Skip to content

Chapter 82

Chapter 82

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ta bashi magungunanshi sannan ta had'a sauran ta kullesu a leda tare da mik'awa Dr Adnan daya shigo yanzu, yana cewa. "Rahma ku fito ku tafi Ayuba na jiranku, zai fara biyawa kaduna ya sauk'i Raihana ku kuma zai wuce daku gombe, Raliya ki kula da Ummi sosai." Ahmad ne ya kalleta tare da cewa. "Goggo Dada ma taje tana can dan gaba d'aya Ummi bata cikin nitsuwa shiyasa nacewa Goggo Dadan taje ta d'an d'ebe mata kewa na kwana biyu." kai ta jinjina tare da cewa. "Allah ya kaiku lfy ya bada sa'an aikin da za'ayi mishi." Amin Amin sukace baki d'aya, sannan Adnan ya kalli Rahma cikin kula yace. "Please ki kula da kanki kada kiyi ta kuka, kinga kinada larurar da ba'a son kina yawan shiga damuwa, kiyi ta shan mgninki kan lokaci, nima Next two weeks zan dawo in Allah ya yarda." kai ta gyad'a kana ta mik'awa Saifuddeen hannu sukayi musabaha tare da cewa. "Ka yafe min d'an uwana ban saniba ko in haihu lfy ko akasin haka, in Allah yasa da sauran ganawarmu to Allah ya had'amu kan Al'khairi in kuma baka dawo ka sameni a rayeba, amana da tarbiyar su Faruq tana gareka." ina Raliya kam juyawa kawai tayi ta fita, hakama Raihana sai dai ita tana kuka ta fita, ita kuwa Rahma shafa fuskarshi tayi tare da juyawa tabi bayan k'annenta, tana isosu ta shiga mota Ayuba yaja suka tafi. Su kuwa Hayatuddeen ne ya had'e woyoyin Hammanshi ya zurasu a jakar system d'in shi sannan yabi bayan Ya Ahmad da Dr Adnan dake biye da bayan Nurses guda biyu da suke rik'e da d'an k'aramin gadon da ake d'aukar masu irin larurarshi. Cikin motar asibiti suka sashi, Ya Adnan ne ya shiga sannan driver ya shiga suka tafi Airport. Ahmad da Hayatuddeen kuwa Ya Rabi'u ne ya d'aukesu a motarshi sukabi bayansu, k'arfe tara dai-dai suka shiga cikin international airport Abuja. Bayan duk matafiya sun shiga kowa ya zauna mazauninsa, 9:30 Am jirginsu ya d'aga zuwa k'asar India cikin babban birnin New Delhi. Bayan lokaci mai tsawo suna ratsa gajimare jirginsu yayi sauk'an ank'ulu cikin Indara Gandhi international Airport Delhi. Bayan duk an fito ma'aikatan lfy na cikin jirgin suka fito da Saifuddeen wanda yana bacci. Ahmad da Dr Adnan da Hayatuddeen suna biye dasu a baya har gaban wata motar asibiti, nan suka shiga kai tsaye driver yaja suka tafi, kusan tafiyar awa d'aya da rabi sukayi sannan suka isa cikin harabar wanni tamfatsetsen asibiti mai tsananin azabar kyau da d'aukar hankali, suna fitowa Ahmad da kanshi ido ya zaro tare da cewa. "Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai mai sammai da k'assai." Dr Adnan da kanshi kyawun asibitin yayi matuk'ar girgizashi, Auta kuwa a hankali Hayatuddeen ya zuro k'afafunshi daga cikin motar, fitowa yayi tare da d'aga kanshi ya zaro idanshi da k'arfi ya kalli can! can!! can!!! Saman bene na k'arshe inda ya zubawa rubutun sunan shahararran asibitin da duniyar New Delhi ke ji dashi. *SUPER SPECIALTY SAFDARJUNG HOSPITAL* da sauri ya dawo da kanshi k'asa a hankali yayi wani irin s...! BY *GARKUWAR FULANI* 8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *NAKASA BA KASAWA BACE* *PAGE 20* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Sassanyan ajiyan zuciya yaja a hankali, ido ya lumshe tare da bud'esu ya juya ya kalli gabas da yamma kudu da arewa, a fili yace. "Gari banban Allah d'aya." Ahmad ne ya juyo ya kalleshi tare da cewa. "Ko wanne wuri da irin kalar ni'imar da Allah yake musu." da sauri suka juyo suka kalli ya Adnan dake ce musu. "Ni zan shiga ciki zamu isa wurin Dr Acash prasat zan kama mana layi, duk dai Dr Aliyu ya mana hanyar ganinshi a watannan to dole sai munbi layi. So kai Ahmad ga can taxi ku shiga sai ku duba mana hotel nan kusa mu samu masauk'i." cikin gamsuwa da hakan Ahmad yace. "To ba matsala bari mu d'auki kayan mu." Shi kuwa Hayatuddeen da sauri yabi bayan nurses da suka fito da Saifuddeen dake kan gado, yana isa ya bawa Saifuddeen hannu tare da cewa. "Zamuje nan kusa, ya Adnan zai shiga ciki da kai." kai ya gyad'a mishi alamar sai sun dawo hakama Ahmad yazo ya salla meshi sannan Dr Adnan yabi bayansu, suka nufi cikin ainihin asibitin, tafiya kad'an sukayi suka ratsa cikin wani babban corridor mai girma, tafiya yar kad'an suka isa bakin wata babbar k'ofa, suna bud'ewa wasu nurses d'in suka karb'eshi, kana wad'an nan suka juya sukayi baya, su kuma wannan da suka k'arbeshi sai suka canza mishi gado suka d'auranshi kan irin k'ananun gadajen tura marasa lfyn, sannan da sauri Dr Adnan kuwa ya mik'a d'aya daga cikinsu wata takarda, bayan ya karb'a ya duba sai ya juyo ya kalli d'aya nurse dake tura gadon yayi mishi mgna cikin indiyancin. Sai kuma suka canza hanya suka fuskanci wani ratsetsen gini mai azabar kyau amman shi ba benaye bane. suna isa harabar wannan wurin wasu nurses d'in suka karb'eshi kana suka basu wannan takardar da takeda tambarin National Hospital Abuja, a k'asa kuma ga sa hannun Dr Aliyu, can gefe kuma ga shaidar transfer zuwansu wannan asibitin da. shi dai Dr Adnan binsu yake a baya. A hankali suka bud'e wata k'ofa mai girma suka shiga Dr Adnan na biye dasu a baya, yana sa k'afarsa cikin Reception d'in nasu yayi wani irin ajiyan zuciya dan wani azabebben sanyi da ya cika wurin, gaba d'aya reception d'in cike yake mak'il da mutane duk da girmanshi sai dai duk ana zaune bisa tsari ba hayaniya, shi kuwa Saifuddeen kanshi ya d'an juya ya kalli gefen hagunshi da damanshi, jerin gadaje ne a gefen hagunshi mutane na konce a Kai, d'aya gefen kuwa kekunan weelchair ne a jere wasu na zazzaune a ciki. gefen gadajen aka tura gadon da Saifuddeen ke kwance, sannan nurse d'in ya yafito Adnan kana suka nufi gaban inda nurses ke zaune suna bada kati dama masu bud'e folda suna isa suka mik'awa d'aya daga cikin matan dake wurin takardar, mgna suka d'anyi cikin yarensu da Adnan baya ji ya dai ji suna kiran Nigeria, sai kuma nurse d'in da aka kira da Divia ta juyo ta kalli Adnan tare da mishi tambayar ina fayel nasu na asibitin da aka turosu nan cikin turanci. Da sauri ya mik'a mata fayel d'in amsa tayi sannan ta had'a da takardar da wannan d'in ya bata, juyawa tayi ta d'auko polder sannan ta bud'e wanna fayel d'in kana ta d'auki biro ta fara rubutu a saman poldern sai kuma ta fara bud'a fayel d'in nan ta d'anyi 'yan rubuce-rubuce sannan ta mik'awa Adnan hand card data zaro cikin polder d'in, amsa yayi ya duba kasan cewarshi Dr ras ya gane rubutunsu na doctors da yafi kama da jagwalgwale, kai ya jinjina ganin bata saurari tambayarshi sunan mara lfy da shekaru ba duk ta samesu cikin fayel d'in da suka zo dashi. kai ta sunkuyar kana ta matso kusa da system d'in dake gabanta a hankali ta fara sassarafashi, daga bisani ta d'ago kai tace mishi yaje ya zauna za'a nemeshi. Gefen da Saifuddeen yake yaje, nan ya samu yana bacci dan ya samu irin sanyin da jikinshi ke buk'ata, kasan

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148