Skip to content

Chapter 122

Chapter 122

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

table sukaci abinci su dukansu cike da ƙaunar juna, inda Hayatuddeen keta damunsu da zancen Asma'u Ahmad Matawalle, zancen nasa ɗayane shine yanda yake faɗin takurawan da tayi masa da zancen hammansa, harma cewa tayi wai idan ayyuka sukai mata sauƙi zatazo Gombe'n ta dubashi. Ummi ce taɗago kai ta dubeshi cikin ɗan mamaki tace. "Au ma'aikaciya ce ma kenan to Allah ya taimaka." "Ameen, ma'aikaciyace amma bata gomnati kota kamfani ba, jarumace ƴar film kuma mawaƙiya". Hayatuddeen ya ƙare maganar yana mai sanya soyayyen chips abakinsa. Baki Ummi ta taɓe tare dayin murmushi kawai ta girgiza kanta, tabbas tasan da ace Saifuddeen ɗinta macece to fa da ankwashi ƴan kallo don ba makawa maza asuke musu layin zance aƙofar gida. Haka suka kammala breakfast ɗin cikin lumana, inda Saifuddeen ya tura kekensa har zuwa tsakiyan falon, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga internet don ɗebewa kansa kewa. Sake muskutawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da ɓacin ran dake shumfuɗe aƙasan zuciyarta amma hakan baihanata jin cewa abun da tayiwa Ishaq bata kyauta ba, sai yanzu kalaman da ta faɗawa Ishaq din ke dawowa cikin brain ɗinta, haƙiƙa tasan Ishaq kamilin mutum ne sannan kuma jajirtacce ne, sam abun da tayi masa bai dace ba, saidai kuma koma me yafaru shi ya jawo, sannan abun da tayiwa abokinsa kuwa ko kaɗan bata dana sanin hakan, don ko ayauma yace zaizo zatayi masa wanda ya ninka na jiya. Wayarta ta ɗauka tare shiga contact ɗinta, number'n Ishaq ta zaƙalo, ɗan cije bakinta tayi cikin gamsuwa da zuciyarta ta dannawa number'n Ishaq ɗin ƙira, don tanaso taɗan bashi haƙuri akan abun daya faru, harsaida wayan ta kusa katsewa kafun akayi picking, cikin sassanyar muryarta tace. "Assalamu Alaikum, Malam Ishaq barka da safiya." Shiru taji anyi batare da anyi magana ba, hakan yasa taɗan ƙara duban screen ɗin wayar, ganin cewa eh da gaske an ɗaga wayanne yasanya cikin zazzaƙan muryarta tace. "Dama haƙuri nakeso na baka akan......". ƙit taji ankashe wayar, da sauri ta cire wayar daga kan kunnenta, tare da duban screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sake dialing number'n. Ishaq dake zaune akan table ɗinsa yanajin wayartasa na ringing amma ya share, har yanzun baigama hucewa ba danko ɗaga wayar da yayi ɗazun ma rashin sanin cewa itace yasanyashi ɗagawa amma sam baida niyar ɗaga wayarta. Zaleeha kuwa jin wayar harta katse ba a ɗauka ba, yasanyata sake ƙiran number'n nanma har ya katse ba ayi picking ba, saida taƙira har sau uku amma no answer, hakanne yasa tagane cewa Ishaq yayi fushi sosai, ɗan taƙaitaccen text message ta rubuta masa na bada haƙuri kana ta aje wayarta.. Cikin wata haɗaɗɗiyar boyel yellow colour wanda taji ɗinkin straight jumper ya shirya kansa, boyel ɗin irin mai tsadan nanne hakan yasa aka fesa haɗaɗɗen aikin ajikin wuyanta da coffee brown ɗin zare, sosai kayan yayi kyau, takalmine sau ciki mai kalan coffee brown sanye aƙafarsa yayinda ya ɗaura haɗaɗɗiyar hula akansa itama me kalan Coffe brown, sosai yayi kyau ba abun da jikinsa keyi sai tashin ƙamshi, cikin nutsuwa yake tura whelchair ɗinsa har ya ƙaraso babban falon na Ummi. Ummi dake zaune hannunta riƙe da carbi tanaja, tana ganinsa ta saki murmushi cikin kulawa ta dubesa tare da cewa. "Sai ina kuma?." Murmushin daya ƙara bayyana cikar kwarjini da haibansa yayi, cikin nutsuwa yayi ƙasa da kansa, sam ƙarya ba al'adarsa bace bata kuma daga cikin ɗabi'arsa, hakan yasa yaɗanyi jim kafun ya ɗago kansa ya kalleta, cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan cewa gidansu Zaleeha zashi, shiru Ummi tayi tare daɗan yin murmushi, wani irin fargaba ne taji yacika zuciyarta, hakanan taji tsoron zuwansa gidan su Zaleehan ya kamata, saboda batasan wannan karon kuma me Zaleehan zata faɗa masa ba, cikin son nuna rashin damuwarta tace. "Masha Allah, amma dai ae zaka ƙira Ishaq ko Ahmad don su rakaka ko?." Murmushi yayi tare daɗan lumshe idanunsa sarai ya fuskanci me Ummin ke gujemasa, amma dayake abun da zuciya ke so ne hakan yasa yayi mata alaman cewa. "Insha Allah.Ba abun dazai faru." Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayi masa fatan dawowa lafiya, cikin body language ɗinsa ya amsa mata da "Ameen." Idanunta akansa harya fice daga cikin falon, ajiyar zuciya ta sauƙe, lokaci guda hawaye suka cika idanunta, haƙiƙa tana tsananin jin tausayin ɗanta Saifuddeen, musamman ma yanzu da ta hango soyayyar Zaleeha kwance acikin ƙwayan idanunsa, cikin dauriya ta maida hawayen nata tare da jingina bayanta da jikin kujera, ahankali take jan carbin tana me tasbihi ga Allah. Shikuwa Saifuddeen yana fitowa daga falon Ummin kaitsaye inda Sule driver ɗinsa yake ya nufa, Sule dakansa ya buɗewa Saifuddeen ɗin murfin motar, cikin hikima kamar koda yaushe haka ya shiga gidan baya ya zauna, both ɗin motar Sule ya buɗe inda ya aje keken Saifuddeen aciki, cikin ɗan hanzari ya shige wajen zaman driver tare dayiwa motar key. Fitowanta awanka kenan, gaba ɗaya fatar jikinta ɗauke yake da danshin ruwa, towel ne ajikinta wanda iya karsa guiwarta, zama tayi akan kujeran gaban mirror tare da ɗaukan handrayer'n ta ta jona ajikin socket, dashi tayi amfani wajen busar da dogon gashin kanta wanda ke jiƙe da ruwa, tana kammala busar da gashinnata ta shafawa gashin nata olive hair oil mai tsananin ƙamshin zaitun, cikin nutsuwa ta shiga taje dogon gashinnata wanda tsawonsa ke taɓa har tsakiyar bayanta, wani baby yellow ribbom tasanya akannata tare da tattara gashin tayi farkin nasa agefen wuyanta, body lotion ɗinta mai daɗin ƙamshi ta shafa agaba ɗaya jikinta, powder'nta wanda aƙalla kuɗinsa zaikai 8k ta shafa akan fuskarta, wani light mochka colour lipstick ta shafa akan siraran pink lips ɗinta, sosai lipstick ɗin ya amshi ɗan ƙaramin bakinta, black eye pencil taɗauka tare da buɗe idanunta ta goga acikinsu, da water proof mascara tayi amfani wajen miƙar da zara zaran gashin idanunta, wanda suke ga cika ga kuma tsawo, kallon kanta tayi acikin madubi'n, murmushine ya bayyana akan fuskarta don ita kanta tayi na'am da kyawun da tayi, haƙiƙa sau da dama takan godewa Allah agame da baiwan kyau daya bata. Miƙewa tayi ahankali tare da ƙarasawa gaban ƙaton drawwer'n ta, buɗe drawwer'n tayi tare da zaro wani tsadadden yadi mai kallan yellow light, sosai yadin ya haɗu yayinda aka ƙawatasa da ɗinkin riga da sket pieces, koda ta sanya kayan baƙaramin kyau sukayi mata ba, sket ɗin ɗas ya zauna ajikinta yayinda ya bayyana faffaɗan ƙugunta wanda ke ɗauke da wani irin tsareren hips mai jan hankali, kasancewar sket ɗin yakamata hakan yasa tsararren hips ɗinta bayyana, kamar yanda sket ɗin yayi mata ɗas ajiki haka ma ƴar fitted ɗin rigan ta amshi jikinta sosai saboda irin yanda rigar ta kamata yasanya har kana iya hango beautiful breast ɗinta ta saman wuyan rigar saidai ba sosai ba, wani ɗan manne'n ɗan kunne mai kyau ta saƙala akunnenta tare da sanya wata ƴar siririyar sarƙa awuyanta, zama tayi agaban dressing mirror tare da tsantsara ɗaurin turban akanta, masha Allah kyau kam Zaleeha tayishi harta gaji. Tunda suka ɗauki hanyar G.R.A ɗin yakejin wani irin shauƙi aransa, babu abun da idanunsa ke ɗoki kamar ganin kyakkyawar fuskarta, baisan wani irin so yake mata ba, da tunani kala-kala acikin ransa

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148