Chapter 110
Chapter 110
halitta zai nema kuma ishaq bai san dakon son dake ran Zaleeha ba. Wani irin ƙwarin guiwa kalaman Ishaq suka ƙarawa Saifuddeen, nan suka cigaba da tattauna hira atsakaninsu ta hanyar gudanar da text message. Zaleeha kuwa daga Jomapwd kai tsaye gidan redionsu na vission FM. ta nufa, tundaga fitowarta acikin motarta gaba ɗaya kallo ya dawo kanta, haƙiƙa Zaleeha cikakkiyar mace ce dake iya ɗaukar hankalin kowani ɗa na miji, cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta ƙarasa babban ɗakin da suke tantance shirye shiryensu kafun su turashi izuwa ɗakin watsa shirye-shirye, saida aka tantance shirin nata na wannan rana kafun aka watsashi tayanda kowa zaijisa raɗau batare da wata matsala ba. Zama tayi akan wata kujera wanda keda ƙafafun taya, ahankali take jujjuyawa yayinda ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta ta ciro tare da saƙala earpiece acikin kunnenta, cool music na Edsheeran ne ke tashi acikin earpiece ɗin nata, ahankali take jujjuya kanta alaman waƙan na taɓa zuciyarta sosai, luf tayi ajikin kujeran tare da kwantar da bayanta kana ta lumshe kyawawan idanunta, tunaninsa ne yayi mata tsaye acikin ranta, wani irin ƙauna haɗi da begensa ne suka cika zuciyarta, bazata taɓa cire rai da rabo ba akansa saba, haƙiƙa ita mai raunice hakanne ma yasanya soyayyarsa ke wahalar da zuciyarta, inama da ace wani zaiji abun da takeji, inama da ace ƴan uwanta zasu fuskanci mai takeji tabbas tasan da kowa sai ya jinjinawa girman soyayyar da takeyi masa, tanajin sonsa har cikin ƙashi da bargo, haka kuma tanajin soyayyarsa tamkar jinine dake gudana ajikinta ako yaushe, hawayene suka cika idanunta sakamakon rauni irin nata. Ajiyar zuciya Raveel yasauƙe, wanda tun ɗazun yake tsaye yana kallonta, ayayinda tayi nisa cikin begen masoyinta, shikuma alokacin yakejin kamar zuciyarsa zata tarwatse saboda ƙaunarta, son Zaleeha yake da duka zuciyarsa, hawayene suka cika idanunsa, hango manager dake ƙoƙarin tahowa garesu da yayi yasanyashi saurin shanye hawayensa, tare da komawa cikin wani ɗan balcony ya tsaya don sam bayason manager ɗin ya gansa, saboda rauninsa ya bayyana sosai ta yanda bazai iya ɓoyewa ba. Yana sako ƙafarsa cikin babban falon wanda yakasance kamar ɗakin hutu ga ma'aikata gidan radio'n vission FM ɗin wani irin walagigin ƙaunarta ne ya daki ƙahon zuciyarsa, yayinda ya lumshe idanunsa tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin ta da ya cika ɗakin, ahankali ya buɗe idanunsa tare da sauƙesu akanta, sam batasan da zuwansa ba kasancewar haryanzu idanunta arufe suke, sannan zuciya da ƙwaƙwalwarta sunyi nisa wajen tunanin abincin ruhinta, ahankali yatako ya ƙaraso gareta, cikin kulawa yaƙira sunanta, sam bata jisaba don tayi nisa atunanin da takeyi, kujera yajawo tare da zama yana facing ɗinta, hannunsa yakai ya zare earpice ɗin dake kunnenta, da sauri ta ware idanunta da sukayi ja ta sauƙesu akansa, cikin mamakin ganinsa da kuma yanda ya cire mata earpiece ɗin kunnenta taɗa kallesa kana tayi ƙasa da idanunta. Murmushi Manager yayi tare da cewa. "Barkanki da hutawa gimbiyar mata". Cikin takura ta amsa masa da yauwa acan ƙasan maƙoshinta, hakanan ganinsa yasanya taji ba daɗi acikin ranta, itafa yanzu hakanan ta tsani duk wani mahluƙin da zaizo mata da zancen soyayya, ayanzu mutum ɗaya kawai take muradi kuma tana nan tana jira ya taho mata da soyayyarsa, "Zaleeha!" Manager yaƙira sunanta murya asanyaye. Bata amsa masa ba bata kuma ɗago kanta ta kallesa ba, sam ayanzu batason damuwa, hutu da nutsuwa kawai take da buƙata. Ganin cewa bata amsa shibane yasanyashi cewa "Kiyi haƙuri Zaleeha, bansan da yaushene kuma tayaya bane nakamu da sonki, amma tabbas inasonki sosai, ina fatan zamo warki mata agareni Zaleeha, nasan kina ganin girma ƙima da kuma mutumci na, amma banda yanda zanyi akan soyayyarki Zaleeha, inajin kaina tamkar ƙaramin yaro akan soyayyarki, bazan gaji da fallasa miki sirrin zuciyata ba, don ina fatan samun nasara agareki!". Sai alokacin Zaleeha ta ɗago idanunta ta kalleshi, inama da ace shine zaune agabanta haka yake furta mata daɗaɗan kalaman soyayya? inama da ace zata kasance da masoyinta kasantuwa tahar abada, ajiyar zuciya ta sauƙe, tabbas tana ganin girman Manager acikin idanunta, saboda hakane ma batajin zata iya tafka masa yayyafin rashin mutumci, don ko bakomai shiɗin babban mutum ne, kanta ta kawar gefe cikin dauriya tace. "Tabbas kamar yanda kafaɗa ina ganin girma da ƙimarka acikin idanuna, saidai dan Allah naroƙeka Manager daka janye soyayyar da kakemin, inada wanda nakeso araina, banajin dagashi zanso wani aduniyar nan, dan Allah karabu dani naji da damuwar dake raina!". taƙare maganar tana me haɗe hannayenta biyu waje guda alaman roƙo. Ajiyar zuciya manager ya sauƙe tare da ɗan rumtse idanunsa, idan yaji tana ambatan cewa tana da wanda takeso, ji yake tamkar kifiya take caka masa aƙahon zuciyarsa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarsa yace. "Kamar yanda kike jinsa acikin zuciyarki haka nima nake jinki acikin tawa zuciyar, bansan taya zan fasalta miki irin tarin ƙaunar danakeyi miki ba Zaliha, dan Allah ki tausayawa zuciyar da ta jima tana dakon soyayyarki!" Idanunta ta rumtse tare da cije laɓɓanta tana mejin kanta na wani irin sarawa tamkar zai fashe, sam bazata iya jurewa ba hakan yasa ta ɗauki hand bag ɗinta, tare da wayarta, ko kallon inda Manager yake bata sakeyi ba ta nufi hanyar fita daga cikin falo, da sauri Raveel dake tsaye yanajin duk abun da suke faɗa ya koma jikin gini ya tsaya, don sam bayaso sugansa harsusan yaji abun da ya wakana atsakaninsu, "Zaleeha! "Zaleeha!!" haka manager keta ƙiran sunanta, ko tsayawa batayi ba balle yasa ran zata juyo ta kallesa, hannayensa ya sanya ya dafe kansa, yayinda soyayyarta ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarsa, itakuwa Zaleeha tuni hawaye sun cika idanunta, kaitsaye wajen motarta ta nufa, tanakai hannunta jikin murfin motar muryar Raveel ya daki dodon kunnenta. Inda yaƙira sunanta, ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi tare da tsayawa cak, saidai bata juyo ba, ajiyar zuciya Raveel dake bayanta ya sauƙe tare da cewa. "Dan Allah kijuyo ki fuskanceni!" "Kafaɗi abun da kakeson faɗa danni sauri nakeyi!" Zaleeha ta faɗa cikin ƙosawa, don gaba ɗaya komai bayayi mata daɗi. "Maganace akan SO Zaleeha, dan Allah Zaleeha ki bani dama, ashirye nake dana zama GARKUWA agareki, zan baki ingantaccen farin ciki me ɗorewa, sannan zan....." "Ya isa haka Raveel, wai me kuka ɗaukenine kowa so! so!! So!!! maikuka maidani ne? shin wai ni kaɗaice mace aduniya? Dan Allah Raveel kafita arayuwata, ka tsaya amatsayinka na abokin aikina kadaina wannan ƙoƙarin na tura kanka inda baka da muhalli awajen!!". Zaleeha ta katseshi tare da faɗin maganan aɗan tsawace. Bata jirayi me Raveel ɗin zai ƙara faɗi ba ta shige cikin motarta, azafafe ta murzawa motar key yayinda ta jata da wani irin speed, ko gama wangale mata gate ɗin bata bari maigadi yayi ba ta danna hancin motar tata waje ranta amatuƙar ɓace. Raveel kuwa idanunsa da ke cike da hawaye ya rumtse tare da juyawa jiki asaluɓe shima yanufi wajen da motarsa take, don yanda yakejin ciwo azuciyarsa bayajin zai iya komawa cikin office ɗinnasu. Ahankali take rage gudun da takeyi, kantane ke mata wani irin ciwo, gaba ɗaya damuwa yayi mata yawa, ɗan lumshe idanunta tayi tare da dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi, kaitsaye Havilla tanufa, don ayanda takejin zuciyarta dole tana da buƙatar abun da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148