Skip to content

Chapter 74

Chapter 74

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 18* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 _Free page hmmm sunfa kusa ƙarewa yaseen gwara ka/ki biya yafi miki, kada kuyi shagala da free page wasan yanzu aka fara, somin taɓine. Daga yawan page ɗinma kunsan labarin mai tsawone shiyasa nake inƙanta yawan pages sabida rage muku zaƙuwa, biya ɗari uku kacal dan samun damar karantashi har ƙarshe._ *Turo katin mtn ta wannan no 09097853276. Ko ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ku turo shaidar biyan naku ta wannan no 09097853276* Sai ta kuma yi saurin sa hannu ta rufe bakinta dan ganin yadda ya had'e fuska kana ya tsareta da kyawan manyan idanun shi, had'iye mgnar tayi kana ta fara b'allo magungunanshi tare da fara yi mishi nuni da wai zata bashi mgnani. hannunshi ya mik'a mata ganin haka ta bashi maganin. Bisimillah yayi a ranshi kana ya afasu cikin baki sannan, ya kuma mik'o mata hannu da sauri ta bashi goran ruwan mai sanyin dake hannunta, amsa yayi ba tare daya kuma kallontaba, ya had'iyi maganin, tare da shanye rabin ruwan dan bin shawarwarin da doctors suke bashi na ya yawaita shan ruwa, a ranshi yake cewa. "Fitsararriya kawai mai kwaɗayin tsiya." ita dai sai kallon saitin mararshi takeyi da alamun tsoro, ya fahimci tsoro ne yasa taketa mishi kallon kurillah. Tsuke fuska ya kumayi tare maganar zuciya, "Ganta kamar mayya, wannan kallo kamar zata cinye min Saif ɗina, ja'ira to wannan dai nan gani nan bari." A zahiri kuwa, hannunshi ya d'ago kana ya had'a yatsunshi biyu dogo na tsakiyar nan da babban yatsarshi ya murzasu suka bada sautin. Tab-tab!! da sauri ta juyo ta kalli fuskarshi. dan tayi nisa da kallon haƙilo da takewa sashin lafiyarshi na inƙarman na miji mai cikar zarra, hannunshi ta zubawa idanu wanda yaketa yimata nuni data fita, ba musu ta kama hanyar fita baya ta ajiye magungunan har taje bakin ƙofa ta kuma juyowa ta kalleshi a hankali tace, "Uhummmmmmm to wai wannan da yana lfy kuma ya yake?." sanin ba amsa yasa ta fice tanata zancen zuci. Shi kuwa Hamma Saifuddeen tsaki ya ja tare da da had'e hak'oranshi, duk duniya babu matar da ta tab'a ganin tsiraicinshi tunda akayi mishi kaciya ya worke lokacin yana d'an shekaru shida, koda Ummin shi da Aunty Rahma basu kuma ganin tsiraicinshi ba, sai wannan yarinya rana tsaka. Wani d'aci yakeji zuciyarshi na mishi tunowa ita gani tayi bai mance Zaleeha ba lokacin da ta lab'e bayanshi ta kama kugunshi lokacin da taga wadannan y'an daban sunyi kansu da makamai, ido ya kuma rumtsewa jin yadda tsikar jikinshi ya mik'e tuno a lokacin tasa hannunshi ta zagaye konkosonshi tana k'ok'arin janshi garin zame hannunta ta shafa sirrinshi ta had'a da ƙugunshi ta riƙe abinda da babu wata d'iya mace data tab'a ko ganinshi bare ta shafa, tun daga wannan shafar da tayi mishine kuma wata azabebbiyar kasala ta rufeshi mood nashi ya canza yaji wata iriyar fitinar da bai tab'a jiba a iya tsawon rayuwarshi hakanne ya bawa yan kalaren daman yin nasara a kanshi. cikin ranshi yake cewa. Da a iya zatonshi shi baida cikekkiyar zarra tunda ko azumi yayi Saif ɗinshi koma yakeyi ya ɓuya, haka kuwa in yayi aikin wahala kaɗan abin kan noƙe, sai randa ya fara ganin laɓɓan Zaleeha a tv ne ya fahimci waye shi, sai kuma gashi daga taɓashi sau ɗaya da tayi har yau bai kuma konciya ba, a ranshi yace. "Ya Allah ka sauk'ak'amin k'addarorina daga wannan ta tab'a sirrina sai wannan taga matsayina. Yarinya har ta fara cemin jarabebbe, ko jarabar uwar mi na mata? alhalin ita keta kallona kamar ta cinyeni ɗanye." sai ya kuma bud'e ido tare dayin mgnar zuciya. "Zaleeha ce sila da bata tab'ani ba da bazan rink'a d'imaucewa ba duk sanda na tunota." ido ya kuma rumtsewa yanaji bayanshi kamar ba'a jikinshi yakeba. Ita kuwa Amina tana fita tayi kicibis dasu Ummi da Dr Batulu tayiyo musu jagora da suka fito office d'in Dr Aliyu, cikin girmamawa ta gaidasu kana ta wuce, su Kuma sukayi ciki. Zaleeha da Ya Ahmad d'inta da Mamy da Mama dasu Habu wanda yayan Zaleeha ne kana sai maryam yayar Zaleeha wacce tazo da mijinta Aminu wanda d'an bappansu ne yayan Baba malam, duk sun nitsu sunyi shiru, shi kuwa Baba malam cikin cikar haiba da dottaku da nitsuwa da kamala irinta manyan mutane wadanda suka wadatu da ilimin addini, ya fara yi musu addu'a kana yayi musu nasiha mai ratsa jiki sannan ya d'aura da cewa. "Alhamdulillahi duk kunsan sanadin zamannan namu tunda kukaga mun zauna zaman jiran Zaleeha." gyad'a kai sukayi baki d'aya sai Aminu wanda da ka ganshi kasan irin mutanen nanne masu zafi da tsauri fuskarnan tashi tana had'e sai harara yake cillawa Zaleeha k'anwarshi d'iyar Bappanshi k'anin mahaifinshi wanda suke uwa d'aya uba d'aya, kana k'anwar salihar matarshi Maryam. Ya Ahmad kuwa tonk'oshe kafafu yayi cikin tsanin girmamawa yace. "Na'am". Alamun suna jiran umarni ko shawara daga mahaufin nasu. Shi kuwa Baba Malam, Malam Bashir Sulaiman Dukku kenan, gyara zama yayi tare da cewa. "Dama ta k'arshe zan baiwa Zaleeha wanda zan ninka mata da damar dana bata, wata shida baya, nace ta fito da gwoninta, na bata dama tayi zab'inta duk da shariya ta bani dama in zab'a mata mijin danaga ya dace a matsayinta na budurwa ni kuwa mahaifinta, to amman na bata dama zan kuma k'ara bata dama na k'arshe kada ita da mahaifiyarta suyi zaton bani basu hak'k'insu,." sai kuma ya tsagaita kana ya kalli Mamansu Zaleeha wacce fuskarta ke had'e kauda kai yayi tare da cewa. "Halima ki shawarci d'iyarki data fidda goninta cikin masu sonta, nanda tsawon shekara guda, na bata wannan damarne sabida ina sane da k'orafin da kikayi tayi a auren Maryam cewa nayiwa yarki auren dole kika rink'a zugata data bijirewa zabin da ni nayi mata, sai nayi dacen Maryam salihace muminace mai biyeyya a gareni, tabi zabina ta watsar da mummunar shawarar da kike bata ta ruggume aurenta tayi biyeyya ga mijinta d'an uwanta." sai ya kuma kalli Maryam wacce yasan duk yayanshi daga Ahmad sai ita basa son duk wani abu da zai bata mishi rai bare ya zubda mutuncinsa. Cikin taushin lafazi yace. "Allah ya miki Al'barka Maryama ubangiji ya sa yaranki su miki biyayya fiye da yadda kikayi min, Allah ya saka miki da jannatul firdausi." "Amin Amin ya rabbil izzati ngd Baba Malam Allah ya kara nisan kwana". Cewar Maryam kana duk parlour suka amsa da Amin, Ita kuwa Mama sai k'ara had'e fuska tayi, itako Zaleeha sai k'ara sunkuyar da kanta ta kumayi, gyaran murya Baba malam ya kumayi sannan yaci gaba da cewa. "Zaleeha ki fito da zab'inki cikin watanni goma sha biyun nan, ki fara lissafi tun daga yau d'in nan yanzun nan kuma, kinga dai a baya na baki wata shida, shiru baki fidda mijiba, to ki sani muddin kika cika wa'adin da na baki baki fidda mijiba, toh zab'i ya dawo gareni, duk wanda naga dama shi zan aura miki, domin nasan, baki rasa ma nemaba, amman kinyi burus da zancen, kinasa ana nunani in na wuce ana cewa shine babanta, ai yar malami ne, wasu na tuhumar to

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148