Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

had'awa yayi sayayyan abincin gidansu to zai yi mako biyu kuma yana saka ribanshi a asusu, riban omonshi kuwa da pure water daya ya koma sai yake ajiyesu dan hidiman yau da kullum. Ya Adnan kuwa tuni ya fara aikinshi gadan-gadan shida Dukku sai dai ziyara. Tuni Mudassir ma yaci gaba da karatunshi a G.S.U inda a gidan Adnan d'in yake zama, Ishaq ma tuni yaci gaba da karatunshi. Hakama Saminu shima yayi nisa a karatunshi. Salisu ma yanzu ya ci gaba da kanshi sabida Saifuddeen ya rege mishi kud'in balance sosai to sai in bashida darasi yake fita aiki dan ya samu damar yin hidimomin karatunshi da kula da kakarshi. Hayatuddeen kuwa tuni ya fara koyan d'inki a wurin Ahmad da shima yanzu yanata cuku-cukun ci gaba da karatunshi inda yake son kafin ya koma cikin gombe Hayatuddeen ya gware a d'inkin, shi kuma sai ya tafi da kekenshi zaije yaci gaba da karatu, duk cikinsu Saifudddeen ne da Warisu sune basu samu daman ci gaba da karatun suba. Sai dai shi Saifuddeen tuni ya samu ya gamawa Raihana da Raliya cuku-cukun karatunsu tuni ma Raihana kam ta k'are secondary school. Yanzu hankalin Ummi ya fara konciya, Tuni Ya Adnan kuma ya baiyana soyayyarshi da Rahma amman biki yace sai next year kowa yayi farin ciki da haka. Koda Ahmad ya koma gombe gidan ya Adnan d'in shima ya zauna. Kasuwa tayi al'barka kullum Saifuddeen baya fashin zuwa shida Salisunshi, yana zuwa zai rarraba leda sai ya d'auko omonshi bisa kai sannan ya rik'o botikin pure waternshi dasu Coca-Cola yayi ta yawatawa kuma Alhamdulillahi sosai yake ciniki Allah ya sawa kasuwancin nashi al'barka. Kota ina yanzu an sanshi a kasuwar gombe. Yanzu duk kostomominshi suna da number shi yanada number su, duk mai buk'atan kaya zai kirashi ya kai mishi misali in ledodin su ya kare suna son k'ari ko in suna son abin sha mai sanyi ko omo to kawai sai su mishi text. Zuwa yanzu duk abo kanshi suna da woyoyinsu. Yau jumma'a tunda sanyin safiya da suka shigo ya gama reba lododinshi har ya d'auko omonshi da da kayan sanyinshi yanata zagayawa. K'arfe d'aya dai-dai na rana ya shiga bakin shagonsu Jabeer ya d'an zauna dan abin sanyinshi ya k'are kuma ya gaji shiyasa ya zauna dan ya d'an huta kafin ya d'auko wani, sunata d'an tab'a hira da Jabeer bai jima da zamanshi yaji wayarshi na babureshin cikin al'jihunshi na k'irjinshi alamun sak'o ya shiga, a hankali yasa hannunshi ya zaro wayar, yana dubawa yaga Alhaji Kabiru ne mai shagonsu Mai, Manja, Maggi, kafi, da dai sauranshi. Bud'e sak'on kana ya karanta sak'on. "Saifuddeen kawo mana ruwa mai sanyi da molt guda hud'u sai fanta d'aya." amsa ya maida mishi cewa. "To gani nan zuwa." daga nan ya mik'e tare da zaran botikin, cikin sabo Jabeer yace. "Allah ko Balarabe wlh ka rink'a hutawa fa." kai ya jinjina mishi tare da mishi alamun ai. "Me nema baya gajiya in dai yana samun d'an na kashewa a sama." daga nan ya juya ya tafi. Koda yaje ya ciko botikinshi da kayan sanyin kai tsaye ya nufi shagon Alhaji Kabiru. Yana zuwa sai ya samu suna can cikin shagon bisa dukkan alamu bak'i yayi kuma manyane masu cikar haiba. Amir ne d'aya daga cikin yan gidan shagon Alhaji Kabirunne ya kalli Saifuddeen tare da cewa. "Yauwa Balarabe tsallaka ka shiga can ciki yana tare da manyan bak'i ne su zaka kaiwa ruwan sanyin. jin haka sai ya tsallaka ya shiga, kai tsaye gefen da suke ya nufa, yana isa Alhaji Kabirun yayi murmushi tare da cewa. "Yauwa Saifuddeen balarabe, bamu ruwan sanyi Faro roba hud'u da molt roba hud'u sai ka mik'o min fanta d'aya kasan ni nafi son fanta." cikin girmamawa fuska k'unshe da murmushi ya matso ya mik'a mishi fantan kana ya rusuna gabansu ya fara zaro gorunan Faro dana molt. Yayinda tuni idanunshi yana kan d'aya daga cikin bak'in inda yake cewa. "Gsky Alhaji Kabiru in dai kanada daman saran wannan kaya to wlh ka zuba jarinka domin kamfaninne ya kawo mana talla har gida, sun bamu tabbacin tabbas akwai riba mai tarin yawa, to ni kuma naga bazan iya yin harkallan ni d'aya ba." ci gaba yayi da kallon bakin mutun tare da mik'a mishi roban Faro, still yana kallon bakin mutum inda yake cewa. "Koda bashi ne kaci muyi sarin nan in sha Allah zamuji dad'in hark'allan." sai kuma ya juyo ya kalli d'aya daga ciki wanda ke cewa. "Ni kaina last week nayi sari yanzu hakama bani da kud'i kuma wlh bashi zanci dan nasan in sha Allah zamu samu riba." d'aya daga cikin sune yace. "Kai bani ruwan nan zansha ka tsaya kana kallon bakin mutane." Alhaji Kabirun ne yayi d'an murmushi tare da cewa. "Alhaji Sani ai wannan yaron irin Isma'il nane kurmane baya ji." jin haka yasa wanda aka kira da Alhaji Sani ya d'an tab'a Saifuddeen tare da mishi alamun ya bashi ruwan, juyowar da zaiyi ne yayi dai-dai da lokacin da Alhaji Sani yayi wata mgnar da ta sa Saifuddeen t...! By *GARKUWAR FULANI* *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 9* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ _Ga masu buΖ™atar sayan littafin Nakasa ba kasawa bace, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number 09097853276. Ko kuma ka/kiyi min transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/ki turo screenshort na shaidar ka/kin biya_ ~Wannan shafi nakune mutanen Group Ι—in Nakasa ba kasawa bace fans two ina al'fahari daku~ Free page Tsurawa fuskokinsu ido cikin hikima yake nazartan zantukan da sukeyi, wanda ya rasa madosar zancen, mik'ewa yayi a hankali ya fara nad'e gammon da yake sawa a kanshi kafin ya aza kwalin omon, yana mai ci gaba da nazartan kalaman wanda aka kira da Alhaji Sani yana cewa. "Nan da wata biyu zasu rufe sararwan, dan haka muyi k'ok'ari mu samu mu sari koda kad'an-kad'an ne, Company ya talla ta mana ne dan sanin mune manyan costumes d'insu na nan jihar Gombe, sun kuma bani tabbacin tabbas nanda wata hud'u Maggi zaiyi tsada sosai kusan ninka kud'inshi zaiyi, domin ya bani misalai da dama, sun kuma ce wannan damace da aka bawa kuduncin Nigeria, to shiyasa suma musulmanmu suka nemi da a bawa arewacin Nigeria samun wannan garab'asar dan sanin arzik'in musulmi yanada fa'idoji da dama." d'aya daga cikin sunne ya kuma cewa. "Ni kam in sha Allah zan k'ok'arta in samu koda kad'an ne." gyara zama Alhaji Kabiru yayi tare da zaro kud'i yana mik'awa Saifuddeen yayinda hankalinshi ke kan abo kan nashi, cikin nitsuwarsa yace. "To zanyi k'ok'ari inga ko zan samu wasu 'yan kud'ad'e na da nike bin bashi sai in sa hannu a ciki." cikin farin ciki sukace. "Alhamdulillahi to Allah yasa ka samesu." Amin Amin yace tare da kallon Saifuddeen da ya juya ya fita zuciyarshi cike da sak'e-sak'e haka kawai yake son yaji tushen zancen. Su kuwa bayan sun gama tattauna yadda abin zai wakana. Nan suka sallami Alhaji Kabiru suka tafi. Saifuddeen kuwa yana fita yaci gaba da zageyenshi na tallan omo da kayan sanyin nashi, bai fito kasuwarba har k'arfe shida na yamma dan tunda azumi ya wuce suka dawo kamar da sai bayan sallan isha

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148