Chapter 7
Chapter 7
hawaye, hakan mutumin nan tunda aka gaya musu ya zame a wurin ya zauna bisa kujera yana kuka mai ban tausayi yanayi yana tasbihi da hailala, sabida hankalin shi yayi matuk'ar tashi tunda yasan shine sanadin mutuwarshi. Bayan an d'auki gawar an kaita macuwari, su kuwa duk su uku sai suka nufi masallacin dake cikin asibitin bayan sunyi al'walane suka fara nafifili da k'auna Qur'an tare da yimishi Addu'a. Koda gari ya waye mutumin nan yayi duk kan abinda ya kamata kafin a basu gawan, Aka yi mishi wonka aka shiryashi kamar yadda musuluncin ya tanadar mana, bayan an gama kimtsashi ne, suka barshin nan cikin asibitin tare da Adnan kana shi kuma ya d'auki bappa Ali ya nufi gidanshi dake Fantami, nan ya sanar musu abinda ke faruwa, kana ya fara gaiyatar jana'izar, bayan ya gama abinda ya sauwaqa sai kuma suka nufi Dukku. Suna isa sukayi cikibus dasu Saifuddeen da Ummi da suke shirin tafiya yanzu. ganin Bappa Ali da wani mutum a cikin zazzafar mota yasa zuciyar Ummi karaya, sai tayi maza ta koma cikin gida, yayinda Saifuddeen kuma ya zubawa Bappa Ali idanu tamkar zai mannasu a jikinshi duk sun kasa yin Magna tuni mak'ota sun taru a wurin anata tambayar jikin Nuruddeen, amman ba mgna Bappa Ali sai jujjuya kai yakeyi yayinda mutumin nan kuwa yaketa zubda hawaye, ganin haka duk aka gane cewa Nuruddeen baya raye. Ita ku Ummi tana shiga cikin gida da sauri Rahma dasu Raihana sukace. "Ummi meya faru." duk da taji abinda sukace amman ta kasa mgna sai nufar inda Abba ke zaune tayi yayinda shi kuwa yayi mutuwar zaune, cikin rawar murya tace. "Bappan Saifu ne ya dawo shida wani mutum." wani irin zabura Abba yayi sai ya kuma koma ya zauna da sauri sabida azabar da yaji mak'ogoronnshi na mishi. Dai-dai lokacin kuma Bappa Ali da mutumin nan suka shigo, gefen Abba suka zauna kana Ummi kuwa ta matsa can gefe ta zauna bisa kujera yar tsuguno gaba d'aya jikinta tsuma yake zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, shi kuwa Abba ido ya zubawa mutumin da ya tasashi gaba yana kuka da shesshek'a a hankali, cikin firgita da rauni murya can k'asa Abba ya kalli k'anin nashi da matarshi da yaranshi baki na rawa yace. "Innalillahiwa Inna'ilaihi rajiun." sai ya kuma rumtse idanunshi wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo mishi masu tsananin k'una murya can k'asa yace "Mutuwa ta barni ta d'auke Seyo na ko?." cikin zubda kolla bappa Ali ya gyada mishi kai, ido ya rumtse kana yayi murmushi tare da cewa. "Hmmm Seyo na ya tafi ya barni! nasan nima bazan kai bad'i iwar hakaba, zan bishi zanbi bayanshi, Aliyu na tausaya maka zan tafi in barka da nauyi, Saifuddeen zai d'auki nauyin da shekarunsa basu kai ya d'aukaba." kawai sai suka had'e kai suna kuka, hakama su Raihana da Raliyya da Hayatuddeen Amman Ummi da Saifuddeen da Rahma sun gaza kuka domin ance wani zafin ya wuce inda hawaye yake. Mutumminan kuwa shima kuka yakeyi cur-cur da hawayenshi yana basu hak'uri. Ita kuwa Ummi wani abu mai tsananin k'arfin taji ya tsoki k'afon zuciyarta ya danne kukan da takeji tana son yi, hakama Rahma sai d'anta Faruq daya tasa a gaba yana kuka ita kuwa sai dafe zaciyarta dake barazanar tarwatsewa tayi kana zuba musu idanu tamkar zautacciya. Aunty Nina kuwa matar bappa Ali fargaba yasa cikin jikinta b'arewa. Saifuddeen kuwa Allah ne kad'ai yasan abinda yakeji a ranshi, in ya kalli Ummi da Rahma ji yakeyi tamkar zai fad'i ya mutu dan tsananin zafin da k'una da zuciyarshi ke mishi. shi ko Abba yunk'ura yayi a hankali ya tashi kana ya kalli k'aninshi yace. "Ina gawar take?." cikin tausayawa mutumin nan ya mishi bayani kana duk masu zuwa jana'iza a dauko motocin a tasha ya biya kudinsu, nan aka dugguzuma aka nufi Gombe. bayan sallan azahar aka sallaci gawar, sannan akaje aka binneshi, motocin nan suka jidi mutanen Dukku suka meda su, kafin su dawo duk yan uwa da abokan arzik'i an hallara tuni Goggo Dada ma da tazo, dama Ahmad da babanshi kam dasu akaje gombe. Nan sukayi zaman makoki na kwana bakwai, mutumin nan shima yayi zaman makoki a gidanshi na tsawon kwana uku,randa akayi sadakan bakwai yaje Dukku ya k'ara basu hak'uri, nan sukace sun yafe, domin k'addarace ta rigayi fata sannan shi kuma yayi musu al'khairi sosai dan harda kayan abinci ya kawo musu tuni kuma ya fara azumi settin d'in da zaiyi. Rayuwa dai taci gaba da tafiya a haka. Yau da dad'i gobe akasin haka. Abu da dama ya faru cikin watanni ukun nan. Bayan wata uku Ranar wata asabar bayan sallan magrib, duk suna tsakiyar gida, Ummi ta tasa Rahma dasu Raihana da Raliyya suna d'an hira, Saifuddeen kuwa da Hayatuddeen suna gaban Abba. mik'ewa Abba yayi kana ya kalli Ummi da yaranta da suke shawarar a saida kayan d'akin Rahma a kaishi asibiti ai mishi aikin mak'ok'on . murmushi ya d'anyi kana ya d'auki butar dake gefenshi tare da nufar hanyar ban d'aki yana mai ce musu. "Uhumm Rahma kenan, kada ku yarda ku saida wani abunku a kaina fa, domin wannan ciwon nawa tabbas wata rana shine ajalina." d'an tsayawa yayi jin Rahma na cewa. "Dan Allah Abba kayi hak'uri mu kaika asibiti, bazamu iya ganinka hakaba." murmushi ya kumayi kana yace. "Rahma iyayena mafa haka sukayi ta nema min mgni k'arshe har suka rasu ban samu lfy ba, hakama k'annena gaba d'aya Ali ya saida gonakinmu da filayanmu na gado, a kan nema min mgni yanzu du-du du gonaki ukune suka rage sai wannan filin da ke can bayanmu wanda shi kuma dama nine na sayeshi da sunanku. dan haka ku dena wahal da kanku ai sauk'in yazo." yana fad'in haka ya juya ya nufi bayan gidan, a dai-dai bakin k'ofar ya fad'i. Wanda kafinma a d'agashi ya cika. Wannan rana anga tashin hankalin wannan ahlin, dole Abba kwanan keso yayi, washe gari da hantsi akayi mishi sutura, wanda tuni k'ofar gidansu ta cika da al'ummar annabi. Bayan an mishi sutura an kimtsashi kamar yadda musulunci ya koyar damu anzo za'a d'auki makar ne za'a fiddashi. da sauri Bappa Ali ya kalli Saifuddeen daya rik'e makarar yanayin wani irin kukan da yasa dukkan bani adam dake wurin zubda zazzafan hawaye, tuni shima Bappa Ali sai ya zame kana ya ruggumi Saifuddeen da Hayatuddeen dake ruggume dashi, kuka sukeyi wanda duk kan mai imani zai tausaya musu. shi kam Saifuddeen duniya ta mishi zafi ji yakeyi tamkar bai tab'a farin cikiba, fata yake inama shima mutuwar tazo ta d'aukeshi. tausayin kanshi da mahaifiyarsu da k'anneshi da yayarshi yakeji tamkar zai d'auke numfashi sa. Man Liman ne suka janye bappa Ali kana Baba Hamisu yasa hannu ya janye hannun Saufuddeen daga rik'on da yayiwa makarar. Baba Ashiru kuwa da wani abokinshi wanda kuma malamin islamiyarsu Saifuddeen ne sune suka kamashi ganin yanayin da yake ciki, cikin sanyi Baba Ashiru ya cewa Hayatudden. "Deen je ka kawo min ruwa. cikin kuka ya mik'e kana ya kawo ruwan amsa yayi kana ya kalli Saifuddeen da idanunshi sukayi jazir tamkar zasuyi aman wuta, ganin bazai k'arb'a bane yasa Malaminshi amsar ruwan ya kai mishi har baki, kana cikin sanyin murya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148