Chapter 108
Chapter 108
hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance, cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo". Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace. "Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?". Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce ne". Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon, da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa. Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu, cikin had'e fuska yace. "Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?." ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido. cikin yin rau-rau da ido tace. "Ya Habu bazan sake ba." kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida. Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi. Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan. Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot, daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta. Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta, addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon, mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!". Murmushine yafaɗaɗa akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace. "Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?". Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani. Yau da wani Gurgu zata gudanar da shirin nata don haka tuni ta tafara ƙoƙarin soma yi masa tambayoyi kamar yanda tsarin shirin nata yazo dashi, ko mintu 10 ba ayi da fara shirinba a hankali taji wani irin ni'imtaccen iska na ratsa ko ina dake jikinta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta, lumshe idanunta tayi sakamakon wani irin daddaɗan ƙamshi da taji ya ratsa cikin hancinta ya kuma cakuɗa da numfashinta, wani irin mimmiƙewa taji tsikar jikinta nayi, wani irin sanyi me daɗine taji yana kusanto ta tamkar wanda ake hurosa, hakan yasanya akasalance ta kai dubanta ga inda takejin kamar tanan sanyin ke fitowa, dai-dai lokacin shikuma ya shigo cikin wajen, zaune yake akan kekensa fuskarsa na fitar da annuri haɗi da ƙyallin kyau sajenshi yayiwa fuskar k'awanya mai jan hankali. Wani irin duka da harbawa zuciyar Zaleeha tayi, yayinda ta kafesa da idanunta masu rikita maza, cikin nutsuwa yake sarrafa kekennasa wanda kuɗinta kaɗai ya isa yasai wani gida, sam ya kasa ɗauke kyawawan idanunsa daga kan kyakkyawar fuskar da yajima yana bege dason gani, wani irin yawu Zaleeha ta haɗiye wanda ya tsaya mata amaƙoshi, zata iya rantsewa bayan mutumin daya taimaketa bata taɓa ganin wani kyakkyawa aduniya ba bayan wannan mutumin dake zaune akan kekensa in dai ido da idone, cikin tsananin dauriya da kama ajinta bawai don ta ƙoshi da kallonsa ba ta kawar da idanunta gefe, ƙarasowa cikin babban falon yayi tare da tsayawa adai dai inda Ishaq ke zaune, A fakaice ta D'angelo kalle fararen yatsun hannunshi da yaketa musabaha da mutanen nasu da suka kewayeshi tamkar sarki a fadarsa, ƙamshinsa kaɗai yasanya Ishaq ganesa, nan ya ɗauki wayarsa ya rubuta masa saƙo kamar haka. "Gafa Zaleeha nan tana gudanar da shirinta wani sati dakai za ayi". Murmushi kawai Saifuddeen yayi tare da yiwa abokin nasa rubutu inda yace. "Allah ya kaimu," kana shiko Ishaq ya gyara zama tare da cewa. "Zaleeha ga aboki na kurman da na tab'a gaya miki naje Indian dubashi da jiki." ba tare da ta kalleshi ba tace. "Ayyah." Shiru yayi tare da kafeta da idanunsa kowani motsi da zatayi tare da bugun zuciyarsa yake tafiya amman da yake ya iya sarrafa kanshi babu mai ganewa sai ita da takejin kwayar kekyawan idanunshi na yawa a surar jikinta. Hakan yasa gaba ɗaya nutsuwarta ce tayi ƙaura daga jikinta, cikin rashin kuzarin dayazo ya lulluɓeta haka take gudanar da shirin, ɗan ɗago da mayan idanunta tayi da niyar satan kallonshi karab idanunsu suka haɗe dana juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, sakamakon wani irin shock da taji acikin jikinta, gaba d'aya taji wani abu na dark'efe kwayan idanunta, bayan kamar minti 7 tasake ɗago da kanta don ta dubesa still idanunsu ne ya sake sarƙewa acikin najuna, sake yin ƙasa da kanta tayi aranta tana cewa. "Na shiga uku waye wannan kuma ne wai da yazo ya hanani sukuni, irin wannan kallo saikace maye hegen gurgu mai jajayen kunnuwa, dama ai ance gurgu yafi mai k'afa iya shege!". bayan kamar 8 minutes a hankali tasake ɗago kanta, har yanzu dai kallonta yake baya ko ƙiftawa sai dai ya rage girman idanun nashi, ɗan jim tayi tare da yin mgnar zuci. "OK tsaurin ido ko tam zanyi mgninka yanzu". kana itama ta tattaro tsaurin idonta da jarumta ta tsaida kwayar idanunta cikin nashi kwayar idanun, dib-dib taji zuciyarta na bugawa da k'arfi-k'arfi kuma da sauri, wani irin kwarjini da haibar fuskarsa da surarshi suka cika mata idani cikin one second ta janye idanunta cikin idanunshi da sauri ta maidasu akan surar kansa zuwa gefen sajenshi, ganin bai ɗauke nasa idanun daga cikin nata ba yasanya ta sakar masa harara tare da murguɗa masa baki, wani irin dariyane ya kama Saifuddeen don sosai hakan da tayi ya ƙarawa fuskarta kyau, lumshe idanunsa yayi yana mejin wani abu ya dark'afe ƙahon zuciyarsa. Adaddafe haka Zaleeha tagama gabatar da shirinta inda gaba d'aya kallon da Saifuddeen ke mata ya dagula mata lissafi, ita sam batason yawan kallo musamman ma shida ya kafeta da ido kamar zai cinyeta kuma idanun nashi wani haiba suke dashi na musammam. a hankali taja gajeren tsaki tare, kallonshi a fakaice kana tace. "Maye kaci Kanka!." ido ya lumshe a hankali dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148