Chapter 105
Chapter 105
turo kekensa har wajen, kasancewarsa bamai cin abinci da yawa bane hakan yasa tea kawai yasha sai kuma chips dayake ɗan tsakala yana sawa abakinsa kaɗan kaɗan, sosai zuciyar ƴan uwansa da Umminsa ke wanke fari ƙal, babu abun dake ɗawainiya dasu face farin ciki da jin daɗi, kasancewarsu da Saifuddeen awaje guda baƙaramin ƙara musu kuzari da karsashi yakeyi ba, basu jima da fara breakfast ɗinba Ahmad da Saminu suka shigo, nan suma suka zauna aka shiga cin abincin tare dasu, duk da cewa suɗin surukaine ga Ummi, amma su jin kansu suke matsayin ƴaƴa awajenta, don sunajin kamar yanda su Hayatuddeen ke ƴaƴa awajenta haka suma suke saboda haka babu batun wani nuƙu-nuƙu agabanta don mahaifiyace garesu a gabanta suka girma tun suna yara har zuwa samartansu sukanci abinci a gabanta a matsayinta na uwa a garesu shiyasa kuma, koda suka auri yaranta tafiyar bata sauya zani ba. Suna kammala cin abincin ne dukansu suka koma falo suka zauna, hira sosai sukeyi yayinda Saifuddeen ke binsu da idanu yana me karantar abun da kowannensu ke cewa, idan na dariyane yakan ɗan murmusawa, ana haka ne Ishaq da tawagar ƙungiyarsu ta Joint National association of persons with disabilities (Jonapwd) Gombe State Chapter. All the best! Suka ƙaraso, nanfa falon Ummi yacika tam da mutane, makafi, guragu, kurame, duk zuƙatansu suka cika da murnar ganin Saifuddeen, Ishaq kam ji yake kamar yamaida abokin nasa ciki saboda daɗi, duk da cewa baya gani amma zuciyarsa ta gamsar masa da cewa Saifuddeen ɗinsa aboki kuma ɗan'uwansa ya samu lafiya, haka Ummi tasa su Raihana suka ajiye abunci da abunsha ga kowanne daga cikinsu, baƙaramin daɗi Saifuddeen yaji azuciyarsa na ganinsu da yayi ba, haka suka kwashe tsawon awanni suna tare da juna, saida akayi Azahar ne Ishaq ya tattarasu duk suka koma. Adda Rahama da Dr Adnan da Baba Bello haɗi da goggo mahaifiyarsa ne suka zo, suna zuwa babu jimawa kuwa saiga mutanen dukku wanda suka kusa cika mota suma sunzo don duba jikin Saifuddeen ɗin da kuma taya Ummi murnar dawowarsa, nanfa gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a. Da yamma kuwa Alhaji Sani da Alhaji Kabiru da kuma Alhaji Sulaiman mahaifin Hisham da Alhaji Adamu yayan Jabeer sukazo duba jikin Saifuddeen ɗin, sosai ƙwarai yaji daɗin ganinsu, suma sunji daɗi sosai da suka tararda jikin nasa da sauƙi, nan suka ɗan taɓa hira inda kowanni magana da body language sukeyi idan basu gane ba kuma yakan rubuta musu awayansa sai ya basu su karanta, sosai suka ɗansha hira kafun daga bisani sukayi masa sallama, koda sukazo tafiya al'khairi me yawa suka bawa Ummi don sunsan idan suka bawa Saifuddeen to ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai amsa ba, awajen Ummin ma kuwa ba tsira sukayi ba don kafewa tayi tace bazasu amsa ba, da ƙyar Alhaji Sani yasanya Ummi ta amsa, inda yayi mata tuni da cewa bakyau maida hannun kyauta baya. Badon Ummi tasoba haka ta amsa kana tayi musu godiya. Wayar Hayatuddeen dake aje kan kujeran falonne kete tsuwa alaman shigowar ƙira saidai hartayi ta katse ba'a ɗauka ba, wani ƙiranne ya kuma shigowa, Hayatuddeen dake cikin kitchine ne yafito da gudu hannunsa ɗauke da wani dogon tsinke wanda jikinsa ke saƙale da gasashshen nama sai tiriri yake da'alama yanzu aka gasa naman, saura ƙiris wayan ta tsinke ya ɗauka tare da karawa akan kunnensa, cikin yanayi na ɗan faɗa tace. "Saikuma kaga dama ne kafun ka amsa wayana?" Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa. "Yi haƙuri Likita ina kitchine ne". Murmushi Amina dake zaune akan kujera tayi tare da gyara zamanta cike da kulawa tace "Kwaɗayayye kawai, meya kaika kitchen?." hyyy yayi dan zafin da yaji lokacin da ya kai bakinshi kan sokan nama daketa tiriri, jin tana mishi dariya ne ya sashi cewa. "Nama ne Ummina ta gasa min, shine nake d'an tab'i." Kwaffa tayi tare da cewa. "Ni bawannan ba yajikin Hamma Saifuddeen?". "Eh dai naji, jikin Hamma Saifuddeen da sauƙi sosai, don yanzu haka ma muna gida, da jiya kika ƙira ma wataƙila da kinzo kin dubashi don muna Abuja" Idanu Amina tazaro tare da cewa. "Wai kana nufin ya tabbata kun dawo Nigeria? kuma ma wai har jiya kun sauƙa Abuja shine baka ƙirani kasanar dani ba?" Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa. "Ga zahiri kuwa muna mgna da number ta na Nigeria." Cikin jin haushi tace. "Tun shekaran jiyan can nake kiran number ka ta Indian bata shiga, sai kawai yanzu kamar da wasa nace bari in gwada mtn naka. kuma sai ya shiga, gsky Hayatuddeen baka kyauta min ba wlh." cikin tauna naman yace "Tuba nake Likita, ai bansan kina da buƙatar ganin kyakkyawan Hamman nawa ba!" Cikin haushin rashin sanin dawowarsu da batayi ba tace "Harsai na faɗa mane sannan zaka sani, nidai ba wani nan munyi faɗa". Dariya sosai Hayatuddeen yayi tare da cewa. "Kiyi haƙuri bokan turai!". "Nidai ai nace maka munyi faɗa ko". tana gama faɗan haka ta kashe wayarta, dariya sosai Hayatuddeen yayi, Ummi dake tsaye abayansa ne ta ƙaraso cikin falon, dubansa tayi tare da cewa. "Kai kuma kaida waye kake waya haka?" Murmushi yayi tare da cewa "Amina ce fa Ummi wannan nurse ɗin da ta kula da Hamma Saifuddeen lokacin da muke Abuja, to shinefa yanzu da ta ƙira nake shaida mata dawowar mu shine wai ita tayi fushi da har jiya muka sauƙa a Abuja ban gaya mata ba taje ta duba jikinshi". Murmushi tayi cikin tsananin jin dad'i tana matuk'ar son duk wani maison Saifuddeen d'inta, murmushin kawai Ummi ta kumayi tare da zama akan kujera kana ta maida hankalinta ga TV inda sunna tv ke haska wa'azin Malam Isah Ali Pantami. Yau tunda tazo wajen aikin nasu fuskanta aɗaure yake tamau, sam takasa sakin fuska ga kowa wanda hakan ya matuƙar bawa abokan aikinta mamaki, don kuwa sunsan bahaka take ba ita takowace sannan itaɗin me yawan fara'a ce saɓanin yau da suka ga ta tsuke fuska, fitowarta daga ɗakin gabatar da shirye-shirye kenan inda ta gabatar da shirinta na mushaƙata, kaitsaye ɗakin hutawansu ta nufa inda anan tabar jakarta harma da wayarta. Koda ta shiga cikin ɗakin kan wata kujera ta zauna tare da ɗaukan jakarta, zip ɗin ta zuge kana ta ciro wayarta, 4 missed call ta iske acikin wayar wanda kuma duk daga Abdussalam ne, tsuka tayi tare da kunna data'n wayarta ta shiga Instagram, Raveel ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, can ƙasan maƙoshi ta amsa masa sallaman batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba, asanyaye ya tako ya ƙaraso zuwa inda take, kan wata baƙar kujera dake facing wanda take ya zauna murya asanyaye yaƙira sunanta "Zaleeha!" Bata amsashi ba haka kuma bata ɗago kai ta kalleshi ba, ganin haka yasanyashi sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗan langwaɓar gefe guda cike da tsananin shauƙin mayen soyayyarta yace. "Dan Allah M B S Dukku ki saurareni mana, ashe shikenan don zuciyata ta kamu da soyayyarki tayi laifi? Dan Allah Zaleeha kiyi haƙuri ki fahimci irin sonda nake miki, wallahi inasonki ina miki son da nikaina bansan adadinsa ba, rasaki dai-dai yake da daiɗaicewar tunanina Inasonki Zaleeha, dan Allah ki Amshi soyayyata!!" Tsananin rauni da damuwar dayake cikine ya bayyana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148