Chapter 24
Chapter 24
kanshiba dan sun sanshi sam baida cin abinci, Warisu ma kad'an yaci ya ajiye spoon d'in sabida baison yayi teb'a suna gamawa suka sha ruwa kana suka fita suka raka Ahmad har shabewa sannan suka dawo, tuni sha d'aya tayi shiyasa kowa ya nufi gida. Yauma da dare kamar jiya haka Ummi ta tashi yaranta, sai k'arfe uku Rahma ta tuk'a musu tuwon shinkafa dama kuma Raihana tayi musu miyar zogale tun da dare. to yau Saifuddeen ya d'anci mai d'an yawa kana yasha tea, suna gama sahur din ya shiga wonka kafin ya fito anyi assalatu, so alwala yayi tasa Hayatudden a a gaba suka tafi, su Ummi kuma sukayi nasu a gida. Ana idar da salla ya fara azkar nashi sai da ya gama sannan ya shiga suka gaisa da Ummi kana ya bata 5k d'innan yace ta sama musu asusu na daban ta rink'a sasu, ita kam Ummi tayi mmkin yawan kudin to ganin yana sauri Salisu na jiranshi yasa ta barshi ya tafi sai ya dawo suyi mgna. Suna isa Salisu ya sauk'eshi a bakin masallacin bakin kasuwan, shi kuma ya wuce kabo-kabonshi. shi kuwa Saifuddeen cikin masallacin ya shiga kamar jiya yayi baccin awa d'aya da rabi kana yana farkawa yayi Al'wala yayi walaha raka'a biyu sannan yayi addu'o'inshi kafin ya fito ya nufi cikin kad'uwa. Yana shiga kai tsaye dilansu na leda ya shiga inda ya samu mutun biyu a gabanshi dole yabi layi, bayan an basu shima aka bashi na 60k Lamar na jiya kenan k'arfe 10:00 Am dai-dai suka bashi nashin, with full confidence ya fara bin layi-layi shago-shago lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya, 1:35 pm ya gama rabawa da yake kusan fiye da rabin kasuwar duk a wurin baba bello suke sayan ledan to shiyasa yake dad'ewa yana yawata kasuwan da k'afa tunda shi bashi da keke kamar baba bello, yana gamawa yazo ya had'a lissafin kud'in ya samu dubu settin da bakwai da dari biyu, cikin aminci ya basu 60k d'insu sannan ya adana ribarshi a jikinshi godiya yayi musu bayan an rubuta ya dawo da kud'in na jiya, tafiya yake yana nazari shifa gani yakeyi kamar kyauta suke bashi kud'in duk da ko azabar nauyin kwalin da yake azawa a k'afad'anshi na dama aikine mai matuk'ar wuya ga yawo cikin rana har ji yake k'afafunshi suna yum-yum dan azaban rana da nauyin kayan da yake azawa a kafad'anshi. Ganin azahar ta kawo kai yasa ya zauna ya d'an huta dan yana jin kafad'arshi na mishi ciwo ga zafin ranan da yabi sai yake jin wani irin azabebben k'ishi , ganin an kira salla yasa ya mik'e yaje yayi al'wala kana ya shiga sahu, bayan an idar ne ya mik'e a gajiye yana tafiya a hankali yaje ya karb'i omo dasu sabulu, sai kuma ya zage da talla dan yanada burin ya maida Raihana da Raliyya makaranta in kes dai ace sun gama koda d'an Secondary school, yana kuma fatan ya ink'anta karatun Hayatuddeen da Faruq da Adam kuma yana fatan Allah ya hanasu sake tsammatan abinda zasuci daga wurin wani. Da wannan tunanin ya zage yaketa yawa tawa cikin ikon Allah ranar ribar 1,200 ya samu. Ganin ya fara ganin jirine ya sashi neman inuwa ya zauna saida ya huta sannan ya maida sauran omon. ganin hud'u da rabi tayi sai yaje shagon ba mishkila gero ya auna mudu shida sai wake mudu shida sai sugar mudu d'aya da rabi, daga nan yaje ya sayi mai k'aramin galam sai ya saya musu lemu da ayaba da kankana, A tak'aice dai ya kashe dubu uku d'ari biyun nan sai dubu biyar ya bari su kuma na sawa a asusune. Biyar na cika Salisu yazo nan suka kama hanyar Dukku, cikin sa'a suka isa da sauran rana. Yauma kamar jiya tare da abokanshi sukayi bud'a baki. ana idar da sallan asham suka tafi tabsir. koda suka dawo suka ci abinci sannan suka raka Ahmad. Yana dawowa ya sumu Ummi a tsakar gida, bisa taburma Rahma na gefenta tana bacci yayinda take ruggume da Adam. gefenta ya zauna ita kuwa Ummi tea ta had'a mishi sannan ta bashi, yana sha ne taje ta d'auko asusun duka biyu yana ganinta da asusun ya d'an kaikaice tare da cusa hannunshi a aljihun wondon Jeans d'in jikinshi zaro kud'in yayi tare da mik'a mata, cikin kula ta amsa kana ta irgasu ganin dubu biyar ne sai ta fuskanci da kyau cikin maganar kurame tace mishi. "Kud'in waye ne." kurb'an tea d'in ya d'anyi bayan ya had'iye ne sai ya nuna mata kanta. fidda numfashi tayi tare da gyara zama dan tasan in abu nashine in ta tambayeshi na waye ne sai yace mata natane haka yasa ta gane kud'in nashine cikin tsoro da tuhuna da gudun masifun zamani wanda dole in kaga d'anka da kud'i ka bincikeshi ina ya samesu a hankali tace mishi. "Ina ka samesu? Me kayi aka baka su? Ya jiya ka samu da yawa yauma kuma gasu da yawa gashi harda su gero naga ka seyo Babana ina tsoro duk da tabbas nasan halinka amman kud'in sunyi yawa." Allah sarki Saifuddeen ganin firgici a fuskarta ya sashi ajiye kofin tea d'in kana ya juyo suka fuskanci juna da kyau, a hankali yasa hannu ya kamo nata hannun cikin sama mata nitsuwa ya mata bayanin komai yadda ya samu kud'in duk da body language yakeyi so Ummi tana bala'i gane body language shiyasa wasu lokutan takanyi mgna dashi cikin mutane ba mai ganewa sai Rahma, sai kuma yanzu sun lura Hayatuddeen ma yana ganewa kad'an-kad'an ajiyan zuciya ta sauk'e lokacin daya gama yi mata bayi, sai tayi murmushi tare da hamdala kana ta godewa Allah, sai kuma ya fara rubutu a gefensu kamar haka. "Yauwa my Ummi ko kefa kada kiji tsoro Saif d'inki da halal zai cigar daku ya shayar daku ya tufatar daku da guminshi." kanshi ta shafa tare da samishi al'barka shi kuwa rubutun ya kumayi. "Amin Amin ya rabbil izzati. Yauwa Ummi batun gero da wake da sugar kuma, a jik'a geron sai a markad'a ayi kamu a rink'a dama kunu kullum da yamma sannan d'auki wake mudu d'aya kullum a surfa ayi k'osai da yamma sai asa a manyan kwanuka a rink'a kaiwa bakin masallaci sadaka, gobe zan sayi dabino a rink'a had'awa da dabinon." Allah sarki Ummi ji tayi tamkar ta ruggumeshi sai kuma taji wasu zafafan hawayen farin ciki, cikin raman murya tace. "Ya Allah ya yimaka al'barka babana Allah ya k'ara maka imani da tausayi ya Allah ya bud'a maka k'ofofin samu mai al'barka in sha Allahu nida kaina zan rink'a wannan aikin har zuwa k'arshen Ramadan su Rahma da Raihana kuma suyi na gida." Wani irin farin ciki yaji yana ratsashi sabida ganin yasa mahaifiyarshi farin ciki. ita kuma cikin bada shawara ko ince neman izininshi a matsayinshi namiji kuma babba tace. "Goggonku Dada ta aiko Ahmad d'azu yake cemin wai dan Allah a bata Raliyya mana taje suyi azumi acan zata d'an taimaka mata da aiki." cikin sanin makamar girma ya rubuta mata. "Ummi in dai kin yarda ba matsala dan na yarda da tarbiyar Goggo Dada, amman ki gayawa Bappa Ali in ya amince ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148