Skip to content

Chapter 85

Chapter 85

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

bawa Dr Adnan number shi cewa gobe in sunzo ya shaida mishi. D'akin babba ne mai kyau gadaje biyu ne a cikin d'akin sai kujeru guda biyu ko wanne gado da kujera d'aya, bayan sun gama komai nan suka zauna su dukan su uku Hayatuddeen yana gefen Saifuddeen, Ahmad kuwa yana tsaye gaban Dr Adnan da yake musu bayanin yadda sukayi da Dr da kuma gwoje-gwojen da akayi da kud'ad'ensu. ganin lokacin salla yayi ne sukayi al'wala sannan suka tafi masallaci, sukayi salla magrib nan suka d'an jira lokacin isha yayi, hankalin konce sukayi salla dan sun san akwai masu kula da Saifuddeen. Bayan sun idar sun koma ne suka sameshi kwance amman an d'an d'aga kan gadon in ka ganshi zakace a zaune yake irin ya d'an jinginane, da sauri Hayatuddeen ya zauna gefenshi tare da cewa. "Sannu Hamma Saifuddeen ya jiki?." kanshi ya jinjina alamun da sauk'i sannan ya kuma mishi mgna cikin body language yake tambayarshi ya labarin Ummi. da sauri Ahmad yace. "Ummi tana lfy tace a gaidaka." murmushi yayi cikin jin dad'i sannan ya kalli Hayatuddeen dake cewa. "Bari in kira Raliya video call sai ku gaisa da Ummin." matsowa yayi kusa dashi ya zauna gab dashi kana ya kira Raliya sannan ya kaikace woyar tashi ya matso da kanshi jikin Hamman nashi duk suka fuskanci wayar. A can gida Nigeria kuwa dai-dai lokacin Raliya na zaune gaban Ummi da take ce mata. "Tunda sukaje basu samu damar ganin Dr bama, ni gaba d'aya hankalin na a tashe yake." da sauri Raliya tace. "Yauwa Ummi dama abinda ya kawoni kenan fa yanzu mukayi mgna da Ya Ahmad yace min yau sun samu ganin Dr kuma Alhamdulillahi duk gwajin da ake buk'ata anyi, zuwa gobe sakamakon zai fito." ajiyan zuciya tayi tare da cewa. "Alhamdulillahi." sai kuma tayi shiru jin Raliya na cewa yauwa gama Auta na kirana." da sauri tace amsa kiran." Da sauri tayi picking call d'in murmushi tayi ganin fuskar yan uwanta duk suma suna mata murmushi da sauri ta yunk'ura ta dawo gefen Ummi ta saita fuskarsu da fuskare wayar, suna kallon junansu, wani irin faffad'an murmushi Ummi tayi ganin fuskokin yaranta cikin happy tace. "Alhamdulillahi babana ya jikin?." kai ya d'an rausayar tare da yin yalwataccen murmushi, Hayatuddeen kuwa cikin tankwara wuya yace. "To wai ni kam bakuyi missing na bako kallifa Ummi ko ki kulani ninefa autanki." dariya tayi har saida wushiryanta ya baiyana sannan tace. "Nayi kewarka mana autana." da sauri Raliya tace. "Ni dai banyi kewarka ba dad'i ma nakeji na huta da tattaren kayanka yanzu gidanmu baya hargitsewa tunda ka tafi." dariya yayi sosai sannan yace. "Wayyo yarinya ai in ke kin huta mijinki bai hutaba yaseen watsar da komai nakeyi son raina Ya Ahmad ke tattaremin, Yau da safe harda boxer na ya wonke min da zai wonke nashi." da sauri yayi shiru tare dasa hannu yana shafa k'eyarshi da Ahmad ya bugi yana mai cewa. "Wato kama maidamu bayinka nida matata." cikin jin dad'i Raliya tace. "Yauwa ya Ahmad buge minshi da kyau, kuma ka dena tattare mishi komatsanshi." Saifuddeen kuwa hannu yasa ya jawo kan Hayatuddeen ya manna da kafad'arshi sannan yasa tafin hannunshi yana shafa mishi inda Ahmad ya d'an buge mishi. murmushi yayi tare da cewa. "Kada ya tattara mana ba sai muyi ta zama cikin dottiba." cikin jin dad'i Ummi tace. "Kai Autana ka fara girma fa ka rink'a womke guntayem wondunanka da kanka kaji ko?." kai ya gyad'a mata sannan ya mik'awa Dr Adnan wayar cikin kauda kanshi yace. "Barka da dare Ummi ya gida." sunkuyar da kanta tayi cikin kunya irin ta surkai tace. "Lfy lau Baban Adam ya mai jikin?." A mutunce yace. "Alhamdulillahi Ummi jiki da sauk'i yau mun samu munga likita, nanda kwana biyu za'ayi aiki, ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai samu lfy." cikin samun nitsuwa tace. "Allah yasa." Amin Amin sukace baki d'aya sai kuma tace. "To ni kuma sai yaushe zan zo in dubashi?." Da sauri Ahmad ya koma gefen Adnan d'in kana yace. "Ummi ki kwantar da hankalin ki bari in an mishi aikin munga yanayin jikin sai kizo." shiru tayi kamar dai bata gamsuba sai kuma Dr Adnan yace. "Ki bari sai anyi aikin, dan nima in anyi aikin zan dawo, in yaso in na dawo sai ki zo ko?." a hankali tace. "To ba matsala Allah ya bada sa'an aiki." Amin Amin yace sannan ya kalli Raliya tare da cewa. "Ina Faruq?." a hankali tace. "Yana d'aki wurin Goggo Dada wai sai ta mishi tatsuniya daga nan duk sukayi bacci." "Ki gaida min shi, gobe asabar yaje gida mana yayi hutun sati a wurin Mamanshi." cikin nitsuwa tace. "To ba matsala, ka gaida Hamma da jiki mun gode Allah ya saka ya bar zumunci." Amin Amin yace sannan suka sallami juna. Sosai Ummi ta samu nitsuwa da sukayi hirar. Su kuwa suna gama woyar Ahmad ya gyarawa Saifuddeen konciyarshi, dan ganin ya fara lumshe ido, a hankali Ahmad ya kalli Dr Adnan tare da cewa. "Ya Adnan kuje masauk'inmu kaida Hayatuddeen ku kwana bari ni in kwana dashi, kaje ka samu ka huta." kasan cewar akwai gajiya a jikinshi yasa ya amince, tare suka tafi shida Hayatuddeen shi kuwa Ahmad ya kwana nan wurin Saifuddeen. D'aya gadon ya hau ya kwanta yana kwanciya Bappa Ali na kiranshi wanda shi kuma kawunshi ne yayan mahaifiyarshi da sauri ya amsa kiran. "Salamu alaikum." "Wa alaikassalam." "Ina wuni Kawu Ali." "Lfy lau Alhamdulillahi Ahmad ya jikin Saifuddeen?." "Jiki da sauk'i Kawu yau mun samu munga Doctor." "Eh haka dai Mudassir ke sanar min yanzu wai sunyi waya da Yayanshi Adnan." gyara konciyarshi yayi tare da cewa. "Na kira d'azu ai zan sanar maka to kuma sai naji layin naka baya tafiya." "Eh lallai na rufe wayar ne, na tafi harami shiyasa." Cikin nitsuwa yace. "Kawu Ali sai yaushe ne dawowarku?." "Saura mako guda, kuma in sha Allah ni daga nan saudia zan taho india". "To Allah ya kaimu lokacin ya dawo daku lfy. Kawu Ali a tayamu da Addu'a fa." "In sha Allah, Ahmad zamuyi ta addu'a." Daga nan sukayi sallama, juyowar da zaiyi sai yaga Saifuddeen na rik'e da wayarshi, a hankali ya tashi zaune kana ya mik'e ya taho gaban gadon, lek'a fuskarshi wayar tashi yayi, ido ya lumshe ganin karatun Qur'an yakeyi, sai ya koma konta. Shi kuwa Saifuddeen tunda Ahmad ya gyara mishi kinciyarshi, ya lumshe ido ya fara bacci sai kuma ya fara mafarki inda yake ganin Zaleeha tanata k'ok'arin son ganin fuskarshi daya rufe da tafin hannunshi, shima kanshi ta tsakanin yatsunshi yake gane fuskarta, ita kuwa sai tasa hannunta tana ta son ciro hannunshi daga fuskarshin amman ta kasa d'age hannun nashi, ganin haka sai ta koma gefe ta zauna tanata kuka, daga nan ya farka daga baccin. To shiyasa kawai ya d'auki wayarshi ya fara karatu. Shi kuwa Ahmad Warisu ya kira suka gaisa sannan sukayi saida safe. Ya Adnan da Hayatuddeen kuwa da k'afa sukayi tattaki har cikin Hyatt kasan cewar ba nisa da asibitin. Suna isa Ya Adnan yayi wonka, yana fitowa Hayatudden ya mik'e ya shiga, bayan sun gama shirin baccinsu ne, Ya Adnan ya koma parlour ganin Hayatuddeen

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148