Skip to content

Chapter 134

Chapter 134

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

saikunji aranku cewa inama da ace bakuyi ganganci ƙulla wannan haɗin ba, saina sanya baƙinciki acikin zuciyoyinku, kuma sannan saina saku danasani marar yankewa, badai dani kuke wasan ba, hmmm Wallahi zakusan kun taɓo cikakkiyar ƙaɓila Batangali da surkin bateriya, akan auren nan babu wanda zan ɗagawa ƙafa!!." Tana gama faɗin haka ta juya fuuuuu kamar kububuwa tafice daga cikin falon na Baba Malam. Tana shigowa falonta ta soma afkawa Zahira ƙira, da sauri Zahira ta fito daga cikin ɗakinsu tana cewa. "Na'am Mama." A harzuƙe tace. "Zo zonan mu kwashi ƴan iskan kayayyakin nan mu watsasu waje, Wallahi bazasu kwanar min a ɗaki ba gayyar tsiya!." Da sauri Zahira tace "To." Nan suka shiga cikin ɗakin, haka suka dinga ibo akwatunan nan masu kyaun gaske, suna watsasu a tsakiyar farfajiyar gidan, wai don ma kasancewar Mama ƙaƙƙarfar mace ce shiyasa kab ta iya jidon manyan akwatunan, tanayin waje dasu harda su gishiri da goron bata bari ba, ranta yakai ƙololuwa wajen tafasa, jin kanta take dai-dai da uban kowa, jira take wani yace mata cass tuni zata sullesa tas. Saida ta gama watsasu a tsakiyar gidan, sannan ta koma cikin ɗakinta tana haki tamkar wacce tayi dambe ta gaji. Al'wala tayi sannan tazo ta kabbara niyar sallan magriba, wanda tuni lokaci ya ƙure mata, don har an riga da anƙirayi sallan isha. Zaleeha kuwa daga ma'aikatan nasu gidan kakar tasu ta koma, don dama kwana uku ta roƙi Baba Malam daya barta tayi, kuma da yake gidan mahaifiyarshi ce sai bai hanata ba. Kafin ma ta dawo tuni Ziyada ta gama haɗa musu komai na girki, tuwon ɗanyar shinkafa da miyar kase, tana ganin haka tace. "Ziyada ina Zakariyya kuma da tsohuwar nan sukaje, suka barki ke ɗaya a gida?." Cikin yanayin nutsuwarta irin na Maryam sak tace. "Sun tafi gidansu abokinshi Hayatuddeen." Tana warware naɗin gyalen hijabin dake jikinta tace. "Sun daɗe da tafiya ne?." Kai ta gyaɗa mata tare da cewa. "Eh tun da akayi sallan la'asar suka tafi." kai ta jinjina kana ta zaro wayarta ta danna ƙiran number'n Zakariyya. Shi kuwa Zakariyya lokacin suna parlour'n Ummi shida Hayatuddeen da Raliya, sunata tsiya wa Hajja Inna, ita kuwa Hajja inna sai surfa musu boris takeyi, Ummi kuwa sai nan-nan takeyi da hajja Inna dan taji dad'in zuwan kakar abokin autan nata, sosai takejin son tsohuwar a ranta, musamman yadda ta nuna tana masifar son Saifuddeen ɗinta. Ta tasashi gaba tana yabo harda kukanta tana. "Allah sarki bawan Allah, yaro kyakkyawa, Allah ya jarabceshi da nakasa, ganshi kuwa kamar balarabe." Sai kuma ta juyo ta kalli Ummy tare da cewa. "Wannan yaron naki abin sone da tausayawa ga ko wanne mutum ɗan Adam me imani, ki godewa Allah daya azurtaki da samunsa a matsayin ɗa, wasu suna can sun haifi lafi yayyun yara amman sai ki samu yaran munanane kamar kashin dare, kinga ko gwara miki kyakkyawa fari ƙal nakasasshen." Hayatuddeen ne yayi dariya sosai tare da cewa. "Kai tsohuwar nan munana sun boni a wajenki." Zakariyya ne ya zaro wayarshi dake suwa, wacce take cikin aljihun wondonshi yana cewa. "Itafa sam bata son mummunan mutum, in taga kyakkyawan mutun kuma wai ji take kamar ta dawo dashi ɗanta." Dariya sukayi baki ɗaya, kana shiko Zakariyya ya amsa kiran Zaleeha tare da cewa. "Hello Adda Zalees ya akayi ne?." Sai ya kuma yafito Hayatuddeen tare da mishi alamun ga mutuniyarshi fa. amsar wayar yayi ya kara a kunne tare da cewa. "Adda Zalees nayi fushi dake muka dawo ko kizo ki duba kyakkyawan hammana da jiki ko." Murmushi tayi tare da cewa. "Afwan autan gidansu." da sauri yace. "No autan Ummi dai zakice, gidanmu kam ai kwanannan ma Hamma na zai fara ƙenƙesa mana yara sabbin zubi, ƴan yayi kuma kyawawa, irin yaran da Hajja inna ke masifar so." Ƴar dariya tayi tare da cewa. "To aku sarkin zance, please ka cewa Zakariyya su biya Abba bakery ya saya min pizza dan Allah." Da sauri yace. "To ba matsala karki damu zan bashi abin daɗi ma ya kawo miki, cikin na Hamma na zan ɗiba miki." Da sauri tace. "A a ni dai pizza kawai nake so." Bai kulataba ya katse ƙiran. sannan ya amshi kular da Raliya ta haɗa musu tsarabar Kai kayan lefen jiya." Daga nan suka miƙe zasu tafi, har sun kusa fita daga parlour Hajja Inna ta juyo ta kalli Saifuddeen murmushi ya mata, haka itama murmushin tayi mishi sannan ta kalli Ummi cikin halin tsufa tace. "Kin ga ƴata kada ki yarda ki bari wannan kyakkyawan ɗan naki ya auro miki mummunar surka, in kuwa kika bari ya auro miki mummunar surka, to shike nan ya ɓata miki wannan kyakkyawar zuriyar taki, dan tabbas dole wata rana sai ta haifo muku mai kama da ita, dan ni dai anmin na gani, yanzu in kika kalli Zahira zakice ba jinin ahlina bane dan ita kamannin dangin uwarsu tayi yo." Zakariyya ne ya tura baki tare da cewa. "Kefa kince baki da goni a duniya sai mai kyau, to sam gigin tsufarki baya gaya miki gsk, ya zaki rinƙa sarata ina ji, aikin kawai." Dariya sukayi dukansu ganin yadda ta kamo hannun Zakariyya tana cewa. "A a kada kaji haushi shalelena, ai kai sak da kakanka baban babanka kakeyi, shiyasa kai da Ahmad kuke tsananin kama, Zaleeha da Ziyada kuwa dani suke kama, bakaga Zaleeha ko gashi irin nawa ta gado ba?." Janye hannunshi yayi tare da kunna machine ɗinsa, kana ya amshi kular da Hayatuddeen ke miƙo mishi ya saka a cikin ɗan kondon dake gaban machine ɗin. Sai ya kuma kallon Hayatuddeen dake miƙo mishi 10k kana yace. "Ga tukuicinmu na jiya." Dariya Zakariyya yayi tare da cewa. "Kace abin namu ne babu ƙaranci, ashe ko zamuyi casu a bikinga." Sosai Ummi ke murmushi dan Zakariyya sak autan tane da shirmensa. Sosai hajja Inna ta ɗale saman machine ɗin na Zakariyya, kamar ba tsohuwa ba, da sauri Ummi ta riƙe kai ganin yadda Zakariyya ya figi machine ɗin ya fita a guje. Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa. "Hege Zakary namu, wata rana zai ɓarar da hagwaran tsohuwar nan a titi yaseen." Dariya Raliya tayi tare da cewa. "Ai harda karya mata ƙafa." Daƙuwa Ummi tayi musu tare da juyawa tayi cikin gida sannan suma sukabita a baya. Su kuwa Zakariyya na isa ya miƙawa Zaleeha kular da Hayatuddeen yabasa yayi, dan tuni shi yaci a can yayi haniƙan, ita kuwa Zaleeha kamar bazata buɗe kularba sai ta kuma buɗe, ganin abinda ke cikine ya sata yin murmushi sannan ta miƙe tsaye, lemon exotic ta ɗauko acikin fridge kana ta dawo ta zauna, haka ta fara cin pepper chicken ɗin dayaji onion, tanaci tana latsa wayarta, Ziyada kuwa tuni tabi bayan Hajja inna da ta kirata wai tazo ta cire mata sarkan da ta sanya awuyanta, kasancewar idanun tsufa gareta bazata iya cirewa kanta ba. Ƙarfe tara dai-dai Zaliha Ziyada da Zakariyya dukansu suna zaune parlour'n Hajja ina sunata hirarsu irin ta ƴan uwan juna, yayinda kakarsu ke tsakiyarsu, tana kallon kyawawan jikokinta da take matuƙar so arayuwa, dan duk cikin jikokinta tafi son Ahmad da kuma Zakariyya. Sam bata shiri da Habu a cewarta wai shi baya dariya.

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148