Skip to content

Chapter 140

Chapter 140

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

dole, gsky dole kiyi kuka." jin haka yasa Zaleeha fuskantarshi cikin kukan tace. "Kuma ina da wanda nakeso sannan su had'ani da wani can banza ginennen tab'o." kai ya jinjina mata tare da cewa. "To meyasa bazakuyi mgna ta fahimtar junaba keda shi, ki gaya mishi kinada wanda kikeso, kice mishi koda ya aureki bazai ji dad'in zama da keba, in ya amince ya hak'ura shine nan kin huta in ya kafe ya nace kuma kiyi hak'uri kibi umarnin iyayenki." Cikin kuka tace. "Na tsaneshi bana sonshi ta yaya zan auri nakasasshe alhalin da lfyta." shiru tayi ganin yadda a take fuskar Hayatuddeen ta canza launi da yanayi cikin had'e girar sama da k'asa mik'ewa yayi ya matsa gefenta tare da cewa. "Zancen banza kenan, ashema baki da hujja, shi nakasasshe ba halittar Allah bane, ko a zatonki Nakasa kasawa ce, aikin banza d'an adam da bai san k'arshenshiba yace yana kyaran larurar wani." Gaba d'aya ran Hayatuddeen ya b'aci sosai sai yake tuno wata k'ilfa wata ran ayiwa Hamma Saifuddeen d'inshi irin wannan cin zarafin, haka kawai kalamanta sukayi masifar tayar mishi da hankali, Hajja Inna ce tayi dariya tare da cewa. "Ato ai duk mai bin bayan Zaleeha zai shak'i takaici, yo wani nakasasshen ma ai yafi mai cikar halitta haiba." Ita kuwa Zaleeha cikin kuka tace. "Bazaku gane bane. Gurgu nefa akan wheelchair yake rayuwa, kuma kurmane bayaji baya mgna." Dam-dam zuciyar Hayatuddeen ya bada wasu tagwayen tarnaki mai cike da fargaba cikin zargin kai anya kuwa wannan bada Hammanshi take ba, cikin tsananin fargaba baki na rawa yace. "Uhmmm me sunan shi ne!?." cikin tarin tsanar tsuna taja wani dogon tsaki tare da mik'ewa kana tace. "Wai Saifuddeen n!!!." da sauri Zakariyya ya mik'e tsaye tare da cewa. "Hamma Saifuddeen. Shi kuwa Hayatuddeen cikin k'arfi ya fizgo hannunta tare da zaro idanunshi da sukayi jazir tuni hawaye na shatata a kumatunshi har kan gemunshi cikin rawan murya yace. "K'arya ne wallahi Hamma na ba nakasasshe bane, domin nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, Ke da kike zagin nakasarsa kinada tabbacin naki lafiyar ne, da har kike inkarin ke da lafiyarki, to wlh yanzu kika fara kuka ko zaki mutu sai kin zama matar kurma kuma gurgun nan, D'an uwane shine jigon rayuwar ahlinmu." Sai kuma ya sake mata hannu ya koma ya zauna, Zakariyya ma tuni hawaye yake zubdawa, dan sai yanzu ya gane ashe Hamma Saifuddeen ne wanda yayarshi Zaleeha keta ƙi. hakama Ziyada hawaye take zubdawa, Hajja Inna kuwa cikin mmki tace. "Hayatu, ashe ma Saifuddeen kyakkyawa ne ta samu har take rigima. Wlh ni ban saniba." Cikin zubda kwalla shima Hayatuddeen yace. "Wlh Hajja Inna nima sai yanzu na gane data kira sunanshi da yanayin nakasarsa kuma, na tuna ance min sunan matar da aka bashi Zaleeha ne." ita kam Zaleeha juyawa tayi ta fita jin ƙaninta Zakariyya na cewa. "Wlh nima ban san akan Hamma Saifuddeen bane take wannan haukan da ko inda take bazanma kallaba." Hajja Inna ce ta katsesu da cewa. "Ai kuwa ko mutuwa zatayi sai ta aureshi." Sai ta kuma kalli Hayatuddeen cikin rarrashi tace. "Kayi haƙuri kaji ko Hayatu, dan Allah kada ka gayawa Umminku da yayunka wannan batun in sha Allah Zaleeha zata tanƙwaru." Kai ya gyaɗa mata alamar to, sai ya kuma Kalli Zakariyya tare da cewa. "Dama nazo nefa muje gidansu Imran muyi batun dinner ɗin da za'ayi a bikin ne, ina son mu tsara fita ta musamman a wurin," cikin bada ƙarfin guiwa Zakariyya yace. "To muje, danko abu namune maganin a kwaɓemu." Daga nan suka tafi gidansu Imran ƙanin ishaq. Ita kuwa Zaleeha abu ya cakuɗe mata komai ya birkice mata, Yanzu ba mai bin ta kanta ta lura Aunty Lubna da Zakariyya basu damu da dmuwar tata ba Haka yasa dole ta ƙudurci son haɗuwa dashi ido da ido ayita ta ƙare. A lissafi dai yau saura kwana biyar ne auren. ganin har danginsu na Dukku sun fara zuwane ya ƙara tayar mata da hankalin. Gashi haka nan take jin kamar ana ingzata da zugata kan tayi wani mummunan abu. Shiyasa yau tunda safe taketa tura mishi text akan yazo gidansu zasuyi mgna mai mahimmanci ganin har yamma ba amsa ne yasa ta kira Ishaq bayan ta tuttura mishi saƙo dan Allah ya amsa kiranta, Yana d'agawa cikin rawan murya alamun zata fara kuka tace. "Dan Allah Malam Ishaq na rok'eka da manzon rahma kace yazo gidanmu inada mgna dashi." cikin danne dariyarshi da sai yanzu kalamanta na wai sun ce mata irin larrarshi basa iya aure dariyar ya ɗan danne kana yace. "Yaushe kike son yazo?." Da sauri tace . "Dan Allah yazo yau. Ban san in da zan sameshi ba da naje na sameshi." wani munafukin murmushi ishaq yayi sannan yace. "Ki duba hanyarshi zuwa bayan sallan isha." Da sauri tace to kana ta katse kiran, a take ta kira Bilkisu dan tasan itace zata tayata ci musu zarafi ta yadda sai sun tsani kawunansu ma, aiko Bilkisu najin shirin Zaleeha tace gata nan zuwa. Bayan sallan isha, Saifuddeen ne zaune bisa wheelchair ɗin shi kalar ruwan toka mai azabar kyau da sheƙi, a zahiri yadda yake caccanza sutura da ɗaukan wanka to hakama mota da wheelchair ɗinshi suma masu kyau da tsada ajin forko yake hawa hakama huluna da takalma, Sanye yake cikin wani d'anyen yadin voyel mai kalar shud'in sararin samaniya, sai kuma ratsin fari fari tamkar gajumare, an ƙyanƙyasawa rigar aiki da surfani mai ruwan garai-garai, hannun rigar guntu ne masu zagayen zaren garai-garai d'in daga bakinsu, hannun yayi cib damatsan hannunsa da suke farare k'al-k'al masu yalwar gargasa mai tsawo da shek'in bak'i mai d'aukar hankalin duk wanda ya gansu sun zauna cib, hular damanga ya kafa a kanshi irin kafin nan da ake cewa baruwanka da duniya bi ma'ana ya d'an tura hular tayi baya, hular farace sai ratsin shud'in zare, sajen nan nashi ya kwanta lib-lib a kyakkyawar fuskarshi mai suturce da farar fata da kan sura jajayen labbansa sai Sheƙi sukeyi a cikin zagayen gashin bakinsa. hakama takalmanshi farare ne k'al sai layi biyu da akaja mai kalar shuɗin daga samansu, sai wani zazzafan agogon fata na Gucci mai kalar garai da manna a tsintsiyar hannunshi na dama, sai farin ring ɗin azurfa dake ɗauke da ɗigon diamond a tsakiyarshi daketa wal-wal, wayarshi samfarin iPhone daya zura cikin al'jihun gaban rigarsa, wanda kana iya ganin kusan rabin wayar ma a sarari. Hayatuddeen ne ya lumshe ido tare da ƙara zuƙan numfashi dan shaƙan ƙamshin turaren Hamman nashi. Ummi kuwa ido ta zuba mishi cikin yin hamdala da godiya wa ubangijinta da azurtata da wannan kyakkyawan matashi a matsayin ɗanta. Murmushi yayi tare da mishi fatan a dawo lfy bayan ya mata alamun zai fita. Hayatuddeen kuwa har bakin mota ya rakashi inda suka samu Ishaq da Sule direba suna jiran fitowarshi. Mota suka shiga sannan suka nufi New G.R.A. Suna isa cikin gidan kuwa sukayi kicibis da Ya Aminu shi yayi musu jagora har cikin parlourn BQ kana yaje ya turo Zaleeha wacce, take tare da bilkeesu. kusan a tare suka fito yana gabansu. suna bayanshi suna tafe zuƙatansu fal farin cikin zasuci zarafinsu A harabar wajen suka samu Ya Aminun da

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148