Chapter 44
Chapter 44
waec da Neco to dole akwai kashe kud'i." Rahma ce ta fara yin Magna cikin jin dad'i tace. "Alhamdulillahi burin Ya Seyo zai cika, yayi kyau naji dad'in haka." Ummi kuwa cikin sanyi tace. "To ya zakayi da kasuwancin naka kuma?." kai ya jinjina tare da cewa. "Raba leda ba wuya cikin awa uku ana hud'u nake gamawa, sannan akwai uzuri tsakanina da abokan kasuwancin na in banje bama ana rabamin kinga kwanaki da banda lfy ma Jabeer ne ya rarrabawa costumes d'ina, kinga duk lakacin da bani da darasi inada damar kasuwanci na, sai dai cinikin pure water dasu omo nane zaiyi k'asa." cikin bada k'arfin guiwa bappa Ali yace. "Hakan yayi Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a. ni kuma in sha Allah daga gobe zan fara d'aukan Warisu zan fara nusar dashi da koya mishi harkan awu da sanar dashi farashin sari da sayan d'ad'd'aya, dole in koya mishi awun kanshi gudun kar yaje yayi ta tauye mudu." sosai dai suka zauna suka tattauna yadda komai zai tafi, shi kuwa Saifuddeen dubu d'ari ukun ya ware kana ya d'auki na saman ya rabawa Ummi da Bappa Ali dubu goma-goma, ya bawa su Rahma da Aunty Nina dasu Raihana dubu biyar-biyar, Su Warisu, Saminu, Salisu, Ahmad Mudassir, kuwa duk suma dubu biyar-biyar ya ware musu shi kuma yasa saura a al,jihunshi. da zummar zai bawa Jabeer da Hisham dubu biyar-biyar sai ishaq inshi dubu biyar shima. Inda yasan machine bajat zataci kusan dubu d'ari da ashirin, saura kuma zai ajiyesu dan hidimar karatunshi. Da haka dai sukayita hira sai har kusan shabiyu na dare sukayi saida safe kana duk suka mik'e kowa yayi makoncinsa zuciyarshi cike da farin ciki. Washe gari kamar yadda suka tsara hakan Saifuddeen yayi ya tallatawa su Alhaji Kabiru Maggi ba musu kuma suka amince dan ai sune da riba mai yawar, yayinda Alhaji Sani kuma yaketa taraddadin shigo da yaron cikin harkarsu a cewarshi karfa ya lalata musu kasuwa so amman ya amince da tsarin, nan take suka buk'aci daya basu account number inshi, Allah sarki Saifuddeen sai yau ya tuna da wata abba tashi account number shi dan shi tun last year bayan s Ya Rabi'u ya aiko mishi woya da ishaq ya matsa mishi dole sukaje suka bud'e account number d'in da shi a lokacin yanaga account d'in baida wani amfani, dan babu ko sisi a ciki in bada wanda ya bud'e dasu babu ko asi a ciki dan shi lokacin yafi ganewa asusunshi, murmushi yayi jin dad'in ya haddace komai na account d'in a kanshi, nan take ya basu account number, inda sukayi sallama da cewa sai gobe zasu tura mishi, inda sun saye kashi biyu cikin kashi uku na kayan. Daga wurinsu kuwa wurin Bello ya nufa na shagon ba miskila nan yayi sa'a ya samu ogon nasu ya mishi bayanin komai, cikin farin ya amince nan take suka tsadance suka kuma ajiye farashinsu dai-dai dana juna, inda ya koka mishi da zai samu yana son ya ara mishi d'aya daga cikin yaran shagonshi dan yaje ya kyautata awun yaran shagonsu tunda su sabbin shigane, cikin aminci da mutunci da kamala da cikar imani ba kyashi bare hasada ba miskila ya amince inda yace Bello zai koma ya kula da lamarin shagon su Saifuddeen nan ya gayawa Saifuddeen farashin yadda yake sallaman yaran shagonsu a kullum da kuma k'arshen wata, shima Saifuddeen ya amince duk da yawan kud'in yasan wannan shine adalcin da ubangida zaiwa yaran gidanshi gudun kada su zama masu zagon k'asa. Daga nan ya shirya yaje makarantarsu yayi cuku-cukun komai daya dace dan ci gaba da fafutukar neman damar shiga jami'ar G.S.U. Shi kuwa Bappa Ali a ranar ya fara nunawa Warisu harkan kasuwancin inda yaji dad'in haka sosai, dan ko ba komai zai samu damar kula da kanshi da ah'linshi. Washe gari kuwa saiga Saifuddeen yanata ganin ruwan miliyoyi a account number inshi, wanda Alhaji Sani Da Alhaji Kabiru da ba miskila suka turo mishi, a ranar su Alhaji Kabiru suka kwashi kayan maggin da suka sara a wurin Saifuddeen suka kai sito insu. Bappa Ali kuwa ya nemi akori kura guda biyu yasa aka lodawa ba miskila kayan daya sara a d'aya motar, d'ayar kuwa yasa aka loda wanda zasu ajiye a shagonsu, nan aka tafi da Warisu da Bappa Alin bayan yan gama sassauk'e kayan ko wanne an ajiyeshi a muhallinshi, sai Bello da da Warisu da Bappa Ali suka tare a shagon su Ssifuddeen d'in nan suka k'ara kimtsa komai sannan bappa Ali yayi musu nasiha da suji tsoron Allah su kyautata awun mudunsu, nan kuma sukayiwa shagunan layinsu ihsani da kayan abinci dama duk wanda yazo gilmawa ta gaban shagon nansu, hakan yasa a take duk layin nasu suka san da shagon dan sanadin bada ala koron. Wasa-wasa kasuwa dai nata d'an tafiya, sai dai yawanci masu sarine ke saya, dan masu sayan d'ad'd'aya basu fara sanin shagonba tukun, tuni kuma masu dattin zuk'ata sun fara suka suna wani cewa. "Yoh aiyi dai mu gani, nanda yaushe wai maye yayi amarya tuni zai lamushe abarsa, sabida wasun gani suke Saifuddeen yazo da wani salo na kashe musu kasuwa da hanasu riba mai yawa, to dama in ubangiji yayi niyar d'aukaka d'an adam a bakin masu hasada zai d'aukakashi tuni masu hasadan dake k'ananun Magna ne yasa kasuwar gombe ta cika da batunsa inda kamar da wasa suka rad'awa shagon dama layin suna wai , *ALHAJI BUTU* wai alhajin araha kenan, abu kamar wasa sai ga sunan shagon dama layin ya zauna hakan. Cikin mako uku kasuwanci yaci gaba da gudana, yayinda Ssifudddeen kuwa har yau bai fasa tallan ledanshi dasu omoba, ana kuma ta shirye-shirye fara WAEC. Sun gama zana exam d'in WAEC, hakama NECO tuni kuma ya zana JAMB inshi bayan wasu makonni sakamon jarrabar na Jabm ya fito inda ya samu 220 kuma Alhamdulillahi waec da neco d'inma result yayi kyau matuk'a gaya. Bayan wata hud'u, tuni Saifuddeen ya samu nasarar zama cikekken d'alibi a Gombe state university. Warisu da Bello kuwa sosai kasuwa take tafiya dai-dai da yanayin cinikin sabbin shaguna masu araha, a dai-dai lokacin ne kuma komai na kayan abinci ya dawo gida a hannun manoma, tuni masu hannu da shuni sun fara rige-rigen saye kayayyakin abincin dan b'oyeshi sai yayi tsada su fiddoshi. A kuma dai-dai lokacin ne company layin Mtn suka kuma biyansu kud'in hayan filinsu da suka kafa services nan suka had'a kud'in suka rub'anya jarin kayayyakin abinci da bappa Ali zai sararo musu. Kamar bara haka banama bappa Ali da Saifuddeen sukayi, bayan sun harhad'a cinikinsu suka ware asalin uwar kud'insu sannan suka ware tarin ribar da suka samu na gefen maggi da kuma sauran kayayyakin abincin da kud'in hayan fiinsu Alhamdulillahi kasuwa kuwa tayi Al'barka dama ance kad'an mai al'barka yafi mai yawan da akasa dan zalumcin, ware kud'in sukayi na maggin jarin da ribar wanda ya basu million uku , sai suka rabasu suka kuma saran maggi million biyu, sannan suka d'auki million d'aya suka sari 'yan kayayyakin masarufi kamarsu, spaghetti, macaroni, indomi, sugar, fulawa, da buhunan madarar awu ajiniyo moto, suka had'a da sarin maggin nasu. Sai kuma suka had'a jari da ribar kayan abincin dana hayan bappa Ali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148