Skip to content

Chapter 145

Chapter 145

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

hand bag ɗinta shima me kalar navy ta riƙe ahannunta tare da ɗaukan wayoyinta, ƙiran iphone da kuma samsung, wani navy blue toms masu kyau da taushin gaske ta sanya aƙafafunta, wanka tayiwa jikinta da daddaɗan turarenta mai daɗin ƙamshi, sosai tayi kyau duk da kasancewar ƴar rama ta bayyana ajikinta amma tayi kyau sosai, raman ma saiya kasance yaƙara mata kyau da burgewa. Cikin takunta mai ɗauke da burgewa tafito daga cikin ɗakin nata, bata samu kowa acikin falon ba hakan yasa kai tsaye ta nufi compound ɗin gidan, cikin nutsuwa taƙarasa jikin motarta, buɗe murfin motar tayi tare da shigewa ciki, maigadi ne ya wangale mata gate sannu ahankali tatura hancin motar tata waje, cikin nutsuwa haka take murza steering motar, azahiri idan kaganta bazaka taɓa tunanin cewa wani abu na damunta ba, amma abaɗini tanajin kusan ma tafi kowa yawan damuwa, sosai takejin kamar zuciyarta zata fashe saboda damuwa, batayi wani tafiya sosai ba taƙaraso gaban gidan na Maryam wanda yake madaidaici mai kyaun gaske, maigadi ne ya wangale mata gate ɗin gidan ta cilla hancin motar ciki. Da mamaki take kallon motar Yaya Ahmad dake fake cikin compound ɗin gidan na Maryam, sam batasan ma da zuwansa cikin garin na Gombe ba, da ɗan sauri ta bude murfin motar tafito, direct ta nufi cikin gidan, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga, bakinta ɗauke da sallama, Ya Ahmad, Maryam, sune zaune acikin falon yayinda suka juyo da kallonsu gareta, idanunta ne suka sauƙa acikin na Ya Ahmad, saurin ɗauke idanunta tayi tare da turo bakin nata gaba, lokaci guda hawaye suka cika idanunta, sai kawai ta kawar da kanta gefe, cak kuma ta tsaya batare da ta ƙaraso tsakiyar falon inda suke zaune ba. "Zaleeha!." Maryam taƙira sunanta murya asanyaye, domin tuni ta hango ƙyallin hawaye acikin idanun Zaleehan. Ɗan juyowa Zaleeha tayi ta kalli yayarta ta, sai kuma ga hawaye zirrr sun ziraro daga cikin idanunta, rumtse idanu Ya Ahmad yayi tare da ɗan cije laɓɓansa, sam baya ƙaunar ganin hawaye a idon ƙannensa, musamman ma ita Zaleeha dayakejinta matsayin shalelensa, cikin son sama mata nutsuwa yace. "Bansan ƴan matan Yaya Ahmad da saurin kuka haka ba, nasan dai tana da juriya sosai, calm down my lovely sister, zo kigayamin menene damuwar da har tasanyaki hawaye!". Ae tuni kafun ma yaƙare maganar tasa ta rugu da gudu zuwa cikin falon, faɗawa jikinsa tayi tare da sakin wani irin kuka mai taɓa zuciya, ƙwarai tajima bata samu wanda zata shiga jikinsa tayi kuka haka ba sai yau, hakan yasa ta ƙara riƙe Ya Ahmad ɗin nata tana kuka sosai, shiru Yaya Ahmad da Maryam sukayi, sam sun kasa hanata kukan, domin sunyi imani cewa kuka ma rahamane, sannan wani lokaci yana gusar da damuwa, kana kuma duk cikinsu babu wanda baisan kukan me Zaleehan keyi ba, domin dama ansan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, tayi kuka sosai, aƙalla ta share sama da mintuna 15 tana kuka, sannu ahankali kukannata ya tsagaita, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai-akai, ɗagota daga jikinsa Ya Ahmad yayi tare da kai dubansa gareta, hannu yasa ya goge hawayen da gaba ɗaya suka dame fuskarta, cikin tausasa murya yace. "Akullum tun kina ƙarama nakasance ina me horanki da ki-kasance mai haƙuri, Domin shi haƙuri yana maganin abubuwa da yawa Zaleeha, sannan Addu'a tafi kuka don itace babban jigo akan komai, ke ƴar uwata ce kuma jinina, bazan taɓa son ganinki cikin damuwa ba, amma yazamuyi Zaleeha? yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta alamace dake nuna ƙarfin imanin mutum, sannan kada ki manta kowani bawa a duniya da irin jarabawar da Allah yake ɗaura masa, wani mai kyau wani akasinta, shin meyasa bazaki sa aranki cewa aurenki da ake ƙoƙarin yi da Saifuddeen haɗi ne na Allah Ba? babu fa wani bawa aduniya daya isa sauyawa kansa Ƙaddararsa!." ɗan tsagaitawa da maganan yayi kana ya sanya hannunsa ya shafi kanta, cikin son kwantar mata da hankali yace. "Kaf cikin ƙannena nafi ƙaunarki Zaleeha, inason duk wani abu da kikeso, banason ɓacin ranki ko kaɗan, dan Allah Zaleeha, kada ki watsawa mahaifinmu ƙasa a ido, kizama mai biyayya agaresa koda yaushe, ita al'barkan iyaye tana da tasiri akan ƴaƴa, har abada Baba Malam bazai taɓayin danasanin zamantowarki ƴa agaresa ba matuƙar kikayi masa biyayya, zai tabbata yana me alfahari dake, ki yi dubi ga ƴar uwarki". Ya nuna Maryma wanda take zaune itama idanunta sunyi rau rau, kana sun cika da ƙwalla. "Maryam takasance abun al'faharin Baba Malam, tayi masa biyayya, bata bijiremasa ba, tayarda da zaɓinsa duk da cewa bata so, amma ayanzu ki dubeta, tana zaune cikin jin daɗi, farin ciki, annushuwa haɗi da salama, hakan yafarune kuma duk saboda biyayyan da tayi ga mahaifinmu, sam bata bijire masa ba duk da kuwa bataso, haka yasa muke tsananin sonta kema ki daure ki masa wannan biyayyar." Hannayen Zaleeha ya kamo cike da kula yace. "Dan Allah Zaleeha kimin al'ƙawarin zaki yiwa Baban mu biyayya, Insha Allah aurenki da Saifuddeen al'khairi ne, sannan Baba Malam bazai taɓa kaiki inda za'a cutar dake ba!." Sabon kuka Zaleeha tasanya wiwi kamar wanda aka faɗawa ranar muruwarta, sam kalaman Ya Ahmad basu shigeta ba, inama dazai gane cewa ayanzu idanunta sun rufe, bataji bata gani, inama dabai ɓata lokacin sa ya faɗi waƴannan maganganun ba, zuciyarta tajima dayin nisa wajen tsanan Saifuddeen, bata sonsa, ba kuma ta son aurensa. Haka Zaleeha ta dinga yi musu kuka wiwi, Ya Ahmad da Maryam kuwa sai nasiha sukeyi mata tare da ban baki, saidai kuma ko ɗaya bata ɗaukar nasiharsu, aduk ma sanda sukace da ita tayi haƙuri ta ɗauki Ƙaddara, takuma yiwa mahaifinsu biyayya, saitaji kamar wuƙa suke caka mata agadon bayanta, idan kuwa suka yaba Saifuddeen, suka kuma ce ta rungumi aurensa hannu bibbiyu sai taji kamar narkakken dalma suke watsa mata cikin kunnuwanta. Haka dai tasha kukanta ta ƙoshi har saida idanunta suka kumbura, daga ƙarshe dai Ya Ahmad ne dayaji yanda jikinta ya ɗau zafi yasakata amotarsa suka dawo gida, yayinda tabar motar ta agidan Maryam ɗin. Tunda ta dawo daga gidan Maryam tasa kanta aɗaki ta kulle, wani zazzafan zazzaɓi kuwa take yakawo mata ziyara, domin irin kukan da tayi yauɗin nadabanne. Haka Zaleeha ta kwashe kwana d'ayan cur bata fitowa ko ina, banda kuka ba abun da ta sa agaba, washe garin nema da taji zaman kaɗaici naneman takurata yasanya ta shirya don zuwa aiki ko kewan da takeji zai ɗan ragu, ko wani wadataccen kwalliya yau ɗin batayi akan fuskarta ba, wata bubu gown red colour da red vail kawai ta yafa ajikinta, amma dayake itaɗin ce mai kyau bawai kwalliyan da takeyiwa kanta ba duk da haka saida tayi kyau, cikin ƙunci haka ta nufi gidan redion nasu na Vission FM. Koda taje banda Rabeel da suka gaisa babu wanda ta kula, kai tsaye tatafi gabatar da shirinta na Mushaƙata. A kasalance ta gyara zamanta tare dacewa. "Barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirinmu mai taken mu shak'ata. sai kuma ta d'anyi shiru tare da sakin wak'ar,. Tattausan lafazi mai dad'i jinshi ya ratsa raina, hadarin so yayi had'owa. Sai ta kuma d'an rage volume tare da cewa. "Taken na masoya ne, gareku masoya." A hankali

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148