Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

uzururruka da kud'in da ya biya wanda ya tashi d'auko motor ya samu sauran ribarsa dubu dari uku da hamsin, nan yaje ya bawa Saifuddeen su, shi kuwa Saifuddeen yace bazai karb'i ko asiba, yace yaci gaba da tara ribarsa randa ya samu ya tara koda 5 million ne sai ya maida mishi kud'inshi million ukun shikenan daya bashin, shi kuma ya d'auki wannan na ribar tashi yaci gaba da sari ya samu jarinshi kenan da haka, ya k'ara da cewa ya bar mishi su halak malak. to fa daga nan Salisu ya fara harkar mota babu kama hannun yaro kuma Alhamdulillahi harkar ta amsheshi. Shagunanshi a kasuwa kuwa yanzu Warisu da Bello da Mudassir suke kula dasu yayinda Ahmad kuma ya zama tamkar manajansu, shine ma'ajiyinsu yakan fita zuwa su Lagos onitsha da dai sauransu yayi musu sarin kayan masarufi, direct to company. Bappa Ali kuwa shine mai sarin kayan abinci ciki da wojen gombe Alhamdulillahi yanzu abun ya hab'aka shiyasa yawanci da Warisu yake shiga sauran k'auyuka na sauran jihohi kamarsu. Bauchi, Jigawa, Jos, da Adamawa musamman kasuwar cigari ta adamawa inda nanne dilar manoman shinkafa na jihar. Ummi taje makka ta sauk'e farali hakama bappa Ali da goggo Dada, shima Saifuddeen yaje tare da Adda Rahma Ya Adnan kuwa ya biyawa kanshi da mamansu so duk a shekara d'aya sukaje. To da yayi niyar Raihana da Raliyya duk zasuje shekarar data gabata, inda yacewa Hayatuddeen yayi k'ok'arin haddace izu arba'in kafin nan to zai had'a dashi suje, aiko Hayatuddeen yasa himma, to yanata shirye-shiryen biya musu hajjin kwasam, sai Alhaji Kabiru ya kawo mishi tallan wani gida dake kusa da gidanshi a nan federal low cost. Koda ya samu Ummi da Bappa Ali da zancen sai Ummi tace ya bar batun biya musu hajjin ya bari sai wata shekar in Allah ya kaimu, a cewarta kadarar babban filin da mahaifinsu ya bar musune suka saida suka kama sana'ar dan haka yayi k'ok'ari ya sai wata kadarar da zata ke tuna mishi da gadon da mahaifinsu ya bar musu. shi yaso ya biya musu Hajjin to amman fir Ummi tak'i hakama bappa Ali dole ya hak'ura yabi ra'ayinsu. Sai dai kuma cikin ribar ledanshi da yake tarawa tsawon shekaru da balance d'in machine d'in da Salisu ya rik'e tsawon shekaru da kuma wanda iro yake kawowa har yanzu da kud'in ne yace zai sai gidan sabida baya son tab'a wannan dukiyar gadon nasu yafi son ya sayi gidan da guminshi shi d'aya yadda zai zama halak makal d'inshi, Ummi da bappa Ali sun amince da haka to amman kud'in nashi basu wuce rabin kud'in gidanba dan haka sai ya ranci sauran rabin kud'in a cikin tarin ribarsu na shekarar da zumar zai biya kud'in da balance d'in machine d'inshi da kuma ribar ledodinshi da omonshi da su pure water da ribarshi na gefen kayan masarufi wanda yanzu k'atun firijine ya saya ya ajiye a bakin shagonsu sannan yana saran omo yana sawa a gefe kuma har yau yakan rarraba leda ya kuma had'a kud'insu ya basu sannan ya cire ribarsa, to duk wani abu daya sani dukiyarshice ta kanshi wanda ya tara da guminshi to a account number daya kuma bud'ewa na musamman yake sa kud'in a ciki. so hakan ne yasa suka amince da hakan cikin wata biyar akayi cikinikin gidan aka gama, sosai cinikin gidan ya zabge asusunsu Saifuddeen ya kuma sashi cin bashi, sai dai kuma duk wanda yaga gidan yasan lallai tabbas gidan yaci wannan milliyoyin kud'in. To fa tun randa Hayatuddeen yaga gidan ya kasa ya tsare dolefa su k'aura su bar dukku, haka zai tasa Ummi da Saifuddeen a gaba harda kukanshi shidai a bar wannan k'auyen dashi. Ahmad da Mudassir kuwa har yau a gidan Adda Rahma suke, ita kuwa Adda Rahma har yau Allah bai basu haihuwa da Ya Adnan d'intaba. Warisu da Salisu kuwa suma yanzu an kusa bikinisu inda sun gina 'yan madaidaitan gida jensu a cikin unguwar Dubai cottars. Ishaq kuwa shima yanzu ya fara taka k'asa, tuni yayi gidan kanshi saidai har yanzu bai fara neman aureba, yafi maida hankalinsu wa kula da k'ungiyarsu ta, Joint national association of persons with disabilities, (Jonapwd) gombe state chapter. All the best!!! yayinda yanzu shi har ya samu muk'amin ciyaman a kungiyar, Saifuddeen kuwa bai fiye zuwa ofishin nasuba sai dai yana matuk'ar bada taimako da dukiyar da Allah ya bashi ta sanadin nema da guminshi kusan akwai kason daya ware duk wata yakan saka a asusun k'ungiyar, baya zuwa amman hannunshi na zuwa sai dai in zasuyi Mittin mai girma da mahimmanci to Ishaq na sashi zuwa bisa dolen-dole da zaran an gama mittin kuma zai tafi. Ahmad kuwa soyayya yake zubawa Raliya sosai. Yauma kamar kullum Hayatuddeen ya tasa Ummi da Saifudden da Rahma da tazo duba jikin Mamansu Ya Adnan a gaba, fuska ya kwabe tare da tura baki cikin kalato hawayen dole yace. "Dan Allah mu bar zancen auren Ya Ahmad da wannan yar cukului d'in shin nan." bai kula Raliyya dake watsa mishi hararaba yaci gaba da cewa. "Ni dai dan Allah ku rufa min asiri mu k'aura mu bar wannan gari na dukku wallahi ni dai na gaji da garin nan." cikin irin son da iyaye ke yiwa 'yan autansu Ummi tace. "Wai ni kam ku saurari autana d'innan mana yace muku ya gaji da dukku." fuskarshi ya kuma kwab'ewa tare da cewa "Ba waninnan Ummi ai duk kece kikak'i ki amince na san in kin cewa Hamma na mu k'aura dai zai yarda." Rahma ce ta gyara zamanta cikin sanyin muryarta tace. "Wallahi Allah ko Ummi nima ina son ku k'aura ku dawo cikin gombe kusa dani, ku ganifa bani da kowa a can dan ma Allah yayi Mamansu Ishaq tanada kirki, wlh ko Ya Adnan ma cewa yayi ya dai kamata ku dawo gombe ko dan karatun Raliya da Hayatuddeen, dan cewa yayi ya kamata ace Raliya taci gaba da karatu ta samu koda N,C,E ne tunda sun nacewa juna ita da Ahmad kuma shi yace bai yi aure a gidan hayaba, gashi kuma ya kasa k'arisa ginin gidanshi." shi dai Saifuddeen ido ya zuba musu dan shi kanshi ya gaji da wannan zirga-zirgan kuma yana son faranta ran Hayatuddeen da Faruq, shiru sukayi jin Faruq na cewa. "Nima dai wlh na gaji da k'auyen nan yaseen ko mu k'aura mu koma gombe, ko kuma inbi Ya Adnan in koma gidansu." cikin nitsuwa Ummi tace. "To Saifuddeen ka jisu ko?." Kai ya gyad'a mata alamun eh yaji, cikin sanyi tace. "To nima da kaina ina son mu koma cikin gombe ko dan tak'aitawa Saifuddeen zirga-zirgan da yakeyi kullum yana hanya tsakanin Gombe da dukku, to sai dai haka kawai in na tuna mu k'auran sai inji zuciyata ta tsinke wani azabebben fargaba yazo ya rufeni shiyasa jikina ke mutuwa." Da sauri Rahma tace. "In sha Allah ba komai sai al'khairi kawai dai inaga fargaban rabuwa da inda kika saba ne shiyasa kikejin hakan." kai Ummi ta jinjina dan kamar ta gamsu da mgnar Rahma, cikin sanyi tace. "To na amince Babana in dai kana son mu k'aura to na amince." da sauri Saifuddeen ya kalli Hayatuddeen da Faruq da suka durk'usa

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148