Skip to content

Chapter 125

Chapter 125

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

BABANA DON ATSAIDA MAGANAR Aurenmu."_ Wani irin ingantaccen farin cikine ya cika zuciyar Baba Malam jin cewa Zaleeha ta amince da Saifuddeen takuma tsai dashi a matsayin gwaninta, cikin tsananin farin cikin daya kasa ɓoyuwa akan fuskar Baba Malam ya ɗago ya kalli Saifuddeen wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, cikin zuciyarsa yace. "Nawa wasan ya soma Zaleeha daga gobe idanunki zasu fara kuka kamar yadda kikasa Ummina kuka, kuma Insha Allah ni da kika ƙira Ginannen taɓo kuma dutse, niɗin nanne zan-zamo mijinki!." "Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin kasancewar haka sosai Saifuddeen, saboda haka ni mahaifin Zaleeha na baka Zaleeha sannan koda yaushe kashirya kana iya turo manyanka su kawo sadaki don atsaida ranar auren ku da ita!." Wani irin tsananin farin cikine suka cika zuƙatan Ya Ahmad da kuma Ya Aminu, shikuwa Saifuddeen faɗan farin cikinsa ma ɓata lokaci ne, domin kallon fuskarsa kaɗai da ƙwayoyin idanunsa sun isa sanardakai farin cikinsa. Cikin aminci da salama Saifuddeen ya miƙa godiyarsa ga Baba Malam harma dasu Ya Ahmad, nan sukayi sallama cikin mutumta juna har bakin mota Ya Ahmad da Ya Aminu suka raka Saifuddeen saida sukaga ficewar motarsa acikin gidan kana suka juya suka koma wajen Baba Malam don su tattauna yanda bikin zai kasance... A cikin mota kuwa wani irin murmushi Saifuddeen yayi tare da sake jingina bayansa ajikin kujeran motar, lumshe idanunsa yayi yana me tunano haɗaɗɗiyar surar jikinta, tabbas yaƙudurta aransa cewa zai shayar da ita ruwan mamaki, aduk sanda ya aureta kuwa saiya nuna mata cewa NAKASA BA KASAWA BACE...! By *GARKUWAR FULANI* *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 29* *NA* *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Daga Gidansu Zaleeha kai tsaye unguwar tudun wada suka nufa wato gidan Baba Bello, aƙofar ɗan madaidaicin gidan na Baba Bello Sule driver yayi parking motar, both ya buɗe inda ya cirowa Saifuddeen kekensa, buɗe murfin motar Saifuddeen yayi, inda dakansa ya yunƙuro ya hau kan keken nasa. Yana gama dai-dai ta zamansa akan keken, Jafar almajirin Baba bello yafito daga cikin gida, ganin Saifuddeen yasanya Jafar sakin murmushi cikin kulawa yaɗan rusuna tare da cewa. "Hamma Saifuddeen sannu da zuwa." Murmushi Saifuddeen yayi masa tare da jinjina masa kai alaman. "Yauwa." Cikin sauri Jafar yajuya ya koma cikin gida, nan ya iske Baba Bello dake zaune yasanar dashi zuwan Saifuddeen, cikin hanzari Baba Bello yazura takalma aƙafansa, inda kai tsaye yanufi hanyar fita daga cikin gidan. Fuska ɗauke da fara'a Baba Bello ya tarbi Saifuddeen, nan yayiwa Saifudeen ɗin iso zuwa cikin ɗakinsa dake hanyar soro. Bayan sun zauna ne Jafar ya kawowa Saifuddeen ɗin ruwa acikin wani babban plastic jug, kofin ruwan Saifudeen ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa, tuno da yanda Zaleeha ta turs masa kayan fruits gabanshi ga kuma tsoronshi cikin ƙwayar idanunta tono hakan ne yasa yayi, yasanyashi sakin murmushi, ɗan kaɗan yasha ruwan gudun kada Baba Bello yaji ba daɗi, cikin kulawa Baba Bello ya dubeshi kana yace. "Sam ban tsammaci zuwanka ba Saifuddeen, ai da nasanya Innar ku (Matar Baba Bello) tayi maka kwaɗon zogale da tumatur, gashi kuma yanzu batanan taje kitso." Murmushi Saifuddeen yayi tare da sadda kansa ƙasa, cikin body language ɗinsa yayiwa Baba Bellon alamar cewa babu komai, nan suka shiga ɗan taɓa hira da Baba Bellon, inda Baba Bellon ya nuna jin daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, domin kuwa tun ranan da suka dawo daga zuwa dubasa da sukayi, lokacin dawowarsa basu sake haɗuwa ba sai yau ɗin, hira sukeyi tsakanin magana da kuma body language, inda sosai Baba Bello ke gane yaren Saifuddeen, wato body language, cikin girmamawa haɗi da kulawa Saifuddeen ya labartawa Baba Bello maganan aurensa, kama daga farkon tura masa tambaya har kawo yanzu, cikin hikima yanemi shawarar Baba Bello agame da bikin. Cikin jin daɗin yanda Saifuddeen ɗin ya karramasa, yakuma maidashi uba, yasanya Baba Bello gyara zama, nan yashiga bawa Saifuddeen ɗin shawarwari masu kyau, sosai kuwa Saifuddeen ya aminta da shawaran, inda ya yanke cewa jibi jibinna za akai masa lefe da kuma sadaki, sun ɗan jima suna hira daga bisani yayi wa Baba Bello sallama, kuɗi yaciro ƴan bandir ɗin ɗari biyar biyar sabbi ƙal ya ajewa Baba Bello agabansa, cikin dattako da halin kamala Baba Bello yace. "Dan Allah Saifuddeen kada kasa kanka awahala, bayan ɗaukemin nauyin gidana da kayi gaba ɗaya kuma saika ƙara da sakanka a wata wahalan? kabar kuɗinka Saifuddeen nagode sosai bani da abinda zance maka sai dai addu'a, domin kuwa koda baka da lfy baka ƙasarma baka daina kulawa damu ba." Fuska Saifuddeen ya kwaɓe cikin rashin jin daɗin dawo masa da kyautar tasa da Baba Bello yayi. fuska ya marairaice, cikin body language ɗinsa yace. "Dan Allah Baba Bello ka karɓa, kaifa matsayin Uba kake agareni, kamar yanda zanyiwa mahaifina kaima haka zanyi maka.!" Jikin Baba Bello ne yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen yaron ƙwarai ne, samun irinsa na da matuƙar wahala, tabbas Ummi tayi sa'ar haihuwa, domin samun Saifuddeen amatsayin ɗa babban nasara ce ga rayuwa, haka Baba Bello ya amshi kuɗin nan batare daya soba saidai sanin halin Saifuddeen yasanyashi karɓan kuɗin dole, nan ya rako Saifuddeen ɗin har bakin motarsa, saida Baba Bello yaga tashin motar tasu Saifuddeen kafun ya juya yakoma cikin gida. Daga gidan Baba Bello kuwa kaitsaye ƙaramar kasuwa suka nufa, abakin kasuwan sule driver yayi parking motar, shida kansa ya buɗewa Saifuddeen murfin motar tare da gyara masa zaman kekensa, haka Saifuddeen da Sule driver suka kutsa cikin kasuwa, cikin nutsuwa Saifuddeen ke sarrafa kekensa, duk inda suka wuce ido ne ke binsu, yayinda mutane da yawa ke yaba tsantsar kyau irin na Saifuddeen, saidai ganinsa akan keken guragu shine abun dake ɗaure musu kai, kowa kallon cikakken balarabe yake yi masa, sam koda wasa babu wanda ya shaida kamannin Saifuddeen, duk acikin mutanen dake kallonsa babu wanda yakawo aransa cewa shine wannan matashin saurayin dake gararanban yawon raba leda, yake kuma yawon raba omo, kana harma da tallan fiyo wata (pure water), babu wanda zai gansa ayanzu yace shine wannan yaron da yasha gwagwarmayar rayuwa, yayi ta zagaye kasuwa koro-koro luggu da saƙo. Fuskarsa ɗauke da annuri ya ƙarasa gaban wawakeken shagon wanda yake mallakinsu, Mudassir da Warisu naganinsa suka taso cikin tsananin farinciki suka tarbeshi, sam basu tsammaci ganinsa ba don ya matuƙar shammace su, yaɗan jima kaɗan ashagon nasu Warisu inda suka ɗan taɓa hira kaɗan, duban Mudassir da Wareesu yayi cikin body language ɗinsa yace. "Kufara shiri tun yanzu don nanda ƴan sati kaɗan zakusha biki." Mamakine ya bayyana akan fuskar Wareesu, daɗan ƙarfi yace. "Biki kuma na waye?." Murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna kansa. Cikin alamun ban mamaki Wareesu yace. "Wow Surprise kenan! Kai amma naji daɗi sosai Allah yasa ayi damu, koya Mudassir, yakamata ne ma ai mufara gagarumin shiri." Wareesu yafaɗa cike da farinciki. Shiru Ahmad da ya shigo yanzu yayi tare da kafe Saifuddeen da idanu, kallonshi shima Saifuddeen ɗin yayi, yanayin yanda yaga fuskar Ahmad kaɗai yasayashi gane abun dake cikin zuciyarsa, murmushin daya bayyana kyawawan dimples ɗinsa yayi, cikin son ganar da Ahmad irin yanayin dayake ciki ya lumshe idanunsa, hannunsa yaɗaura adai-dai saitin zuciyarsa wacce ke beating. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ahmad ya sauƙe, tabbas ya gane hakan da Saufuddeen ɗin yayi me yake nufi, alamace

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148