Chapter 135
Chapter 135
A can New G.R.A kuwa kasan cewar yau girkin Mamane dan Mamy yau ta ƙare kwana biyunta. Suna dawowa sallan isha Ahmad da Habu sukayi cikin gida. Da sauri Habu ya tsaya, cikin mamaki yace. "Ya Ahmad kalli can." Da sauri Ahmad ya isa wurin da Habu ke nuna mishi, ganin kayan lefen Zaleeha ne da aka kawo jiya watse aƙasa, setin gaba ɗaya akwatuna 30 dasu tarkacen gishiri da goro duk an watsosu waje, cikin tsananin Al'ajabin halin Mama da tsaurin ido irin nata yace. "Innalillahi! Habu tayani mu kwashesu, tunkan Baba Malam yazo yagani, nasan bazaiji daɗi ba aransa ba." Da sauri suka fara tattara kayan, sai kuma duk suka tsaya tare dayin shiru, sakamakon jin muryar mahaifinsu ta window parlour'n shi. "Ku barsu a wurin ko tsinke kada ku ɗaga, ku wuce ku bar wurin." Shiru sukayi cikin tsananin tarin damuwa dan dagajin muryar Baba malam yana cikin tsananin baƙin ciki, muryarshin ce ta katse musu tunanin da sukeyi. "Ku bar wurin ko nace!." ya ƙarishe maganar cikin bada umarni irin na fusata. Da sauri sukace. "Toh". sannan suka juya, kowa ya nufi ɗakin mahaifiyarshi. Gefen Mamy Ahmad ya zauna cikin ƙunan rai yace. "Please Mamy kije ki bawa Baba malam haƙuri, naga ranshi ya matuƙar ɓaci, kice yayi haƙuri ya barmu mu kwashi kayan, in yaso mushigo dashi nan ɗakinki." Murmushi Mamy tayi tare da cewa. "Hmmm Ahmad ai wannan ba hurumi na bane, ku bar kayan kamar yadda ya umarceku, Mamanku ta zauna da Malam kusan tsawon shekaru 30 kenan yau, amman har yau bata san waye Malam ba, bata taɓa ƙureshi ba, amman da dukkan alama yau zata san kaɗan daga cikin halaiyarsa, idan ransa ya ɓaci, shi acikin ruwan sanyi zai dafata." Jin haka yasanya Ahmad cewa. "Hmmm kai Mama tanada matsala Wallahi, mutum duk haƙurinshi sai ta ƙureshi." "Kaje kaci abinci ka dena zama da yunwa." Mamy ta umarceshi cikin son kauda zancen, kasancewar bata son tayi mgnar kishiyarta, dan wannan shi ke ɓata alaƙar zuciyar yaro da matar ubanshi. Ƙarfe tara dai-dai Mama ta shiga parlour'n Baba Malam, tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi, ta yadda shi baima jitaba. A kan kujera ta sameshi zaune ya zubawa TV idanu yana kallon BBC News. Kan dinning table ta kai dubanta, gani tayi yanda ta ajiye abinci, yana nan ayanda yake, da alama babu wanda ya taɓa ko food flask ɗin bare akai ga ci, juyowa tayi ta maida kallonta kan fuskarshi da ta ɓoye ɓacin ransa, ta sani koda bazaici abinciba to tabbas zaisha tea, dan haka taku uku zuwa biyar ne yakaita gaban dinning area, cup ta ɗauka sannan ta haɗa mishi tea kamar yadda ta saba, a hankali tazo ta ajiye mishi cup ɗin a kan table ɗin dake gabanshi, wanda yawanci nan yake miƙe sawunshi idan yana zaune akan kujera. danne ɓacin ranta tayi dan yanzu so take ta gwada kirsa tunda taga hayagagar bata kamashi, gefenshi ta zauna tare da cewa. "Ga tea ɗinka nan nahaɗa ma kada yayi sanyi." shiru yayi baice ƙala ba, ganin yadda yayi kamar babu wani mahaluƙin dake kusa dashi, yasanya cikin tsareshi da ido taƙira sunanshi. "Malam!." Baima juyo ya kalleta ba bare tayi zaton ko zai amsa mata, saima kaɗa ƙafafunshi da ya farayi a hankali. shi kuwa wani irin tafarfasa zuciyarsa keyi, yadda tazo tayi ta mishi ihu da haushi a kanshi gaban yaranshi da uwar gidanshi, shine ke ƙara ɓata masa rai, sam bata sa hankali da nutsuwa cikin lamuranta. Kusa dashi ta kuma matsowa tare da cewa. "Malam magana nake so muyi da kai fa." Bai bi ta kantaba bare ya saurareta saima ƙara volume ɗin TV da yayi. Cikin takaicin abin tace. "Ya kamata muyi magana ta fahimtar juna, a bani matsayina da damata a matsayina na uwar yarinya, ni nasan Zaleeha bata son wannan nakasasshen, ta tsaida gwaninta, harma ta bashi daman ya turo komai na aure, tunda dama iyayenshi kam sun zo kuma ka sansu ba baƙin fuska bane, d'an manya ne gaba da bayansa." Gum yayi mata tamkar dutse, ita kuwa sai surutai takeyi uwa aku, ganin an gama labaran ne ya sashi, miƙewa tare da kashe TV sannan ya nufi bedroom ɗinsa, da sauri tabi bayanshi tana Magana, bai kulata ba, haka ya shiga bathroom, ruwa ya watsa sannan yayi al'wala kana ya fito. A bakin gado ya sameta tana zaune, shi kuwa shirin bacci yayi kana yazo ya tsaya gefenta, da hannu ya nuna mata hanyar fita alamun ta fice mishi daga ɗaki, fuska a tsuke tace. "Muyi maganar tukun!." Fuska ya kuma tsukewa wanda saida taji gabanta ya ɗan faɗi, yayinda zuciyarta kuwa ta buga da ƙarfi, hanyar fita ya kuma nuna mata, da sauri tace. "Dan Allah, dan darajar ma'aiki kayi haƙuri ka buɗi baki muyi magana." Ido ya rumtse dan ya rigada ta haɗashi da Allah. Itama sanin in dai ta haɗashi da Allah zai saurareta ne ya sata yin hakan. cikin kaushin murya da haɗe fuska zuciya na tafasa murya a zafafe yace. "Kije ki kwashi kayan da kika watsar ɗin ki maidasu ɗakinki ki ajiyesu yadda kika samesu." da sauri tace. "Dare yayi fa." A kausashe yace. "Baza kuma su kwana a waje ba." Cikin sanyin jiki tace. "To bari in ƙira Habu yazo ya kwashesu." A ƙufule yace. "Waya fito dasu?." Kai ta juya tare da cewa. "Ni ce." Cikin bada umarni yace. "To kije ki maidasu kizo muyi maganar." Bata da zaɓi dan ta san kaɗan kenan daga halinshi dole taje a daren ta kwashi kayan, ta maidasu cikin ɗakinta, tana gamawa a gajiye ta koma ɗakin nashi, a kwance ta sameshi cikin maida numfashi tace. "Na maidasu. Ka tashi muyi maganar." Kai ya jujjuya tare cikar haiba da isa da gidanshi yace. "Maganar ai na gamata babu wani wanda zan aurawa ɗiyata Zaleeha sai Saifuddeen, kuma babu wani mahaluƙin da ya isa hanani sai ubangijin daya halicceni!." Yana faɗin haka ya gyara kwanciyarshi tare da rufe ido alamun bacci zaiyi. Cikin tsananin takaici haɗi da ƙunci tace. "Ni kuwa Wallahi ƴata bazata auri gurgu kuma kurma ba, ɗiyata bazataje ta zama majinyaciya ina kallo da idona ba, sannan bazan taɓa bari takashe rayuwarta wajen kula da nakasasshe ƙaskantacce ba, Allah ya sauwaƙa ma, ni dai ajinina ban haifawa nakasashshe matar da zai aura ba ehe!!." Tana gama faɗin haka ta juya ta fita a fusace. Gyara kwanciya Baba Malam yayi tare da rufe idanunsa, sunayen Allah Kawai yake ambata acikin ransa. *** Washe gari kuwa Zaleeha daga gidan hajja Inna ma'aikatarsu ta nufa, bayan ta gabatar da shirinta na mushaƙata kai tsaye gidansu kuma ta nufa. A harabar gidan tayi kiciɓis da ya Ahmad, cikin shaƙuwarsu ta nufi inda yake, da alamun cewa shima yanzu shigowarsa cikin gidan. hannunshi ta kamo tare da cewa. "Ya Ahmad nayi kewarku kwana biyu bana nan ko kuyi cikiyata." murmushi yayi tare da cewa. "Muma munyi kewarki, kin san inata shirin tafiyarmu ne, naso in wuce da Lubna amman Mamy tace wai in bar miki ita." tsalle tayi cikin jin daɗi tace. "Yessss! My mamy kai amman ko naji daɗi sosai!!." Murmushi yayi tare da cewa. "Ato ai dama amare yan jin daɗine." Sam bata kawo komai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148