Chapter 124
Chapter 124
acikin idona ba? kaduba kaga na tsaneka nace, na tsaneka!!!". Cikin tsananin ƙaraji take maganan yayinda hawaye suka cika idanunta, jitake kamar taje ta ɗauko wuƙa ta caccaka masa. Dai-dai lokaci Sallaman Kaltume mai aikin gidan nasu ya ratsa kunnuwanta, amatuƙar harzuƙe tajuyo tana kallon Kaltume, ƙarasowa cikin falon Kaltume tayi hannunta ɗauke da wani babban tray wanda samansa ke ɗauke da bottle water dakuma kayan marmari dangin su Apple da Inibi, akan babban table ɗin dake tsakiyan ɗakin Kaltume ta ajiye tray ɗin, dubanta takai ga Saifuddeen wanda yake kallonta, aladafce tace dashi "Ina wuni ranka shi daɗe!". Murmushin daya bayyana cikar haiba da ƙwarjininsa yayi inda ya gyaɗa mata kai alamar. "Lafiya" Nan Kaltume ta miƙe tafice daga cikin falon aranta tana me mamakin tsananin kyau irin nasa take cewa. "Duk yanda akayi balarabe ne shiyasa banji ya amsa gaisuwata ba, dadukkan alama baisan ma menace ba, gsky Aunty Zaleeha tayi sa'an miji". Kaltume na fita Zaleeha tasaki wani mugun murmushi tare da cije laɓɓanta, ahankali ta ƙarasa gaban table ɗin da tray ɗin kayan marmarin yake, ɗaukan tray ɗin tayi tare da juyowa ta kalli Saifuddeen turamasa tiran kusa dashi tayi, ranta aɓace tace. "Dama nakasassu irinku sunfi buƙatar irin waƴannan abubuwan hala shiyasa kazo nan don kaci ko? Mayunwaci gasunan saikaci ae!". Tafaɗa tana me tura masa gaba ɗaya tray ɗin, cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da azaban k'arfi, jin zuciyarsa na tafarfasa, sai kuma ya bud'esu da sauri. Juyawa tayi daniyar barin falon, cikin zafin nama da tafasan zuciya Saifuddeen ya damƙo hannunta tare da hankaɗata kan kujeran dake kusa dashi, mamaki ɗauke akan fuskar Zaleeha ta zaro idanu tana kallonsa cike da tsoro, domin sam ita batasan ya akayi ba sai jinta tayi akan kujera, cikin zafin nama ya ƙaraso dakekensa har gabanta, ƙafansa ɗaya yasanya ya tokare gefen kujeran yanda babu yanda za'ayi ta iya tashi. Wani irin horo yashiga yi mata da idanunsa wanda duk rashin kunyarta take kasa kallon cikinsu, da sauri ta sunkuyar da kanta yayinda k'irjinta ke duka uku-uku, ga wani iri abu da taji ajikinta, cikin haɗe fuska da tattaro d'an guntun jarumtarta da ragwowar tsiwartata tace. "Miye hakane dahalla Malam, ni ɗagamin ƙafanka na wuce idan ma maitan nakane yatashi kurwata kur kaci kanka!". Tafaɗa tana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, da sauri Saifuddeen yasanya ƙafarshi ya tokari guiwanta, da tashi guiwar da azaban k'arfi. da sauri ta yarfa hannu tare da cewa. "Wayyo Allah na, mugu'azzalumi, karya min k'afa zakayi ka maidani gurguwa irinka ko?." bai kulata ba sai k'ara datse mata guiwarta da yayi da tasa guiwar har takai suna iya jiyo hucin numfashin juna, yayinda daddaɗan ƙamshin turarensu ya cakuɗa waje ɗaya, ahankali yashiga yawo da idanunsa akan jikinta, wani irin yaaarrr haka yaji a jikinsa alokacin da idanunsa suka sauƙa kan tudun ƙirjinta, tuni tsikar jikinsa suka soma mimmiƙewa yayinda yaji wani irin feeling ya dirar masa alokaci guda, idanunsa ya ɗauke daga kan ƙirjin nata tare da sauƙesu akan laɓɓanta, wani irin yawu ya haɗiya amaƙoshinsa tare da ɗan lumshe idanunsa, jiyake kamar ya jawota ta faɗa jikinsa, yanajin kamar ya ladabtar da ita tahanyar bawa kyawawan laɓɓan bakinta professional kiss, ahankali idanunsa suka ɗan sauya kala daga farare zuwa yanayin bacci, cikin wani irin salo yasanya hannayensa inda ya tallafo haɓarta, idanunsu ne suka dire acikin najuna da sauri tayi ƙasa da idanunta cikin faɗa tasanya hannunta ta buge hannun nasa daya taɓa haɓanta, cikin son koyan rashin kunya murgud'a mishi baki tace. "Ɗan iska kawai!, ai bama sai ka gwadamin a zahirance nagani ba. Duk wanda yaga waƴannan munafukan idanun naka yasan kai ɗan iskane!!". taƙare maganar tana murguɗa bakinta, wayarta dake hannunta ce takawo haske, cireta a key tayi tare da k'ok'arin duba waye mata flashing, sam ba zato ba tsammani taji Saifuddeen ya wafce wayar daga hannunta, rai aɓace ta ɗago ta dubesa cikin gatsali tace. "Bani wayata tunda bada kuɗin Nakasassun guragu na saya ba!". Ƙin bata wayar yayi gashi gaba ɗaya yayi mata ƙawanya da jikinsa, sannan kwarjininsa ya cika mata ido. Saifuddeen kuwa number'nsa ya sanya acikin wayan inda ya danna dialing, take wayarsa dake cikin al'jihun gaban rigarsa ta soma ƙara, ganin numbern ta yafito acikin wayarsa ne yasanyashi katse ƙiran kaitsaye wajen text messages ya nufa, sannu ahankali ya rubuta kalamai masu hikima inda yayi sending zuwa phone ɗinsa, saida ya tabbatar da cewa saƙon yashiga wayarsa sannan ya maida idonshi kanta. Itakuwa Zaleeha cikin ƙufula take binsa da harara, ganin yanda ya tsareta da idanune yasanya a hatsale ta wafce wayarta dake hannunsa, miƙewa tsaye tayi tare da watsa masa harara cikin yanayi na tsanarshi tace. "Kada ka taɓa manta cewa bana sonka, sannan kuma na tsaneka tsana mafi mufi, cigaba da kusantata tamkar kusantan ajalinka ne!". Tana kaiwa nan azancen nata ta tsallake ƙafarsa ta wuce. Da kallo Saifuddeen ya bita harta ɓacewa ganinsa, murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace. "Kin gama naki daga yau ɗin saura nawa ƴan mata yanzu lokacina ya fara." cikin nutsuwa ya shiga tura kekensa har ya fice daga cikin falon, koda ya kawo compound ɗin gidan nan ya iske Ya Aminu wanda fitowarsa kenan aɓangaren Baba Malam, ganin Saifuddeen yasanya Aminu cewa. "Har zaku tafi?" Kai Saifuddeen ya jinjina masa fuskarsa ɗauke da murmushi alaman. "Eh". kana cikin body language ɗinsa yace "Yanason gaisawa da Baba Malam idan yana gida." Murmushi Aminu yayi don sam baigane me Saifuddeen ɗin ke nufi ba, kasancewar ba sosai yake gane body language ba. Ganin cewa Ya Aminun bai gane me yake nufi ba, yasanya shi zaro wayarsa daga al'jihu inda yayi rubutu ya miƙawa Ya Aminu'n, amsan wayan Ya Aminu yayi, koda ya karanta saƙon murmushi yayi, cikin yabawa da hankalin Saifuddeen ɗin yace. "Masha Allah, aikuwa Baba Malam na ciki muje sai namaka jagora." Ya Aminu ne yayiwa Saifuddeen jagora har zuwa cikin haɗaɗɗen falon na Baba Malam. Ganin Saifuddeen yasanya fara'ar dake kan fuskar Baba Malam ƙara faɗaɗa, cikin farin ciki yace. "A'a ɗalibina Saifuddeen kaine ke tafe, Masha Allah sannunka da zuwa." Murmushi Saifuddeen yayi cikin hikima da ladabi yagaishe da Baba Malam ɗin, fuska asake Baba Malam ya amsa tare da tambayansa ya bayan rabuwa, nan suka ɗan taɓa hira tsakanin Baba Malam da Saifuddeen, yayinda Ya Aminu ke sa musu baki, Ya Ahmad ne yashigo cikin falon na mahaifinsa, ganin Saifuddeen ya sanyashi faɗaɗa fara'arsa inda suka gaisa amutumce. Nan suka sake ɗan taɓa hira wanda Saifuddeen ke ɗansa baki ta hanyar body language ɗinsa. Wayarsa yaciro inda ya miƙawa Ya Aminu, bayan yashiga text message saƙon da ya tura da kansa ta wayarta ya bayyana akan screen ɗin wayar tasa, koda Ya Aminu yakaranta saƙon murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa cikin jin daɗi ya miƙawa Ya Ahmad, Ya Ahmad ma yana karanta saƙon yasaki wata nannuyar ajiyar zuciya sosai hakan yayi masa daɗi, amincewa da auren Saifuddeen da Zaleeha tayi, abun farin ciki ne agaresu, domin samun nagartaccen namiji kamar Saifuddeen amatsayin suruki cikin zuri'arsu abun alfaharine sosai. Miƙawa Baba Malam wayar Ya Ahmad yayi, koda Baba Malam yakaranta saƙon da aka rubuta kamar haka. _"Ni ZALEEHA NA AMINCE DA AURENKA Hamma SAIFUDDEEN SABODA HAKA KATURO MAGABATANKA WAJEN
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148