida dubu d'aya cikin al'jihunshi, kusan a tare suka had'a baki wurin cewa. "A a haba dai Saifuddeen in bamu baka ba ai baza mu karb'a daga gareka ba." kai ya rink'a jujjuya musu alamun dan Allah kada suk'i amsa su karb'a su samishi al'barka. Cikin sanyi Baba Ashiru yace. "Deen ai sai ka sani jin kunya ni ya cancanci in taimaka muku, amman na gaza sabida lamarin yau da gobe ya hana." kanshi ya rinka jujjuyawa alamun kada yak'i karb'an kud'in, sai ya kuma kalli Malamin nasu dake cewa. "Kud'in sunyi yawa ai Deeen." wayarshi ya d'an zaro yayi rubutu kana ya bawa melanin nashi wayar, amsa yayi tare da fara karantawa yana karatun yana murmushi cikin dottaku yace. "Bodd'i ta girma ai yanzu ta bar kukan zuwa makaranta ta daina genged'i in zata bada hadda, to ta gode niko zan saya mata sweet dan har yanzu tana nan da son shan zak'i tunda ka koya mata." murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna Hayatuddeen yayi alamun tambaya ko ta kai Hayatuddeen d'in tsawo, da sauri ya gyad'a mishi kai tare da cewa. "wai ai tafi Hayatuddeen tsawo yanzu kusan shekaru biyar fa rabonka da ita tun randa ka bar zuwa Islamiya, nima tunda ka fara spacial education ban kuma ganinkaba saida ka gama daka gama d'inma sai rasuwar Abbanku na kuma ganinka." murmushi yayi kana yayi alamun a gaidata daga nan ya sallamesu ya tafi. Kai tsaye gidan Baba Hamisu ya wuce dasu Faruq, bayan sun gaisa ne ya bashi sauran dubu d'ayan nan sannan ya bar Faruq da Adam anan dan suyi d'an kwana biyu. daga nan ya tasa keyar Hayatuddeen suka nufi gidan su Aunty Nina dan yi musu gaisuwan salla, suna fitowa yaji alamun saqo ya shiga woyarshi dake cikin aljihunshi, yana dubawa kuwa yaga sak'on Ishaq ne yana ce mishi yazo Dukku fa gashi ga Ummi, so jin haka yasa suka kama hanyan gida. Yana shiga ya samu suna zaune a tsakar gida bisa taburma, Ishaq sarkin surutu sai hira suketayi da Ummi da Adda Rahma, suna shiga imran yayi sauri ya mik'e yaje ya ruggumi Saifuddeen tare da cewa. "Oyoyo Hamma Saifuddeen yau kam nima nazo gidanku, Umminka ta bani fura da nono nasha." kanshi ya shafa tare da jinjina mishi, Hayatuddeen kuwa tuni ya isa jikin ishaq sunata surutu dan duk masurutane, Ummi da Rahma kuwa sai murmushi sukeyi, yayinda Ishaq yake cewa Hayatuddeen. "Yauwa Autan Ummi kaga yau na kawo maka abokinka imran autan Mama." da sauri Hayatuddeen ya juyo ya kalli Imran tare da cewa. "Shima autane?." cikin dariya ishaq yace. "Eh shima autane kuma sakali irinka." aifa daga nan Hayatuddeen da imran suka d'inke dan sakalcinsu iri d'aya ga tsawonsu dai-dai. ranan Ummi da Ishaq da Saufuddeen da Adda Rahma da Aunty Nina tare suka wuni koda yamma tayi Ishaq yace dole Saifuddeen ya rakashi Shabewa dan zaije ya gaida Goggo Dada ya kuma ga Raihana da Raliya dan yayi missing d'insu, aifa haka suka d'unguzuma da su Saminu da dama yake son bin bayan Raihana nan sukaje suka gaida Goggo Dada, daga bisani suka dawo dole Ummi tasa Ishaq da Imran suka kwana. Washe gari suka tafi da Saifuddeen. saida yayi kwana biyu a gombe sunje gidansu Jabeer da Hisham har gidansu Ibrahim duk sunje, kana Baban Ishaq ya tasasu gaba shida kanshi ya kaisu k'ungiyar (Jonapwd) nan take sukayi duk abinda ya kamata na shaidar suna cikin members d'in k'ungiyar. Daga nan suka ziyarci abokan su da suka yi makaranta d'aya. Sannan ranar da zai koman yaje ya wuni a kasuwa dan hutun salla ya k'are. to a ranar ya tambayi Alhaji Aliyu gidan baba Bello ina yake, to cikin sa'a ya samu Alhaji Aliyu da kanshi ya d'aukeshi sukaje gidan Baba Bello dake cikin jeka da fari, nan suka samu ashe baida lfy shiyasa tunda akayi salla bai dawo kasuwa ba, yayi farin cikin ganin Saifuddeen sosai bare da Alhaji Aliyu ya yaba mishi nagartan Saifuddeen d'in, shi kuwa Saifuddeen wannan 10k d'in ya zaro ya bashi ya yace ya nemi mgni sannan ya d'anyi cefene, yayi godiya sosai hakama matarshi Inno sunji dad'in sosai, sannan yace ba matsala Saifudddeen yaci gaba da kasuwancin shi, sai in Allah yasa ya samu lfy, in ya dawo sai suci gaba da kasuwancin. Da haka dai sukayi sallama suka tafi. Tun daga ranar Saifuddeen yaci gaba da kasuwancin sa ba kama hannun yaro, sosai fa harkan leda ta amsheshi harkalla taci gaba, ya k'ara sabawa da mutane sosai, duk sati yakan ware ribar kwana biyu ya yiwa baba bello sayayyan kayan abinci, na dubu goma sannan ya bashi dubu biyu ya rik'e wannan abu yasa sam Baba Bello bai kuma sha'awan komawa kasuwancinsa ba tunda yanaga ya huta da wahala kuma ya lura hannun Saifuddeen yanada al'barka duk abinda ya kama yana cin gaba. Shi kuwa Saifuddeen ribar kwana biyar d'in yake

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148